Top Banner
Dr.Abdullah Bahammam Hukunce-Hukuncen Biyan Buqata
7

Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

Oct 21, 2021

Download

Documents

dariahiddleston
Welcome message from author
This document is posted to help you gain knowledge. Please leave a comment to let me know what you think about it! Share it to your friends and learn new things together.
Transcript
Page 1: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

Dr. Muhammad Sani Umar MusaShaikh Nura Sani Muhammad

bita

Muhammad Rabi'u Umar Musa R/lemo

tarjama

ZakkahAzumiSallah

Karantar da hukunce-hukuncen musulunci a sauqaqe

Fiqihun ibada a cikin hotuna

Dr.Abdullah Bahammam

Hukunce-HukuncenBiyan Buqata

Page 2: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

28

Kashen RuwaKashen Ruwa

5

Abin Da Ya Wajaba Yayin Biyan Buqata1. Suturce al'aura daga idon mutane yayin biyanbuqata, saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم) :«Kariya tsakanin ganin aljannu da al'aurar 'yan adam shi ne idan xayansu zai shiga banxaki ya ce, "Bismillahi» (Tirmizi ne ya rawaito shi).

2 – Kiyaye tufafinsa da jikinsa daga najasa, saboda abin da ya tabbata Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya wuce ta wajen waxansu qabubura guda biyu, sai ya ce, «Haqiqa ana yi musu azaba, amma ba saboda wani abu mai wahala ba ne, shi dai wannan ya kasance ba ya –Abin da ake nufi da ba ya tsarkaka daga fitsari shi ne ba

ya nisantarsa kuma ba ya kiyaye kansa daga gareshi kaffa-kaffa wajen fitsari» (Abu Dawud ne ya rawaito shi).

3 – Yin tsarki da ruwa ko hoge, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce,

«Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan zai tafi biyan buqata, ni da wani yaro sa’ana muna xaukar buta da sanda Sanda ana nufin xan qaramin mashi, sai Manzon Allah ya yi tsarki da ruwa (bayan ya gama)» (Bukhari

da Muslim ne suka rawaito shi).

Hukunce-Hukuncen Biyan Buqata

T s a r k i

Hukunce-Hukuncen Biyan Buqata.

Abin da ya wajaba yayin biyan buqata

Abin da ya haramta yayin biyan buqata

Abin da ake so yayin biyan buqata

Abin da ake qi yayin biyan buqata

Tsarkin ruwa da tsarkin hoge

Menene tsarkin ruwa da na huge

Hikimar tsarkin ruwa da huge

Hukuncin tsarkin ruwa da huge

Sharaxin abin da za a yi tsarkin huge da shi

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha

Page 3: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

29

Abin Da Ya Haramta Yayin Biyan Buqata1. Fuskantar alqibla, ko ba ta baya yayin biyan buqata a fili. Idan kuwa a cikin gini ne to abin da ya fi kada a fuskanceta, saboda faxin Manzon Allah Idan kun zo wurin biyan buqatarku kada ku» (صلى الله عليه وسلم)fuskanci alqibla kada kuma ku ba ta baya, ku kalli gabas ko yamma» (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi)

2. Biyan buqata akan hanyar mutane, ko inuwarsu ko wurin da suke taruwa, saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم) «Ku ji tsoron wurin tsinuwa guda biyu". Sai suka ce, "Menene masu jawo tsinuwa guda biyu?" sai ya ce, "Wanda yake biyan buqata akan hanyar mutane, ko inuwarsu» (Muslim ne ya rawaito shi)

3. Shiga banxaki da Alqur'ani, saboda yin hakan wulaqanta littafin Allah Maxaukakin Sarki ne.

4. Yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudu, kamar ruwan tafki wanda ake yin wanka a cikinsa, saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم)«Kada xayanku yayi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudu, sannan ya yi wanka da shi» (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi)

Fitsari a cikin ruwan da ba ya guduYa tabbata cewa yin fitsari a ruwan da ba ya gudu yana haifar da cutar Kurkunu.

Duba littafin "Axxibun Nabawiy Fi Dau'il Ilmil Hadis" Na Giyasul Ahmad

Biyan buqata a fili cikin sahara

Biyan buqata akan hanyar mutane

Shiga banxaki da qafar hagu

Fita daga banxaki da qafar dama

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha

Page 4: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

30

Kashen Ruwa

Abin da ake so yayin biyan buqata1. Nisantar mutane yayin biyan buqata a sahara ko fili

2. Ya ce yayin da zai shiga banxaki: «Bismillah, Allahumma Inni A'uzu bika minal Khubthi walkhaba'ith»

(Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

3. Gabatar da qafar hagu yayin shiga banxaki, da gabatar da qafar dama yayin fitowa

4. Ya ce yayin da zai fito : «Gufranaka» (Abu Dawud

ne ya rawaito shi).

Abin da ba a so yayin biyan buqata1. Yin magana yayin biyan buqata, ko magana da wasu sai dai in da wata buqata, saboda hadisin xan Umar - Allah ya yarda da shi – ya ce, wani mutum ya wuce ta wajen Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana bawali, sai ya yi masa sallama, amma bai amsa masa ba. (Muslim ne

ya rawaito shi)

2. Shiga banxaki da abin da yake akwai ambaton Allah a jikinsa, sai dai in ana jin tsoron sacewa, saboda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) «ya kasance idan zai shiga banxaki sai ya cire zobensa» (Abu Dawud ne ya

rawaito shi).

3. Shafar gaba da hannun dama, ko yin tsarki da shi, saboda faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) «Kada xayanku ya riqe gabansa da hannun damansa idan yana fitsari, kada kuma ya shafi bayan gida da damansa» (Bukhari

da Muslim ne suka rawaito shi.)

4.Yin fitsari a cikin ramuka, don kada wata dabbar ta cuce shi ko shi ya cuce ta.

Yin magana yayin biyan buqata

Shiga banxaki da abin da yake xauke da sunan Allah

Yin fitsari a cikin ramuka

Shiga banxaki da Alqur'ani

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha

Page 5: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

31

Yin fitsari a tsayeManzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya hana yin fitsari a tsaye, sai dai idan ya aminta cewa tartsatsin fitsarin ba zai vata shi ba, to ya halatta yayi, saboda hadisin Huzaifa – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya zo wajen bolar Bola : Wurin da ake zubar da qazanta. wasu mutane sai ya yi fitsari a tsaye» .

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha

Page 6: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

32

Kashen Ruwa

Fa'ida :Ba a yin tsarkin don an yi tusa

Yin tsarki da ruwa ya fi yi da dutse, saboda ruwa ya fi tsarkake wa da fitar da najasa.

Tsarkin Ruwa Da Tsarkin Hoge

Hikimar Yin Tsarkin Ruwa Da Na Hoge1 – Don samun tsarki da gusar da najasa

2 – Saboda samun tsafta da nisanta daga abubuwan da suke kawo rashin lafiya

Tsarki da hannun dama :Ba ya halatta a yi tsarki da hannun dama, saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم) «Kada xayanku ya riqe gabansa da hannun damansa idan yana fitsari, kada kuma ya shafi bayan gida da damansa»(Muslim ne ya rawaito shi)

Tsarkin hoge Shi ne gusar da abin da yake fita daga gaba ko dubura da hoge ko makamancinsa

Tsarkin ruwaShi ne gusar da abin da yake fita daga gaba ko dubura da ruwa mai tsarki

Hukuncin Tsarkin Ruwa Da Tsarkin HogeAn shar'anta yin tsarki da ruwa, saboda hadisin Anas xan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan zai je biyan buqatarsa, sai ni da wani yaro sa’ana mu xaukar masa ruwa da sanda, idan ya gama sai yayi tsarki da ruwa» (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

Ya halatta a taqaita a kan tsarkin dutse kaxai, da sharaxi guda biyu:

1 – Ya zama fitsarin ko bayan-gidan bai wuce wurin ya saba fitowa daga cikinsa ba, idan kuwa ya wuce to lallai sai an yi amfani da ruwa.

2 – Tsarkin hogen ya zama da hoge guda uku ko sama da haka, har gabansa ko duburarsa ta tsarkaka daga najasa.

Sharuxxan abin da ake tsarkin dutse da shiA. Ya zama mai tsarki, ba ya inganta a yi da abu mai najasa.

B. Ya zama halataccen abu, ba ya inganta da haramtaccen abu.

C. Ya zama mai tsarkake wurin najasar.

D. Kada ya zama qashi ko kashin dabbobi, Salman Afarisi – Allah ya yarda da shi – ya ce, «Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya hana mu mu fuskanci alqibla da bayan-gida ko bawali, ko kuma mu yi tsarki da hannun dama, ko mu yi tsarki da duwatsun da ba su kai uku ba, ko mu yi tsarki da kashin dabbobi ko qashi» (Muslim ne ya rawaito shi).

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha

Page 7: Fiqihun ibada a cikin hotuna - al-feqh.com

33

E – Kada ya zama abu ne mai qima, kamar abinci, ko wata takardar da aka rubuta wani abu mai qima a cikinta.

Daga cikin abin da ya halatta a yi tsarkin dutse da shi akwai : duwatsu masu tsarki, hankici, takarda mai tsarki, da qyalle mai tsarki

Yin tsarki da abinciYin tsarki da Hankici

Yin tsarki da takarda mai qima

Yin tsarki da duwatsu

Yin tsarki da qashiYin tsarki da qyalle

http

s://w

ww

.al-f

eqh.

com

/ha

https://www.al-feqh.com/ha