Top Banner
DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES AND LINGUISTICS FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES BAYERO UNIVERSITY, KANO TOPIC OF DISCUSSION: ‘Waqoqin Zamantakewa kan zama Waqoqin Faxakarwa ga Al’ummar Hausawa’. PRESENTATION DATE: 11 TH JUNE, 2013
65

'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Mar 11, 2023

Download

Documents

Welcome message from author
This document is posted to help you gain knowledge. Please leave a comment to let me know what you think about it! Share it to your friends and learn new things together.
Transcript
Page 1: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES AND LINGUISTICS

FACULTY OF ARTS AND ISLAMIC STUDIES

BAYERO UNIVERSITY, KANO

TOPIC OF DISCUSSION:

‘Waqoqin Zamantakewa kan zama WaqoqinFaxakarwa ga Al’ummar Hausawa’.

PRESENTATION DATE:11TH JUNE, 2013

Page 2: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

1.0 Gabatarwa‘Waqoqin zamantakewa kan zama waqoqin faxakarwa ga al’ummar

Hausawa’. Wannan shi ne batun da za mu tattauna a

wannan aiki. Za mu yi wannan tattaunawar ne tare da

kawo misalai na wasu waqoqin zamantakewa na

Hausawa. Mun kasa wannan aiki zuwa kashi uku manya.

A kashi na farko, za mu kalli ita kanta waqa da

rabe-rabenta da kuma taqaitaccen tarihin samuwar

rubutattun waqoqi. Za mu yi wannan ne a taqaice. A

kashi na biyu kuwa, za mu ga ma’anar zamantakewa da

nau’o’in wasu daga cikin waqoqin zamantakewa. Shi

kuwa kashi na uku, zai mana sharhi a kan yadda

waqoqin zamantakewa kan zama faxakarwa ga al’ummar

Hausawa. Saboda haka, a wannan kashi, za mu fara da

kawo ma’anar faxakarwa, sannan faxakarwar da

waqoqin zamantakewar kan yi dangane da gyaran hali,

da qarfafa neman ilimi, da aure, da zumunta, da

kishin harshe, da ma’malar siyasa, da yin

2

Page 3: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

ta’aziyya, da sauransu. Za mu fito da faxakarwar ne

a kan waxannan al’amurra na zamantakewa daga cikin

waqoqin marubuta waqoqin Hausa daban-daban. Saboda

haka, wannan tattaunawar ta taqaita ne a kan

rubutattun waqoqin Hausa, ba da na baka ba.

Bayan waxannan kashi uku manya da za mu

tattauna a kansu, akwai jawabin kammalawa daga

qarshe. Bayansa kuma, mun kawo manazarta, wato

littattafan da muka yi nazari da kuma samo bayanai,

da ma waxanda suke da alaqa da waxanda suka shafi

tattaunawar tamu, ko da kuwa ba mu tsakuro daga

gare su ba. A qarshe kuma, mun kawo ratayen wasu

daga cikin waqoqin zamantakewa na marubuta waqoqin

Hausa daban-daban.

2.0 Ma’anar WaqaMasana1 sun bayyana ma’anar waqa. Yanzu kuma za mu

duba mu ga yadda suke kallon ma’anar waqa, daxa ta

baka ce ko rubutacciya. Yahaya (1976:1) ya ce2:1 Irin su Yahaya (1976); Umar (1980); Dangambo (2007); Yahya (1984);Gusau (2003); Auta (2008).2

3

Page 4: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

“Waqa magana ce ta fasaha a

cure wuri xaya a cikin tsari

na musamman”.

Shi kuwa Umar (1980:3) cewa ya yi:

“Waqa tana zuwa ne a sigar

gunduwoyin zantuka waxanda ake

kira baitoci ko xiyoyi kuma

ake rerawa da wani irin sautin

murya na musamman”.

Dangambo (2007:6) kuma ya ce:

“Waqa wani saqo ne da aka gina

shi kan tsararriyar qa’ida ta

baiti, xango, rerawa, kari

(bahari), amsa-amo (qafiya),

da sauran qa’idojin da suka

shafi daidaita kalmomi,

zavensu da amfani da su cikin

sigogin da ba lalle ne haka

suke a maganar baka ba”.

Shi kuma Yahya (1997:2-3) sai ya ce:

“Waqa maganar hikima ce da ake

rerawa ba faxa kurum ba wadda? A cikin gabatarwar da ya yi wa littafin Waqar Haxa Kan Afirka.

4

Page 5: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

ke da wani saqo da ke qunshe

cikin wasu kalmomi zavavvu,

tsararru, kuma zaunannu”.

Gusau (2003: xiii) ma ya ce:

“Waqar baka, wani zance ne

shiryayye cikin hikima da

azanci da yake zuwa gava-gava

bisa qa’idojin tsari da

daidaitawa a rere cikin sautin

murya da amsa-amon kari da

kixa da amshi”.

Auta (2008) ya ce:

“Waqa tana nufin manufa da

qayyadaddun kalmomi, da zubi,

da tsari, da baiti, da jin

daxi, da sanyin murya, da

tsarin kalmomi, da sautin

murya mai zaqi, da rerawa, da

amshi ko qari, da azancin

zaven kalmomi, da sarrafa su,

da kixa, da busa, da

annashuwa, da rausaya, da

5

Page 6: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

sauran kalmomi masu yawa da

suka danganci waqa”.

A dunqule, ta la’akari da yadda masana suka kalli

ma’anar waqa, za mu iya cewa, waqa tsararriyar

magana ce da ake yin ta cikin hikima da zavin

kalmomi, ba kara zube ba, domin isar da saqo ko

wata manufa ga al’umma.

2.1. Rabe-Raben WaqaWaqoqin Hausawa, masana sun nuna cewa iri biyu ne.

Kamar yadda Dangambo (2008:5) ya nuna cewa, akwai

waqoqi iri biyu: rubutacciyar waqa da waqar baka,

wato waqar makaxa. To, mu wannan tattaunawar tamu,

ta tsaya ne a kan waqa rubutacciya. Saboda haka, za

mu xan waiwayi tarihin rubutattun waqoqin Hausa,

amma a taqaice, kamar yadda masana suka bayar da

shi.

2.1.1 Taqaitaccen Tarihin Samuwar

Rubutattun WaqoqiSu rubutattun waqoqi sun samo asali ne daga waqoqin

Larabawa (Yahaya da Dangambo, 1986). Waqoqin Hausa

na farko an rubuta su ne a cikin Hausa ajami. Haka

6

Page 7: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

kuma, su waxannan waqoqi duk sun wanzu ne sakamakon

addini. Wato, abin nufi a nan shi ne, qoqarin yaxa

addinin Musulunci shi ne ya haddasa kuma ya havaka

rubutattun waqoqi na Hausa. Ana zaton cewa, waqoqin

sun faro daga lokaci mai tsawo da ya wuce, wato tun

lokacin da Musulunci ya yi qarfi. Akwai zancen

cewa, rubutattun waqoqi sun faru tun qarni na 173

da na 184, kamar yadda tarihi ya nuna5. Abin da yake

tabbas shi ne cewa, rubutacciyar waqa ta havaka ne

a qarni na 19, wato zamanin jihadin Shehu Usmanu

Xan Fodiyo.

Waqoqin Qarni Na Sha Tara

A wannan qarni na sha tara, an sami wani yunquri na

bunqasa ilimi, da yaxa addinin Musulunci, da kau da

jahilci da al’adu, da camfe-camfe a qasar Hausa.

Shugabannin jihadi sun yi wallafe-wallafe masu

ximbin yawa na fannonin ilimi daban-daban da

Larabci, kamar su Tauhidi da Fiqihu da Hukunce-

3 Wato kamar waqoqin su Wali Xanmarina da Wali Xanmasani, irin su WaqarTaba, da Waqar Yaqin Badar, da di sauransu.

4 Wato kamar waqoqin su Muhammadu Alkatsinawi da Muhammadu Na BirninGwari da Malam Shi’itu Xan Abdurra’ufu, irin su Gangar Wa’azu/Bakandamiya,da Waqar Wawiya, da Waqar Jiddul Ajizi Ba’ajamiya, da sauransu.

5 Kamar a cikin littafin Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa naIbrahim Yaro Yahaya (1988).

7

Page 8: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Hukuncen Shari’a da tsarin mulki da dai sauransu.

Daga nan suka ga cewa, hanyar da ta fi sauqi ga

isar da saqonsu ga jama’a, ita ce ta hanyar

harshensu. Suka ga kuma cewa, waqa ce ta fi sauqin

shiga kai, sai suka shiga bayyana musu manufofinsu

a waqe da Fillanci da kuma Hausa, suna tsamo

waxannan manufofi nasu daga cikin talifan da suka

yi da Larabci (Abdulqadir, 1979).

Shehu Usmanu da Abdullahi qanensa da Nana

Asma’u da Isan Kware ‘ya’yansa da wasu daga cikin

almajiransa irin su Mamman Tukur da Dikko Xanbagine

da Gixaxo xan Lema, duka sun rubuta waqoqi masu

yawa da Hausa. Daga cikin waqoqin da suka rubuta

akwai ‘Waqar Tabban Haqiqa’ da ‘Waqar Lalura’ da

Waqar na Shehu Usmanu Xan Fodiyo. Sannan kuma,

akwai ‘Waqar Tsarin Mulki na Musulunci’ da ‘Waqar

Murnar Cin Birnin Alqalawa’ na Abdullahi Xan

Fodiyo. Haka kuma, Nana Asma’u ta rubuta waqoqi

irin su ‘Godaben Gaskiya’ da ‘Tawassuli’ da

‘Kirarin Amada’ da ‘Roqon Ruwa’ da ‘Sharuxxan

Qiyama’. Shi kuwa Isan Kware ya rubuta ‘Waqar

Haqqin Mumini Bisa Mumini’ da ‘Waqar Tarbiyyar

Yara’. Haka Mamman Tukur ya rubuta ‘Waqar Baqin

8

Page 9: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Mari’. A taqaice dai, Shehu Usmanu Xan Fodiyo da

mutanensa sun rubuta waqoqi masu a wannan qarni na

196.

Yawancin waqoqin qarni na 19, an rubuta su ne

kan yabon Ubangiji da yabon Annabi da wa’azi da

fiqihu da shari’a da sha’anin mulki. Wato dai

jigonsu ya fi ba da qarfi ga addini. Wannan bai

canja ba har zuwa qarshen wannan qarnin, da ma

farkon qarni na ashirin.

Waqoqin Qarni Na Ashirin

A cikin qarni na ashirin an samu wani sabon salo na

rubuta waqa a qasar Hausa. Sarkin Zazzau Aliyu

Xansidi shi ya fara buxe qofar wannan qarni da

waqarsa ta habaici mai suna ‘Tabarqoqo’

(Abdulqadir, 1979). Mun ce waqoqin qarni na sha

tara kusan sun qunshi addini ne kawai, to amma a

qarni na ashirin sai aka sami wasu waqoqin da suka

shafi rayuwar xan’adam ta yau da kullum, bayan na

addini. Da farko dai, a wannan qarni jigon addini

ya ci gaba. Sannan kuma, an sami waxansu jigogi

daban-daban da ba na addini ba. Waxannan jigogin6 Don qarin bayani duba Gudummawar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa (Juzu’i Biyu),Kundin Digiri na Biyu na Bello Sa’id, 1978. Ko Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa na Ibrahim Yaro Yahaya, 1988.

9

Page 10: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

sun haxa da siyasar jam’iyya da soyayya da al’adu

da wayar da kai da kishin qasa da kishin harshe da

gargaxi da faxakarwa da nasiha da ta’aziyya da nuna

hikima da dai sauransu da yawa.

3.0 Ma’anar ZamantakewaAl’ummar Hausawa, al’umma ce mai kyakkyawan tsari

na zamantakewa da ingantattun al’adu na gudanar da

rayuwa. Ko da addinin Musulunci ya zo qasar Hausa,

ya tarar da al’adu da tsarin zamantakewa na

Hausawa. Inda ya yi na’am da wasu, wasu kuma ya ce

a sa su a mala. Su ma Turawa da suka zo sun tarar

da Hausawa da tsarin zamantakewarsu mai kyau, sai

dai kuma sun cusa wa Hausawa wasu xabi’u na

zamantakewa da ba su saba da su ba.

Qamusun Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya

(2006:489) ya bayyana zamantakewa da cewa:

“Zamantakewa na nufin zaman tare wanda kan jawo

shaquwa da juna”. Shi kuwa Habibu Sani Vavura7 ya

ce: “Zamantakewa na nufin duk wani abu da ya shafi

rayuwar al’umma, ba ta dabbobi ba, shi ake kira

zamantakewa. Saboda haka, zamantakewa ta qunshi7 A Laccar Aji da ya yi wa ‘yan Aji Huxu, a Shekara ta 2011

10

Page 11: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

xabi’a da al’ada da fasaha da matsayin ilimi na

al’umma da yanayin tattalin arzikinsu da na siyasar

mulki da rayuwa gaba xaya”.

A taqaice dai, zamantakewa ita ce yanayin zaman

tare na mutane, ba dabbobi ba. Wannan yanayin kan

iya zama mai kyau ko akasin haka. A al’ummar

Hausawa akan sami dukkan yanayin zamantakewar iri

biyu. Haka kuma, zamantakewa aba ce mai matuqar

muhimmanci ga rayuwar xan’adam, kasancewar mutum ba

zai iya rayuwa shi kaxai ba.

3.1 Nau’o’in Waqoqin ZamantakewaA baya, an bayyana mana cewa, zamantakewa ita ce

zaman tare wanda kan jawo shaquwa da juna ko kuma

duk wani abu da ya shafi rayuwar al’umma. To, idan

kuwa haka ne, akwai waqoqi da dama da marubuta

waqoqin Hausa suka rubuta da suka shafi

zamantakewa. Kusan ma a iya cewa, su ne waxanda

suka fi yawa a cikin rubutattun waqoqi. Saboda

haka, nau’o’in waqoqin zamantakewa suna da yawa,

sai dai mu xan kawo misalan wasu daga cikinsu.

11

Page 12: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Waqa Mawallafi Zamantakewa

Mikiyar Zuhudu Abdulqadir Babajo Aure

To Da Ke Nike Sambo Wali Basakkwace Aure

Kadaura Babbar Inuwa Aqilu Aliyu

Neman Ilimi

Gargaxi Ga ‘Yan Makaranta Wazirin Gwandu

Neman Ilimi

Waqar Karuwa Mu’azu Haxeja Gyaran Hali

‘Yar Gagara Aqilu Aliyu

Gyaran Hali

Shaye-Shaye Aibi Na Sambo Wali Basakkwace

Gyaran Hali

Son Maso Wani Cuta Ne Wada Hamza

Soyayya

Wasiqa Ga Yusufu Kantu Bello Gixaxawa Sada

Zumunci

Siyasa Zamanin Salama NPC Bello Gixaxawa Siyasa

Ta’aziyyar Mudi Salga Kano Bello Gixaxawa

Ta’aziyya

Marsiyyar Zainu Bunguxu Bello Gixaxawa Ta’aziyya

Haqqin Mumini Bisa... Isan Kware

Maqwabtaka

Hausa Mai Ban Haushi Aqilu Aliyu Kishin

Harshe

Qalu-Bale Aqilu Aliyu Neman Ilimi

12

Page 13: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

‘Yar Budurwa Son Ki Nake Wada Hamza

Soyayya

Waqar NPC Shekara Siyasa

Waqar NEPU Gambo Hawaja Siyasa.

Waxannan kaxan ke nan daga cikin waqoqin

zamantakewa. Kasancewar zamantakewar al’ummar

Hausawa mai faxi ce, sannan kuma waqoqin da aka

rubuta a kan vangarori daban-daban na zamantakewa

masu yawa ne, ya sa muka taqaita a kan waxannan

waqoqin da waxannan vangarorin zamantakewa.

4.0 Ma’anar FaxakarwaMasana sun bayyana ma’anar faxakarwa a cikin

ayyukansu. Haka kuma, a cikin qamusoshin Hausa an

bayyana ma’anar faxakarwa. Saboda haka, za mu xan

tsakuro abin da qamusoshi da masana suka faxa

dangane da ma’anar faxakarwa.

Qamusun Bargery (1934:288) ya bayyana faxakarwa

da cewa: “faxakarwa na nufin zaburar gargaxi a sa

mutum ya fahimta ko a sa mutum ya tuno, misali wani

abu da aka sani aka take”. Shi kuwa qamusun Cibiyar

13

Page 14: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Nazarin Harsunan Nijeriya (2006:129) ya ce: “ka

farka ko ka lura ko ka kula shi ne faxakarwa”.

Masana kuwa sun bayyana faxakarwa da cewa,

“tunatar da mutum a kan waxansu al’amurran rayuwa

domin ko dai ya aikata abubuwan nan saboda

muhimmancinsu kuma ya amfana da su, ko kuma lurar

da mutum ga waxansu al’amurra munana domin ya guje

su” (Auta, 2008:76). Junaidu da ‘Yar’adua

(2007:189) sun bayyana faxakarwa da cewa: “tambihi

ne ga wasu sanannun halaye na rayuwa don jawo

hankali da wayar da kan jama’a da irin

muhimmancinsu”. Shi kuwa Sadiq (1990:30) sai ya ce:

“faxakarwa na nufin nusar da mutum a kan abubuwan

da ya sani tun tuni amma ya manta da su. Don haka

ne aka yi masa tuni da hannunka mai sanda don ya

dawo ya yi la’akari da su.

A taqaice, za mu iya cewa, faxakarwa na nufin

tunatar da mutum wani abu na zamantakewar rayuwarsa

a kan ya aikata shi idan mai kyau ne, ko kuma ya

guje masa idan maras kyau ne. Saboda haka,

faxakarwa na iya kasancewa nasiha ko jawo hankali

ko wayar da kai ko gargaxi a cikin zamantakewar

al’umma.

14

Page 15: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

4.1 Faxakarwa A Cikin Waqoqin

Zamantakewa Zamantakewar al’ummar Hausawa ta qunshi vangarori

masu yawa, masu kyau ko kuma marasa kyau. Su kuma

marubuta waqoqin Hausa sun rubuta waqoqi da dama da

suke yin faxakarwa a kan zamantakewar al’ummar

Hausawa. Saboda haka, idan zamantakewar Hausawa ta

kasance mai kyau, sai marubuta waqoqin (a cikin

waqoqinsu) su faxakar da al’umma a kan su ci gaba

da irin wannan zamantakewar. Idan kuwa ya kasance

tsarin zamantakewar bara-gurbi ne, sai su faxakar

da su a kan munin irin wannan zamantakewar don su

yi gyara. Wannan ke nan ya nuna mana cewa, akwai

faxakarwa a cikin rubutattun waqoqin zamantakewa. A

nan, za mu dubi yadda waqoqin zamantakewa kan zama

waqoqin faxakarwa, wato yadda waqoqin kan faxakar

da al’ummar Hausawa ga tsarin zamantakewa mai kyau

ko maras kyau.

A tsarin zamantakewar Bahaushe, akwai aure da

maqwabtaka da abota da sada zumunta da siyasa da

neman ilimi da ta’aziyya da sauran vangarori da

15

Page 16: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

yawa. Waxannan vangarori da muka faxa, masu kyau ne

a zamantakewar Bahaushe. To, amma kasancewar a

kowace al’umma akan sami tsarin zamantakewa maras

kyau, ya sa shi ma Bahaushe yana da tsarin

zamantakewa akasin mai kyau. Alal misali, a

al’ummar Hausawa ana gudanar da auren dole da

karuwanci da shaye-shaye da faxace-faxace da

munafunci da hassada da makamantansu. Saboda haka,

waqoqin da suka yi tsokaci a kan xaya daga cikin

waxannan vangarori ko al’amurra na zamantakewa,

suna yin faxakarwa ne a kan a ci gaba da

zamantakewa mai kyau ko kuma a daina zamantakewa

maras kyau. Don haka, a nan, waqoqin zamantakewa

sun zama waqoqin faxakarwa ga al’ummar Hausawa.

Yanzu za mu yi nazarin wasu nau’o’in waqoqin

zamantakewa don mu ga irin faxakarwar da ke cikinsu

dangane da zamantakewar al’ummar Hausawa.

4.1.1 Faxakarwa a kan Gyaran HaliGyaran hali shi ne tuni ko gyara abin da ya gurvace

ko ya lalace na daga hali ko aka shiriritar da shi,

ko kuma daidai al’amarin halayen mutane na

kyakkyawar xabi’a da kauce wa duk wani hali da za

16

Page 17: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

ai tir da shi da umarni da hali na gari, misali

kunya, kawaici, kara, tarbiyya da sauransu, da hani

da mummuna kamar karuwanci da daudu da sauran

mummunan hali (Ali, 2012).

A waqoqin zamantakewa, mawallafa waqoqin sun

faxakar da Hausawa a kan wasu munanan halaye na

zamantakewa domin a qyamace su ko kuma a guje su.

Alal misali, a ‘Waqar Karuwa’, Mu’azu Haxeja ya

faxakar da al’umma a kan munin karuwanci, inda ya

bayyana munanan halayen karuwa, ya kuma faxakar da

mutane a kan su qyamace su ko ma su guje ma

halayenta gaba xaya. Ga abin da yake cewa a baiti

na 30 da na 31:

“Aboki da hankalin kanka, Kakan auka cikin halaka, Abin duniya shi dame ka,

Ga aiki ba na hairi ba.

Kowab bi halinta ya tave,Ga aikin hairu ya keve,Dukan zarafinsa ya cave,

A nan Ibilisa yai galaba.”

17

Page 18: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Shi ma Aqilu Aliyu a cikin waqarsa ta ‘`Yar Gagara’

ya faxakar da al’umma a kan munin karuwanci da kuma

munanan halayen karuwa don mutane su qyamace su. Ga

dai abin da ya ce:

“Karuwa ba ta nufin ta yi aure,Kai dai bar ta a savon Sarki.

(baiti na 4)

Ta qi shiri da uwa da uba ma,Balle Yaya abokin dambe.

Ai kome ta yi ba mamaki,Domin ba ta da shayin kowa.”

(baiti na 8 da na 9)

Haka kuma, ya faxakar da ma’aurata masu gidaje a

kan kar su bar karuwa ko mai irin halayenta su riqa

shiga gidajensu. Kamar a baiti na 37 da na 38, inda

ya ce:

“Kar ka amince zamanta gidanka,Sai ta tula maka shara kullum.

Hana mata leqa wajen matanka,Don kar tai musu hirar banza.”

18

Page 19: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Shi ma Sambo Wali Basakkwace8 ya yi faxakarwa ta

gyaran hali a cikin waqarsa ta ‘Shaye-Shaye Aibi

Na’, inda ya bayyana munin shaye-shaye, wanda

babban qalubale ne a zamantakewar ‘ya’yan Hausawa

musamman a wannan lokaci da muke ciki, da kuma

faxakarwa a kan a daina yin sa. Ga kaxan daga abin

da ya ce:

“Yanzu kun ji niyyata, In roqijama’ata,

Dukkanmu mu qoqarta, Don mu zanmahankalta,

Kar mu zan magigita.

Hankali muhimmi na, Don ku ganeqaulina,

Kare shi abin yi na, Shaye-Shaye aibina,

Ni kam ga fahimtata.”(baiti na 4 da na 5)

A zamantakewa ta makaranta musamman makarantar

sakandare, akan sami xalibai masu yin shaye-shaye.

Saboda haka, Sambo Wali ya faxakar da shugaban

makaranta (principal) a kan ya kula don hana irin

wannan mummunan hali. Ga abin da ya ce:8 Sambo Wali Basakkwace shahararren marubuci waqoqin Hausa ne a qasarSakkwatao

19

Page 20: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

“Zan Kwalej wajen yara, Masutattalin sura,

To Firinsifal gyara, Ka daina sarashin lura,

Har su kai ga shibka ta.

Zan ka tsara mallammai, Rodikol kuzan yi nai,

Har cakin ana so nai, Duti Masta aikinai-,

Na hana su kunna ta.”(baiti na 25 da na

26)

Haka kuma, Sambo Wali ya faxakar da hukuma da

sarakuna a kan a yi qoqarin kawo gyara ga wannan

mummunar zamantakewa ta shaye-shaye, inda ya ce:

“Za ni gargaxin qarshe, Don ku jishi koyaushe,

Na yi gargaxi qumshe, Ga misalsalitarshe,

Kun kasa ku lisafta.

Ya fi kyau ku lisafta, Hankali kabambanta,

Mutum da shi da dabba ta, Kwas sayo ma kaicuta,

Ta fi shi ga aikinta.

20

Page 21: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Gwamna sai ka qoqarta, A gargaxinmalalata,

Sarakuna ku yunqurta, Dottive kuhankalta,

Kula ma masu yarin ta.(baiti na 39 – 41)

A zamantakewar Hausawa ta tsakanin iyaye da ‘ya’ya

akan sami bijirarrun ‘ya’ya waxanda ke sava wa

iyayensu har ma su kai ga vata musu rai. Wani

lokaci ma har da sa iyayen cikin rikici, wanda ke

kai ga yi musu wulaqanci ko zubar da mutuncinsu a

idon jama’a. Mu’azu Haxeja a waqarsa ta ‘Birrul

Walidaini’ ya faxakar da ‘ya’yan Hausawa a kan su

riqa yin xa’a da biyayya da kyautatawa ga iyayensu.

Saboda idan ba su yi ba, to Allah zai yi fushi da

su, Ya haramta musu ni’imominsa, Ya kuma yi musu

azabobi duniya da lahira. Ga kaxan daga faxakarwar

da Mu’azu Haxeja ya yi a wannan waqar:

“Sani bayan bin sa Allah, Da Ma’aiki dukda salla,

Sai iyaye ga farilla, Bin iyaye nesabila,

Wanda zai kai mu Janani.(baiti na 2)

21

Page 22: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Tun kana xan jariri, Ka yi kashi dafitsari,

Duka xaki shi yi wari, Ban da banzaasharari,

Wa ka vata walidaini.

Ga su nan dai bisa fama, Ga ka nan har kayi dama,

Su yi rainonka ka girma, Wajibi ne hakakai ma,

Kyautata wa walidaini.

‘Yan’uwa dole mu bi su, Kun sani in munrasa su,

Babu canjinsu kamarsu, Mu yi kuka darashinsu,

Babu tamkar walidaini.

Kyautata wa walidanka, Matuqar dukrayuwarka,

Don su sa ma albarka, Ita ce ma za ta bika,

Duniyata haka dini.”(baiti na 8 – 11)

Waxannan baitoci, sun nuna mana irin faxakarwar da

Mu’azu Haxeja ke yi game da kyautata wa iyaye,

wanda sanin kowa ne cewa, a zamantakewar Hausawa,

kyautatawa iyaye hali ne mai kyau.

22

Page 23: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

4.1.2 Faxakarwa a kan Neman IlimiAuta (2008:41) ya bayyana ilimi da cewa, “ilimi shi

ne ya bambanta mutum xan’adam da dabba. Ilimi

al’amari ne mai darajar gaske, don haka wanda ya

sani ba zai zama daidai da wanda bai sani ba. A

qarqashin ilimi kowace xaukaka take, kamar yadda

matsala a qarqashin jahilci take.”

A zamantakewar al’ummar Hausawa, duk wanda ba

shi da ilimi, ba a xaukar sa da daraja. Saboda

haka, waqoqin zamantakewa da dama sun faxakar a kan

neman ilimi. Idan muka dubi waqar ‘Qalubale’ ta

Aqilu Aliyu, za mu ga cewa tana faxakarwa ne a kan

neman ilimi. Ga kaxan daga faxakarwar da Aqilu

Aliyu ya yi a kan neman ilimi a ‘Waqar Qalubale’:

“Kadan ka ture zuciya,Da ilmu ake qalubale.

Abin da ya kyautu da mu mu yi,Mu himmatu har mu kashangale.

Mu qyale buqata kowace,Cikin ilimi mu shugulgule.

A ofis ko a cikin sito,A kowane gu ya maqalqale.

23

Page 24: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Mu je mu tsaya mu fito da shi,Mu jajjawo shi mu qwaqule.”

(baiti na 4 – 8)

Cikin nema nasa kar mu ji-,Kasala kar mu katangale.

Kaxan ba ka gane ilmu ba,Ba ka cure ba ka dunqule.

Ba ka shafe ba ka lailaye,Ba za ka naxa ba ka mulmule.

Kaxan ba ilmu gare ka ba,Cikin sha’ani kai ne bale.

Kana kallo a yi ban da kai,Ganinka da ji ka dabalbale.

Baqar magana a yi ma ka ji,A dole ka zam ka daqile.

(baiti na 11 – 16)

Mu tashi mu miqe qyam tsaye,Mu nemi sani mu fi’ittale.”

(baiti na 29)

Haka ma a cikin waqarsa ta ‘Kadaura Babbar Inuwa’,

Aqilu Aliyu ya faxakar da jama’a a kab cewa, su

nemi ilimi. Kuma ya tunatar da su a kan martabobi

24

Page 25: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

da darajojin da mai ilimi zai samu. Ga dai abin da

yake cewa:

“A mazanmu har matanmu yara da manya,Jama’a mu san ilimi muna tarawa.

Shi ne Kadaura ilmu babbar gayya,Inuwa mayalwaciya wajen hutawa.

Lallai mu ja xamara mu miqe sosai,Ba nuna lalaci da son gajiyawa.

(baiti na 6 – 8)

Shin ko akwai namu ba wani ilimi ba,Mai kai mutum qolqoliyar xorawa?

(baiti na 11)

In ba sani ba za a san shari’a ba,Balle a san odar da ke shiryawa.

Ba za ka zam wani kashiyan banki ba,In babu ilimi da me kake

kawashewa.

In ba sani ba za ka zam dokta ba,Sai dai akwai ilimi ake aikawa.

Aikin tiyata masu ilmu suke yi,Mai hattara shi ne da qulla abawa.

Ba za ka zamto malamin ofis ba,Sai mai yawan ilimi yake aikawa.

25

Page 26: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Ba za ka zamto malamin huji ba,In babu ilmi da me kake hudawa?

In ba sani ba za ka zam lauya ba,A’a haba mai ilmu ke lauyewa.

Aikin jarida masu ilmu suke yi,Qasgi qumusgi ba shi fara tavawa.

In ba sani ba za ka zam tica ba,Sai mai yawan ilimi yake koyarwa.

(baiti na 58 – 66)

Ba na xarar muku hankali ba haba wa!Sai dai tunatarwa kurum

faxakarwa.”(baiti na 36).

Bayan Aqilu Aliyu ya faxakar da jama’a a kan neman

ilimi, sai Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nassarawa9

ya faxakar da masu neman ilimin

(‘yanmakaranta/xalibai) a kan yadda ya kamata su

kasance a lokacin da suke neman ilimin, a cikin

waqarsa ta ‘Gargaxi Ga ‘Yanmakaranta’. Ga

faxakarwar da yake musu kamar haka:

“Wada anka so almajiri,A ishe hali mai kyau garai.

9 1916 – 2000

26

Page 27: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Duka lokacin salla shina-,Tsare duk da tasbi ag garai.

Mai hankali mai girmamawa,Har a san ladabi garai.

Shi fake amanam malami,Shi tsare umurninai garai.

Na gabansa ko ba malami-,Ba shi zan tsaron girma garai.

Tsararsa duk shi fake mutum-,Cin nasu har irli tsarai.

A ishe shi ba shi da twakara,Kuma hanqurewa ag garai.

Da cikin aji da cikin gari,A ishe halin girma garai.

Kyawon hali shi am mutum,Sannan a so ilimi garai.

A cikin aji in an shiga,A ishe akwai himma garai.

A ishe shina sa hankali,In an gwadi lura garai.

Da dare da rana duk a iske,Hanqurin nazari garai.

27

Page 28: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Ga tufa da littaffansa har-,Ga jiki akwai tsabta garai.

Wanki shi kai wanka shi kai,Xakinsa ko shara garai.”

(baiti na 14 – 27)

Haka kuma, ya faxakar a kan abubuwan da ake gudun

xalibai da su a lokacin da suke neman ilimi, kamar

a inda yake cewa:

“Almakiri na nan daban,Shi kam halin qyama garai.

Ibilisu na shaixanu na,An gane taurin kai garai.

Mutakabbiri na makiri,An gane girman kai garai.

Ga fakon amana shi da ve-,Ra xai yawan varna garai.

Ko an yi foro ba shi ji,Halin batsalci ag garai.

Babba da yaro xai garai,Duk babu mai girma garai.

Tsararsa bai da tagomashi,A cikinsu don fitina garai.

Ga twakara da yawan faxa,

28

Page 29: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Haka nan yawan qara garai.

Tcintce gare shi da tcegumi,Haka nan yawan qarya garai.

Ko ya faxi mu ba mu amsa,

Don yawan qissoshi garai.

Da cikin aji da cikin gari,Kowa shi nemi tsari garai.

Mugum hali varnar mutum,Ko da akwai ilimi garai.

Balle daqiqi na balidi,Babu amfani garai.

A cikin aji in an shiga,Abada yawan barci garai.

Ai gwamma kwananai zama-,Falken yawan yaya garai.

Fashi shikai bai zakkuwa-,Bisa lokaci makara garai.

Luro da bakinai wa ma-,Su dave akwai gamtci garai.

Ga jikinsa littaffai tufa-,Nai ko’ina dauni garai.

Wada ba shi wanka ba shi wan-,

29

Page 30: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Ki kun ji har wari garai.(baiti na 35 – 53)

Almajiraina kun ji ho-,Rona ku sa kunne garai.

Ga gargaxi ku riqa shi,Jalli na yawan riba garai.”

(baiti na 74 da na 75)

A taqaice, waxannan baitocin sun nuna mana irin

faxakarwar da Wazirin Gwandu ya yi wa xalibai a kan

yadda ya kamata su zama a lokacin da suke neman

ilimi.

4.1.3 Faxakarwa a kan Aure Aure dangantaka ce halastacciya tsakanin mace da

namiji wadda ake qullawa bayan wasu sharuxxa (Ali,

2012). Aure muhimmin abu ne a zamantakewar kowace

al’umma. Zamantakewar aure a al’ummar Hausawa ta

tattara abubuwa masu yawa da suka shafi lokacin

auren da ma kafin a yi shi. An rubuta waqoqi da

dama da suke faxakarwa a kan zamantakewar aure da

ma muhimmancin da auren ke da shi ga zamantakewar

Bahaushe. Saboda haka, a nan, za mu nazarci wasu

30

Page 31: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

waqoqin da ke faxakarwa a kan aure da

zamantakewarsa.

Sambo Wali Basakkwace ya rubuta waqa mai suna

‘To Da Ke Nike’, inda yake faxakar da al’umma a kan

aure. Alal misali, a baitin waqar na 3 ya ce:

“Wannan da yat tafo da shari’atai, Yab bar abin karatu hujjatai, Gare shi munka gano farillatai,

Ciki munka gane aure Sunna na.”

A nan, Sambo Wali ya faxakar da al’umma cewa fa

aure Sunnar Manzo (SAW) ce. Daga nan kuma sai ya ci

gaba da faxakar da al’umma cewa, aure fa Sunna ce

mai qarfi, sannan kuma duk wanda ya vata aure, to

yai vanna. Ga dai abin da ya ce:

“A tabbatar da amre aikin nan, Sunna muwakkada mai qarhin nan, Wannan da tak kusanci farillan nan,

Kowa ka vata aure yai vanna.”(baiti na 6)

Haka kuma, daga baiti na 7 zuwa na 12, Sambo Wali

ya faxakar da samari da ‘yanmata waxanda suka yi

ilimi ko suke da sana’a a kan su yi aure. Saboda da

yawa musamman a wannan zamani da ake ciki, samari

31

Page 32: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

da ‘yan mata kan qi aure saboda sharholiya da suke

yi a makarantu da sauran wurare.

“Farko kiran nikai yaran yanzu, Tun dag garin ga har bisa markazu, In Zuljalali ya sa kun wanzu,

Kowanku mai buqatar amre na.

Kai wanga ka yi tarin ilminka,Kai wanga ka tsaya da sana’arka,Wancan da yay yi gona don kanka,

Amre kukai ku gane misalina.

Ku karkato ku gane larura na,In kun riqa da gaske ibada na,Na gane dai cikar talitta na,

Ba wai mutum ba kai ko icce na.

Don Allah mallama am ji jawabina,Daxa ko ki so shi ko ki ga aibina,In na faxe shi na san haqqan na,

Ilminki babu amre shibci na.

Ilminki babu amre sharri na,Shaixan ka xunguza ki cikin vanna,Ki yo ta ba ki dubin aibi na,

Kullum sai faxin kikai injoyin na.

Sai rad da kig ga ke rasa mai son ki,Duk wanda kin nufa bai dubin ki,Mai son ki dauri ya bar shawar ki,

Sannan ki sa kira wayyo kaina!”

32

Page 33: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

A zamantakewar Hausawa, sau da yawa mace kan ce

tana son namiji da aure ko namiji ya ce yana son

mace da aure, amma daga baya sai xaya ya yaudari

xaya, ko da kuwa an qulla yarjejeniyar aure a

tsakaninsu, ana jiran lokaci. To, irin wannan

zamantakewar ma Sambo Wali ya yi faxakarwa a kanta,

a inda yake cewa:

“Zavar shi tun da sauran siffarki,Ki yo bixar miji da mutuncinki,Da hankali da kyawon kirkinki,

Waxanga masu sa miki haiba na.

In ke bixa kula da mutunci nai,Sa alqawar tsarikke amana tai,Sa gaskiya zamanku ya yo daidai,

Ita gaskiya tsare ta wujuban na.”(baiti na 14 da na 15).

Haka kuma, Sambo Wali ya faxakar a kan irin matan

da ya kamata a gujewa wajen nema aure, a inda yake

cewa:

“Ja gaskiya na Abdu yi kwancin ka, Mai hankali ya bar mamakin ka, Bari son abin da yac cika huskarka,

Dattako za ka bi ga bayanina.

Katse-vace ka bar sn xaukar ta,Haka macce in yabanyar jibji ta,

33

Page 34: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Amren irin su duk lalata ta,Kway yo shi mai gamo da hasara na.

Har mai yawan xumi ka yi shakkar ta,Har wadda anka ce mai harshe ta,Gama da macce in mai yawo ta,

Amren guda cikinsu musiba ta.

Wuyyinka duniya akushin-talla!Kowaz zage da son ta yana qwalla,Ka bayyana kamar wada kam mela,

Amren xiya ga macce jidali na.”(baiti na 23 – 26)

A zamantakewar Bahaushe, wasu iyaye mata suna nuna

kwaxayi a wajen aurar da ‘ya’yansu mata, wanda irin

wannan kan kai ga gurvacewar tarbiyyar ‘ya’yan nasu

har su kai ga aikata vanna. Sambo Wali ya faxakar

da ire-iren waxannan iyaye a kan irin wannan

xabi’ar. Ga dai abin da yake cewa:

“Ke wagga mai xiya am ba ki kyauta ba, Ke vata goma xai ba ki gyara ba, Ba ki bar xiyanki sunka yi Sunna ba,

Wata ran su qulla cuta jazman na.

Abin da munka so ba mu samu ba,Kirki gare su ban ga alama ba,Abin da kab bixa in ba ka samu ba,

34

Page 35: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Don Allah kak ka gyarasa yin vanna.

‘Yar tsohuwa nuhinki la’ihi na,Nuhin a runguma miki naira na,In haihuwa garinku sana’a na,

Ke mu garinmu aure Sunna na.”(baiti na 27 – 29)

Haka kuma, akan sami gardama da ce-ce-ku-ce da

neman yin kasayya a lokacin da ake neman aure a

zamantakewar Hausawa. Ire-iren waxannan kan kai

wasu da zuwa wurin malami ko boka don neman magani.

Sambo Wali ya faxakar da mutane musamman maza game

da irin wannan neman auren.

“Amre da gardama bari amren nan, Maccen a ja ka ja kai bari maccen nan, Ko ka yi magani don bai yi nan,

Amre da magani wani aibi na.

Amren kasayya ba amre na ba,Bai zan a yo wani buxi ba,Vannar zama yakai ba ku gane ba,

Sai an yi an gama a ga illa na.”(baiti na 34 da na 35)

A zamantakewar aure ta Hausawa, dole ne a kiyaye

haqqi. Miji dole ya kiyaye haqqin matarsa, ita ma

dole ta kiyaye haqqin mijinta. Sambo Wali a waqarsa

35

Page 36: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

ta ‘To Da Ke Nike’ ya faxakar a kan haqqin

zamantakewa na aure, inda yake cewa:

“Mata ku lura al’adun vanna, Waxanga masu nakkasa haddi na, Ku kula riqon mazanku abin qamna,

Mata wajen zamansu ra’iyya na.

Maza ku bai wa mata haqqinsu,Ciyar da su da shansu lalurarsu,Tufan jikinsu har bisa duba su,

Kan gwargwadon zamanku wujuban na.

Ku zan kula ku xauki lalurarsu,Dukkan abin da yaz zama haqqinsu,Wasa gami da motsa nishaxinsu,

Na so ku san zaman ga ibada na.

In ban da ku da wa suka walawa,Bayan da ku da wa suka hutawa,Da wa mavuvvugarsu ka motsawa?

Ku san hakan ga sai ku bi qaulina.

Ku dai maza ku tattara shawarku,Ta zan wuri guda ga iyalinku,Duk sad da kunka tashi nishaxinku,

Ku zo gare su ya fi ku bar vanna.

Mata ku luri kun fita sirdinku,Kun bar abin da shi a ‘aikinku,Kun kamma barkata da mutuncinku,

Mi za ku yi ku lura da furcina?

Maccen qwarai ta kama mutuncinta,

36

Page 37: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Tsaron jikinta dag ga shiririta,Har ‘yan uwa su xaura misalin ta,

To kun ji gaskiya ga bayanina.”(baiti na 38 – 44)

A qarshe, saboda mata su fahimci faxakarwar da yake

musu a kan haqqin mazansu, sai ya bayar da misali

da matarsa a kan irin yadda take kula da shi.

“Ni na Abdu Sambo mijin Salmu, Maccen da tar riqan har nik kamu, Kullum yini ta dama min kamu

Sannan ta zwazwafar da abincina.”(baiti na 54)

Hausawa suna yin auren mace fiye da xaya, wato mace

biyu ko uku ko huxu10. Idan aka samu irin wannan

zamantakewa ta auren mace fiye da xaya, akan sami

kishi tsakanin mata. Abdulqadir Babajo ya yi

tsokaci a kan irin wannan zamantakewa tare da

faxakarwa game da kishi, a waqarsa ta ‘Mikiyar

Zuhudu’.

10 Wannan tsarin zamantakewa na auren mace fiye da xaya, wato xaya kobiyu ko uku ko huxu, ya samo asali ne daga Qur’ani Maigirma Sura ta 4Aya ta 3.

37

Page 38: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

“Wasu mata sukan yi hauka domin gudunkishiya,

Mata sun haxe cikin ra’ayi ba su sonkishiya,

Kishi mai yawa yakan sa zawata kamarqwaya,

Musamman wacce za ta fi su kyau dayawan kaya.”

(baiti na 95)

4.1.4 Faxakarwa a kan Sada ZumunciA zamantakewar Hausawa, akan sada zumunci tsakanin

‘yan uwa da abokai. Irin wannan sada zumunci yakan

kawo qaunar juna tsakanin al’umma. Wataqila saboda

haka ne, marubuta waqoqin Hausa suka rubuta waqoqi

a kan sada zumunta. Ko dai su rubuta waqa mai nuna

sadar da zumunta ko kuma su rubuta suna masu

faxakarwa a kan sadar da zumunta.

Za mu dubi wasu baitoci da suke nuni ga sadar

da zumunta a zamantakewar Hausawa. Ala misali,

Aqilu Aliyu a cikin waqarsa ta ‘Amsa Ga Wasiqa Ta

Sha’irci’ ya ce:

“Cikin zancen ga ba gilli, A warwarebuxe ba qulli,

Kaxan mun sami ma hali, Mu je mu ziyarci mafalali,

Na ilmi ba na nauyi ba.

38

Page 39: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Fasaha Hausa ba shakki, Tana gode wa janzaki,

Fa Alqalinmu mai aiki, Zumunci mai yawanxinki,

A kullum bai taqaita ba.(baiti na 23 da na

24)

A waxannan baitoci, Aqilu Aliyu ya yi qoqarin nuna

mana cewa, mu riqa yin ziyara (kamar a inda ya ce

‘mu je mu ziyarci ma falali’), saboda zumunci yakan kawo

haxin-kai a zaman tare (zumunci mai yawan xinki). Su ma

Alqali Bello Gixaxawa Xangaladiman Wazirin Sakkwato

da Alhaji Sanusi Xanbaba Kano sun yi amfani da waqa

domin qara danqon zumunta a tsakaninsu, kamar haka:

Wasiqar Sanusi ta Ranar 24-7-1983

“Sanusi Haji xan Baba,Ya dawo don ya gaishe ka.

Muhammadu Bello Alqali,

A yanzun ga ni garkakka.

Idan ka ce da ni na shigo,In maka yanzu labbaika.”

Amsar Wasiqar Sanusi ta Ranar 24-7-1983

39

Page 40: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

“Maraba Sanusi xan Baba,Alo lale a gaishe ka.

Shigo zamna mu xan yi batu,Da murna ga sakin fuska,

Maraba haqiqa na gode,

Yawan ladabinka na so ka,

Gidan ga shigo kana da rabo,Zama ya zan na babanka,

Ka aikata duk abin son ka,Na alher duk ka bar shakka,

Ka bar tsoro ka bar tuhuma,Amincin namu mun ba ka,

Fa tammat sai mu dakanta,Daxa kai sai ka yo barka.”

A taqaice, waxannan waqoqi guda biyu, sun nuna mana

yadda ake sadar da zumunta da yadda ya kamata a

tarbi baqo ko wanda ya zo sada zumunta.

4.1.5 Faxakarwa a kan Nuna Kishin HarsheHausawa suna amfani da harshen Hausa a

zamantakewarsu ta yau da kullum. Amma kuma haxuwa

40

Page 41: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

da wasu baqin harsuna ya sa sun fara samun koma-

baya ko qyama da yin amfani da harshensu na Hausa a

zamantakewar tasu, musamman ma ‘yan boko. Saboda

haka ne marubuta waqoqin Hausa suka riqa rubuta

waqoqi don faxakarwa game da nuna kishin harshen

Hausa, musamman a zamantakewar yau da kullum. Ala

misali, Aqilu Aliyu ya yi irin wannan faxakarwa a

kan nuna kishin harshe a cikin waqarsa mai suna

‘Hausa Mai Ban Haushi’, kamar a inda yake cewa:

“Ga gargaxi ya zuwa gare ku zumaina,‘Ya’yan Arewa da wanda duk ke

Hausa.(baiti na 2)

Qwazo ya kyautu da mu mu nuna kuzarin,Inganta harshen namu shi ne Hausa.

Ku mu bar kasala sai mu himmatu kunji,

Zazzage dantsen nuna kishin Hausa.(baiti na 6 da na

7)

Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka,Ya irin na kaka nasa can mai nisa.

Ku sani Bature ba shi qin Turanci,In ya game da kininsa ko a makasa.

41

Page 42: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

(baiti na 18 dana 19)

Abu namu ne mu riqe shi kankan ya fi,In mun yi wasa dole zai mana

nisa.”(baiti na 24).

4.1.6 Faxakarwa a kan Ma’amalar SiyasaA zamantakewar Hausawa akwai siyasa. Siyasa

ma’amala ce tsakanin mutane, wadda kan kawo ci gaba

ko akasinsa. Saboda haka, akwai buqatar faxakarwa a

irin wannan ma’amala ta siyasa. Faxakarwar kan iya

kasancewa ta cikin gida, wato ta faxakar da mutane

a kan manufofin jam’iyyar siyasa, ko ta gama-gari,

wato faxakar da mutane yadda ya kamata su riqa yin

ma’amalar siyasa ko faxakar da shugabannin da aka

zava a qarqashin mulkin siyasa game da yadda za su

gudanar da mulkinsu.

Idan muka dubi waqar Alqali Bello Gixaxawa ta

siyasa mai suna ‘Siyasa Zamanin Salama NPC’, za mu

ga cewa, cike take da faxakarwa ta cikin gida, wato

42

Page 43: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

yana faxakar da mutane a kan su zama ‘yan jam’iyyar

siyasaru. Ga kaxan daga baitocinta:

“Batun kalimar Salama zan faxa ma,Ka gane shi ka sa ka zamo da himma.

(baiti na 5)

Idan ka gane wanga irin bayani,Fa ka san bin salama as Salama.

Daxa in ka fahimta ina faxa ma,Ka zan yin addu’a ga mutan Salama.

(baiti na 17 da na18)

Ku bar Akashan Guruf birnin gururi,Biyar su shina hana ka zaman Salama.

Fa ‘yan kurxinsu lura ka san guba ta,Idan ka ci su ba ka cikin salama.”

(baiti na 30 da na31)

4.1.7 Faxakarwa a kan Yin Ta’aziyyaTa’aziyya ita ce gaisuwar mutuwa. A zamantakewar

Hausawa, idan mutum ya mutu, bayan an yi

jana’izarsa, akan yi zaman makoki. A wannan zaman

43

Page 44: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

makokin akan yi ta’aziyya ga waxanda aka yi wa

mutuwa. Saboda haka, ta’aziyya ma wani vangare ne

da ya shafi zamantakewar al’ummar Hausawa.

Akwai waqoqin Hausa rubutattu da suke yin

faxakarwa a irin wannnan zamantakewa ta ta’aziyya.

Wasu daga cikinsu suna nuna yin ta’aziyya. Wasu

kuma suna faxakarwa a kan muhimmancin yin

ta’aziyyar ga waxanda aka yi wa mutuwa. Ire-iren

waxannan waqoqi na ta’aziyya suna da yawa. Wasu

marubuta waqoqin sukan kira waqar ta’aziyya da

marsiyya. A waxannan waqoqi, akan faxakar da mutane

a kan su riqa yin tunani game da mutuwa da kuma

nuna alhini ga waxanda aka yi wa mutuwa. Kamar

yadda Alqali Bello Gixaxawa ya faxa a cikin waqarsa

ta ‘Marsiyyar Sarkin Musulmi Hassan Xan Mu’azu*’:

“Yau zucciyata ta tuna,Don ya kamata ta tuntuni.

Bisa xan Mu’azu da yaw wuce,Gwarzonmu hasken zamani.

(baiti na 3 da na 4)

Allah shi gafarta mishi,Shi tsarai da tsutsa had da ni.

Shi tsarai Nakiri da Munkaran,

44

Page 45: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Furcinsa gunsu na mumini.

Allah shi shasai kausara,Tabkin da ba shi da tsantsani.

Allah shi yo mishi gafara,Jama’ar Musulmi had da ni.

Don Jaili don Usumanu don-,Manzo na qarshen zamani.

Wussai siraxi nan da nan,Hasken Muhammadu zai gani.

Cetas shi ceci Mu’azu don-,Jama’ar Musulmi insu had da na

aljani.”(baiti na 18 – 24)

A qarshe, waxannan vangarori na zamantakewa da muka

kawo nau’o’in waqoqinsu tare da yin taqaitaccen

sharhi a kan faxakarwar da suke yi ga al’ummar

Hausawa kaxan ne daga cikin vangarorin zamantakewa.

To, amma duk da haka, mun ga cewa, nau’o’in waqoqin

vangarorin zamantakewar da muka kawo sukan zama

waqoqin faxakarwa ga al’ummar Hausawa, musamman

idan aka nazarci sharhin da muka yi a kan wasu daga

cikin baitocin waqoqin.

45

Page 46: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

5.0 KammalawaDuka-duka, wannan aikin namu ya yi tsokaci ne a kan

yadda waqoqin zamantakewa kan zama waqoqin

faxakarwa ga al’ummar Hausawa. A cikin aikin mun

bayyana ma’anar waqa ta la’akari da ra’ayoyin

masana a kan ma’anar waqa. Mun ga rabe-raben waqa

da kuma taqaitaccen tarihin samuwar rubutacciyar

waqa. Haka kuma, mun bayyana ma’anar zamantakewa da

kuma wasu daga cikin nau’o’in waqoqin zamantakewa.

Da yake vangarorin zamantakewar yawa ne da su. Su

ma kuma waqoqin yawa ne da su. Faxakarwa ma mun

bayyana ma’anarta, sannan daga qarshe, muka yi

nazarin yadda waqoqin zamantakewa kan zama na

faxakarwa ga al’ummar Hausawa. Wato yadda waqoqin

kan faxakar da al’ummar Hausawa a kan gyaran hali

da neman ilimi da aure da sada zumunci da nuna

kishin harshe da ma’amalar siyasa da kuma yin

ta’aziyya.

46

Page 47: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

ManazartaAbdulqadir, Xandatti (1979) Waqoqin Jiya Da Yau. Lagos:

Thomas Nelson (Nigeria) Limited.

47

Page 48: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Ali, Bilkisu Yusuf (2012) ‘Yanayin Turken FaxakarwaA Waqoqin Baka Na Zamani’. Takardar da akaGabatar don Neman Shawarar Ci Gaba da RubutunKundin Digiri Na Biyu, a Sashen Koyar daHarsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’arBayero, Kano.

Auta, Aminu Lawan (2008a) ‘Rubutattun WaqoqinFaxakarwa a kan Jigon Ilimi a Qarni naAshirin’. A cikin 2nd International Conference on HausaStudies: African and European Perspectives. Kano: Centrefor the Studies of Nigerian Languages, BayeroUniversity.

Auta, Aminu Lawan (2008b) ‘Rubutattun Waqoqin Hausana Faxakarwa a Qarni na Ashirin’. UnpublishedPh.D Dissertation. Bayero University, Kano.

Bargery, G.P. (1934) A Hausa – English Dictionary and English– Hausa Vocabulary. London: Oxford UniversityPress.

Bunza, Aliyu Muhammad (1994) Yaqi da Rashin Tarbiyya,Lalaci, Cin Hanci da Karvar Rashawa cikin Waqoqin AlhajiMuhammadu Sambo Wali Basakkwace. Lagos: IbrashIslamic Publications Centre Limited.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar BayeroKano (2006) Qamusun Hausa. Zaria: ABU Press.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar BayeroKano (1979) Waqa A Bakin Mai Ita. Littafi Na Biyu.Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

48

Page 49: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu DanfodiyoSakkwato (2006) Bargon Hikima: Diwanin WaqoqinXangaladiman Wazirin Sakkwato Alqali (Dr.) Muhammadu BelloGixaxawa. UDU Press.

Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu DanfodiyoSakkwato (2006) Gizama Gogan Waqa: Diwanin WaqoqinAlhaji (Dr.) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916 – 2000).UDU Press.

Dangambo, Abdulqadir (2007) Xaurayar Gadon Fexe Waqa:Sabon Tsari. Kano: KDG Publishers.

Gusau, Sa’idu Muhammad (2003) Jagoran Nazarin WaqarBaka. Kano: Benchmark Publishers.

Junaidu, I. da ‘Yar;aduwa, T.M. (2007) Harshe daAdabin Hausa a Kammale Don Manyan MakarantunSakandare. Ibadan: Nazareth Press Limited.

Muhammad Xalhatu (edita) (1986) Fasaha Aqiliya. Zaria:Northern Nigerian Publsihing Company.

Sadiq, I.A. (1990) ‘Nazari a kan Jigon RubutattunWaqoqin Ilimin Zamani’. Unpublished B.A.Dissertation. Bayero University, Kano.

Waqoqin Hausa na Northern Nigerian PublishingCompany, Zaria (1972).

Waqoqin Mu’azu Haxeja na Northern Nigerian PublishingCompany, Zaria (1970).

49

Page 50: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Umar, M.B. (1980) Nazarin Waqoqin Hausa. Zariya: HausaPublications Centre.

Yahaya, Ibrahim Yaro (1988) Hausa A Rubuce: TarihinRubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Kamfanin BugaLittattafai Na Nigeria Ta Arewa.

Yahaya, Ibrahim Yaro da Dangambo, Abdulqadir (1986)Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern NigerianPublishing Company.

Yahya, Abdullahi Bayero (1997) Jigon Nazarin WaqarBaka. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yusha’u, Nasiru (2012) ‘Zamantakewar IyaalinHausawa A Tatsuniyoyin Hausa’. Takardar da akaGabatar don Neman Shawarar Ci Gaba da RubutunKundin Digiri Na Biyu, a Sashen Koyar daHarsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’arBayero, Kano.

RatayeA nan qasa, ratayen wasu waqoqi ne na zamantakewar

al’ummar Hausawa.

Waqar To Da Ke Nike

Ta

Muhammadu Sambo Wali Basakkwace

50

Page 51: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

1. Allahu la’ilahwa illallah,Na yo salati inda Rasulullah,Da Alihi da dukkan Ahlullah,

Na gode Jallah don Mai’iko na.

2. Kiran nikai Gwani mai kama min,In na kirai Shi Shi zai karva min,In yo salati gun mai ceta min,

Na tabbata Muhammadu Jigo na.

3. Wannan da yat tafo da shari’atai, Yab bar abin karatu hujjatai,Gare shi munka gano farillatai,

Ciki munka gane aure Sunna na.

4. Mun gano gaskiyar manzancinka,Don mun gani cikin Qur’aninka,Ya zo tari bisa ga Hadisinka,

Liwali da yin sadaki tilas na.

5. Sannan a kammala a bixo shaidu,Duk sad da mai du’a’i yas sadu,Da su a qulla aure sai shaidu,

Taro a xaura aure Sunna na.

6. A tabbatar da amre aikin nan,Sunna muwakkada mai qarhin nan,Wannan da tak kusanci farillan nan,

Kowa ka vata aure yai vanna.”

7. Farko kiran nikai yaran yanzu, Tun dag garin ga har bisa markazu,

51

Page 52: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

In Zuljalali ya sa kun wanzu,Kowanku mai buqatar amre na.

8. Kai wanga ka yi tarin ilminka,Kai wanga ka tsaya da sana’arka,Wancan da yay yi gona don kanka,

Amre kukai ku gane misalina.

9. Ku karkato ku gane larura na,In kun riqa da gaske ibada na,Na gane dai cikar talitta na,

Ba wai mutum ba kai ko icce na.

10. Don Allah mallama am ji jawabina,Daxa ko ki so shi ko ki ga aibina,In na faxe shi na san haqqan na,

Ilminki babu amre shibci na.

11. Ilminki babu amre sharri na,Shaixan ka xunguza ki cikin vanna,Ki yo ta ba ki dubin aibi na,

Kullum sai faxin kikai injoyin na.

12. Sai rad da kig ga ke rasa mai son ki,Duk wanda kin nufa bai dubin ki,Mai son ki dauri ya bar shawar ki,

Sannan ki sa kira wayyo kaina!

13. To yanzu shawara zan bayarwa,Gare ki ban da hujjar voyewa,Amren dole ya wuce ki ga qullawa,

Ki zavi wanda kig ga amini na.

14. Zavar shi tun da sauran siffarki,

52

Page 53: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Ki yo bixar miji da mutuncinki,Da hankali da kyawon kirkinki,

Waxanga masu sa miki haiba na.

15. In ke bixa kula da mutunci nai,Sa alqawar tsarikke amana tai,Sa gaskiya zamanku ya yo daidai,

Ita gaskiya tsare ta wujuban na.

16. In waiwaya ga aure tushenai,In qwalqwalo tarihin tarihinai,In bayyana shi don ku ji faila tai,

Ku sha ku wantsala ga tahukka na.

17. Amre haqiqa so at tushe nai,Tsaurin zama ka jawo illa tai,Matan gari ka haddasa vaci nai,

Shexan ka xunguza su ga yin vanna.

18. Amre abin bixar alheri na,Abin bixar a samo rahama na,Gyara gare shi babbar hanya na,

Aljanna za ta kai ku haqiqan na.

19. Zan karkata cikin tarihi nai,Don na tuno da Adamu tsagi nai,Nan anka qirqiro Hauwa’u nai,

Da ganin ta yas sani alhairi na.

20. Yay yo salati shi gun jika nai,Wannan da zai taho ga zuri’a tai,Yak karkaxo abinci abinci nai,

Yab ba ta wanga kun ga sadaki na.

53

Page 54: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

21. Shixar su gun qasa yas sada su,Kan saduwarsu yak kuma yaxa su,Sun yo zama da su da iyalinsu,

Shi wanga kun ga tushen amre na.

22. Habila ko batun qurbani nai,Akan batun Labila qanwa tai,Qabila yay yi mugun aiki nai,

Wannan musabbabin jayayya na.

23. Ja gaskiya na Abdu yi kwancin ka,Mai hankali ya bar mamakin ka,Bari son abin da yac cika huskarka,

Dattako za ka bi ga bayanina.

24. Katse-vace ka bar sn xaukar ta,Haka macce in yabanyar jibji ta,Amren irin su duk lalata ta,

Kway yo shi mai gamo da hasara na.

25. Har mai yawan xumi ka yi shakkar ta,Har wadda anka ce mai harshe ta,Gama da macce in mai yawo ta,

Amren guda cikinsu musiba ta.

26. Wuyyinka duniya akushin-talla!Kowaz zage da son ta yana qwalla,Ka bayyana kamar wada kam mela,

Amren xiya ga macce jidali na.

27. Ke wagga mai xiya am ba ki kyauta ba,Ke vata goma xai ba ki gyara ba,Ba ki bar xiyanki sunka yi Sunna ba,

Wata ran su qulla cuta jazman na.

54

Page 55: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

28. Abin da munka so ba mu samu ba,Kirki gare su ban ga alama ba,Abin da kab bixa in ba ka samu ba,

Don Allah kak ka gyarasa yin vanna.

29. ‘Yar tsohuwa nuhinki la’ihi na,Nuhin a runguma miki naira na,In haihuwa garinku sana’a na,

Ke mu garinmu aure Sunna na.

30. Daxin zama ga macce da ilminta,Yat tabbatar da kyawon kirkinta,Wani bai zuwa gare ta ya lotsa ta,

In ka ga tai xumi don aure na.

31. Tubabbiya ku aure ta Sunna na,Amma ku tabbata ta tuban na,Idda ga mai barin zina shari’a na,

Don savo a tuba zancen Allah na.

32. Amma kula fa karuwa tarko ta,In tar riqe mutum sai an qwata,Don kar ka sa qafarka katawa ta,

In ta buge farutta shike nan.

33. Ga bindiga da sabon xurinta,Duk wanda bai iya ba ya rava ta,Da ma haqaqqiyar harsashe ta,

Gun wanda yat tava ya yo vanna.

34. Amre da gardama bari amren nan,Maccen a ja ka ja kai bari maccen nan,Ko ka yi magani don bai yi nan,

55

Page 56: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Amre da magani wani aibi na.

35. Amren kasayya ba amre na ba,Bai zan a yo wani buxi ba,Vannar zama yakai ba ku gane ba,

Sai an yi an gama a ga illa na.”

36. Da abukkiya da kwarto zozozo-,Suke tun da wance ta ce sai in zo,Wallai raba su mallam yo qwazo,

Sirrin zamansu mai kashe amre na.

37. Ban san abukkiya ga shari’a ba,Don ban ganat cikin Ijima’i ba,Ba ta zo ga kowane littafi ba,

Vanna takai ga amren dangina.

38. Mata ku lura al’adun vanna,Waxanga masu nakkasa haddi na,Ku kula riqon mazanku abin qamna,

Mata wajen zamansu ra’iyya na.

39. Maza ku bai wa mata haqqinsu,Ciyar da su da shansu lalurarsu,Tufan jikinsu har bisa duba su,

Kan gwargwadon zamanku wujuban na.

40. Ku zan kula ku xauki lalurarsu,Dukkan abin da yaz zama haqqinsu,Wasa gami da motsa nishaxinsu,

Na so ku san zaman ga ibada na.

41. In ban da ku da wa suka walawa,Bayan da ku da wa suka hutawa,

56

Page 57: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Da wa mavuvvugarsu ka motsawa?Ku san hakan ga sai ku bi qaulina.

42. Ku dai maza ku tattara shawarku,Ta zan wuri guda ga iyalinku,Duk sad da kunka tashi nishaxinku,

Ku zo gare su ya fi ku bar vanna.

43. Mata ku luri kun fita sirdinku,Kun bar abin da shi a ‘aikinku,Kun kamma barkata da mutuncinku,

Mi za ku yi ku lura da furcina?

44. Maccen qwarai ta kama mutuncinta,Tsaron jikinta dag ga shiririta,Har ‘yan uwa su xaura misalin ta,

To kun ji gaskiya ga bayanina.

45. Sai in wuce ga auren al’adu,Don ko gare su sai an sa shaidu,Gama da qa’idodi qayyadaddu,

In an cika su ya zama amre na.

46. Ai na tuno ana auren golmo,Aikin da za yi bisa kai komo,Waxansu ko suna xaurin kalho,

Kan qa’ida ko ko noman na?

47. Don hankali ya kwanta kai waye,In ga al’amurra na tauye,Waxansu har suna amren kaye,

To amren Nasara amren zobe na.

48. Fanni irin na aure tsari nai,

57

Page 58: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Was san iyakaci da jimilla tai,Mu dai gare mu mun san qima tai,

Mun tabbatar da amre Sunna na.

49. Dubinmu kar mu koma wawaye,Mi yaf fi kyau mu lura mu bar maye,Don duk da masu tsahi tsuntsaye,

Kowansu masu tsarin amre na.

50. Tsuntsu da tsuntsuwa suka yawonsu,Wajen kiyo su xora nishaxinsu,Su je cikin gije su yi kwancinsu,

Ba yamusti gare su bale vanna.

51. Ga shamuwa tana ga hamisinta,Shi am mijinta shi aj jigonta,Gauraka sad da tar rasa gagunta,

Ta dangana da amre shike nan.

52. Koma zuwa ga dabbobi duba,Amre gare su bai rasa tsari ba,Ba a yo mutum da tsarin dabba ba,

Tsari na hankali na shari’a na.

53. Tammat na Abdu ya cika waqa tai,Yai godiya ga wanda ka kama mai,Ya yo salati inda Nabiyyi nai,

Saboda shi salati abin yi na.

54. Ni na Abdu Sambo mijin Salmu,Maccen da tar riqan har nik kamu,Kullum yini ta dama min kamu

Sannan ta zwazwafar da abincina.

58

Page 59: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

55. Kai mai bixar ya san ni da shiyarmu,Bazzar Magaji can kaka iske mu,University gari muka aikinmu,

Centre Matattarar addini na.

Waqar Qalubale

Ta

Aqilu Aliyu

1. Qulun qulufit abu dunqule,Qalau na qale qalubale.

2. Kacinci-kaci miye abin,Da ke yaxo kuma dunqule?

3. Ya watsu ya barbazu tattare,Da rassa ga shi a mulmule.

4. Kaxan ka ture zuciya,Da Ilmu ake qalubale.

5. Abin da ya kyautu da mu mu yi,Mu himmatu har mu kashangale.

6. Mu qyale buqata kowace,Cikin ilmi mu shugulgule.

7. A ofis ko a cikin sito,A kowane gu ya maqalqale.

59

Page 60: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

8. Mu je mu tsaya mu fito da shi,Mu jajjawo shi mu qwaqule.

9. Ina magana kan ilmu ne,A nan qumshinsa na walwale.

10. Da kyau haka bai zama aibu ba,A kan ilmi mu zaqalqale.

11. Cikin nema nasa kar mu ji,Kasala kar mu katangale.

12. Kaxan ba ka gane ilmu ba,Ba ka cure ba ka dunqule.

13. Ba ka shafe ba ka lailaye,Ba za ka naxa ba ka mulmule.

14. Kaxan ba ilmu gare ka ba,Cikin sha’ani kai ne bale.

15. Kana kallo a yi ban da kai,Ganinka da ji ka dabalbale.

16. Baqar magana a yi ma ka ji,A dole ka zam ka daqile.

17. Rashin Ilimi in yai daqu,Ba a ga fara ba a dunqule.

18. Kiran mu nake jama’a mu ji,Mu amsa kar fa mu daqile.

19. Mu lura da saurin zamani,Ya dafe kansa ya walwale.

60

Page 61: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

20. A gurguje ba ya waiwaye,Mu nace bin sa a zazzale.

21. Mu zabura shi ya fi kyau da mu,Mu cure qasarmu mu dunqule.

22. Da gaske mu zage damtsuna,Mu hau ilimi mu maqalqale.

23. A nan ya kyautu na tambaya,Abin da ya harxu a walwale.

24. A yau qoshi wa ye da shi?Mutan ilmi suka makkale.

25. Su wa ye masu faxa a ji,Da sun magana ta daddale?

26. Cikon girma wa ke da shi?Mutan ilmi suka kammale.

27. Ashe masana su ne gaba,A komi ba su zama bale.

28. Abin da ya nemi ya wargaje,Da shi ilmi kan mulmule.

29. Mu tashi mu miqe qyam tsaye,Mu nemi sani mu fi’ittile.

30. Ina wani in ba ilmu ba,Da in lamari ya dagule.

61

Page 62: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

31. Ya kwakkwave ya dabalbale,Yana nema ya jagwalgwale.

32. Da zai tsamo shi ya fid da shi,Irin rikicinsa ya walwale?

33. Fasaha ba ta wadar mutum,Kaxan ilmi ya xangale.

34. Kaxan da sani ba a tsiya,Rashin sa ya sa a tavalvale.

35. Marar ilimi ba ya gaba,A bar shi a baya masha-tile

36. Juhala noman barka ne,Da baya da baya ya zoqale.

37. Marar ilmi dattijo ne,Irin na biri mai xan kwale.

38. Cikin zarafin assha da tir,Marar ilmi ya zaqalqale.

39. Wajen madalla babu shi,Da an jawo shi ya zumvule.

40. Fa duk sha’aninsa daban-daban,Marar nasara a jagwalgwale.

41. A nan bana dai kam babu shi,Bale baxi can ya tavalvale.

62

Page 63: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

42. Kaxan an duba shi kuwa,Akan rasa inda ya maqqale.

43. Fa ba shi a nan kuma babu can,Kawai shi dai ya gantale.

44. Akwai zaqin baki garai,Marar ma’ana da yawa tule.

45. Da farko bai nem ilmu ba,Da ya zai gane yau bale?

46. Shakwab da Lakwab da Na-makkale,A yau za ai ta a daddale!

47. A wannan garnannen buki,Na waqoqin qalubale.

48. Salamu alekum sai baxi,Aqilu Aliyu ya hamdale.

Waxansu Baitoci daga cikin Waqar Mikiyar Zuhudu

Ta

Abdulqadir Babajo

Mataye halinsu cuta kissa da kitsa qarya,In ka ba su babu tabbas ka hana su ja baya,Ga ko ruwan ido zara tare da sassarya,

63

Page 64: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

Duk su gama su je su zavo danja wutarbaya.

Duk mai gaskiya gudun sa suke sun fi son qarya,Buqatocinsu sun yawa sun faye son sayen kaya,Su sai yauqi su sai qarafa da qerau da

zinariya,Ba su isar su har suna qulla qawa da

dillaliya.

Wasu mata sukan yi hauka domin gudun kishiya,Kishi mai yawa yakan sa zawata kamar qwaya,Mata sun haxe cikin ra’ayi ba su son kishiya,

Musamman wadda za ta fi su da kyau koyawan kaya.

Idann da rabon ka kalli kishin mata haxe datsiya,

Sai kun tsufa kai da matarka ka auri yarinya,Amarya za ta sha azaba sharri gami da wuya,

Kan girkinta za a vata mata shi ta zub damiya.

Wata ran za ka turare har sabulu a miya,‘Ya’yayenka za a sa su su raina ta ai ta tsiya,Ita kuma za a sa ta rena ka ta rinqa ba ka

wuya,Labarin abubuwan baya a farfaxi ta jiya.

64

Page 65: 'Wakokin Zamantakewa kan zama Wakokin Fadakarwa ga Al'ummar Hausawa'

65