Top Banner
Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM · MUTUN UKU NE SUKA FARA HARAMTA BOKO DA YIWA GWAMNATI TAWAYE A NIGERIA (1) Marwa Maitatsine, kafiri ne, mai bautar dodonni, 'dan asalin kasar Kamaru ne, har aka hallakashi bai shiga musulunci ba, makiya addinin Musulunci ne suka dauki kwangilarsu suka tura su Kasar Masar domin su koyi ilmin adddinin Musulunci su dawo Nigeria su halakar da al'ummar Musulmi, kamar yadda tsohon sakataren kungiyar CAN Professor Dawud Ojobe ya bayyana a Daarul Hadeethis Salafiyyah Zaria Nigeria (DHSN), ana saura kwanakin da basu wuce 7 ba kafin a hallaka Malam Albaniy Zaria (2) Ibrahim Yakubu Zakzaki: yayi da'awar Boko Haram sosai, harma yaki yin bautar kasa (NYSC), yace shi baya bauta ma kasa, ya janyo yaran musulmai su kai ta yaga result din su, daga baya da ya ga 'ya'yan shi sun taso, yana so suci abinci da boko, sai yayi kwaskwarima ya shigar dasu karatun boko alhali yace dagutu ne. (3) Muhammad Yusuf: shugaban kungiyar Boko Haram, wannan hoto da kuke gani da farin rawani a kanshi, shi ne a lokacin yana shi'ah, yana wakiltar Zakzaki a jihar Yobe da Maiduguri, suna haramta shiga boko da barranta daga gwamnati Daga baya yazo sunnah, yana so ya yada wannan akida, sai Malaman sunnah suka mai caa, su kai mukabala dashi, irin su Marigayi Malam Jaafar Kano, dasu Sheik Isah Ali Ibrahim Pantami, Ash-sheikh Dr Idris Abdul'aziz Dutsen-Tanshi Bauchi, suka kure shi a mukabala, amma yaki ya tuba, ya rinka kafa hujjojin shi da aya da hadisi da maganganun Malamai irin su Ibnu Taimiyyah, dasu Shehu dan Fodiyo, da su Alkadi Iyyad akan barnar shi, Malamai suka ce karya yake, babu abinda ya hada shirman shi da ayoyin Qur'ani, Hadisai da maganganun Malaman Musulunci. A takaice dai Zakzaky shine ya fara dora Muhammad Yusuf akan haramta boko da rigima da gwamnati. ALHAMDULILLAH yanzu dai dukkan su asirin su ya tonu, an fahimci 'yan ta'adda ne, an kuma soke kungiyoyin nasu na ta'addanci ~Nasiru Ahmad Bawa Yaa Allah Ka tsarkake mana Kasarmu Nigeria daga burbushin kungiyoyin ta'addanci da masu tallafa musu ta kowace hanya Amin See Translation
8

Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...

Feb 01, 2022

Download

Documents

dariahiddleston
Welcome message from author
This document is posted to help you gain knowledge. Please leave a comment to let me know what you think about it! Share it to your friends and learn new things together.
Transcript
Page 1: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...

Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM · MUTUN UKU NE SUKA FARA HARAMTA BOKO DA YIWA GWAMNATI TAWAYE A NIGERIA (1) Marwa Maitatsine, kafiri ne, mai bautar dodonni, 'dan asalin kasar Kamaru ne, har aka hallakashi bai shiga musulunci ba, makiya addinin Musulunci ne suka dauki kwangilarsu suka tura su Kasar Masar domin su koyi ilmin adddinin Musulunci su dawo Nigeria su halakar da al'ummar Musulmi, kamar yadda tsohon sakataren kungiyar CAN Professor Dawud Ojobe ya bayyana a Daarul Hadeethis Salafiyyah Zaria Nigeria (DHSN), ana saura kwanakin da basu wuce 7 ba kafin a hallaka Malam Albaniy Zaria (2) Ibrahim Yakubu Zakzaki: yayi da'awar Boko Haram sosai, harma yaki yin bautar kasa (NYSC), yace shi baya bauta ma kasa, ya janyo yaran musulmai su kai ta yaga result din su, daga baya da ya ga 'ya'yan shi sun taso, yana so suci abinci da boko, sai yayi kwaskwarima ya shigar dasu karatun boko alhali yace dagutu ne. (3) Muhammad Yusuf: shugaban kungiyar Boko Haram, wannan hoto da kuke gani da farin rawani a kanshi, shi ne a lokacin yana shi'ah, yana wakiltar Zakzaki a jihar Yobe da Maiduguri, suna haramta shiga boko da barranta daga gwamnati Daga baya yazo sunnah, yana so ya yada wannan akida, sai Malaman sunnah suka mai caa, su kai mukabala dashi, irin su Marigayi Malam Jaafar Kano, dasu Sheik Isah Ali Ibrahim Pantami, Ash-sheikh Dr Idris Abdul'aziz Dutsen-Tanshi Bauchi, suka kure shi a mukabala, amma yaki ya tuba, ya rinka kafa hujjojin shi da aya da hadisi da maganganun Malamai irin su Ibnu Taimiyyah, dasu Shehu dan Fodiyo, da su Alkadi Iyyad akan barnar shi, Malamai suka ce karya yake, babu abinda ya hada shirman shi da ayoyin Qur'ani, Hadisai da maganganun Malaman Musulunci. A takaice dai Zakzaky shine ya fara dora Muhammad Yusuf akan haramta boko da rigima da gwamnati. ALHAMDULILLAH yanzu dai dukkan su asirin su ya tonu, an fahimci 'yan ta'adda ne, an kuma soke kungiyoyin nasu na ta'addanci ~Nasiru Ahmad Bawa Yaa Allah Ka tsarkake mana Kasarmu Nigeria daga burbushin kungiyoyin ta'addanci da masu tallafa musu ta kowace hanya Amin See Translation

Page 2: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...
Page 3: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...
Page 4: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...
Page 5: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...

Datti Assalafiy Yesterday at 4:33 AM · BBC HAUSA KUNYI BABBAN ABIN KUNYA Kafar yada labarai mallakin yahudu da nasara wato BBC Hausa sun wallafa labari kamar yadda sukace wai Muhammad Yusuf shugaban kungiyar Boko Haram ya cika shekaru 10 da shelanta jihadi A cikin rahoton na BBC sun kawo tarihin Muhammad Yusuf sukace wai yayi karatu a jami'ar Musulunci dake garin Manzon Allah (SAW) wato Madina Sannan BBC Hausa sunce Muhammad Yusuf karantarwan Sheikhul Islam Ahmad Abdul-Haleem Ibn Taimiyyah Al-harran yake bi, da kuma karantarwan Sahabban Manzon Allah da sauran bayin Allah magabatan kwarai (Salafussalih) Bayan da BBC suka saki wannan labari mai cike da tarin Qarya, sharri, yarfe, batanci da rashin adalci, sai aka fara musu raddi, an kira har wakilansu a waya aka nuna musa Qaryan dake cikin tarihin Muhammad Yusuf da suka wallafa, shine sai a shirin hantsi na yau da suka gabatar sun bada hakuri, sannan sukace a gafarcesu wai sunyi kuskure Daga cikin mafi girman kuskuren da BBC sukayi shine cewa wai Muhammad Yusuf yayi karatu a jami'ar Madina, alhali wannan Qaryace tsagwaronta BBC suka zuba Ni ban yarda kuskure bane abinda BBC sukayi, nafi gamsuwa akan cewa da gangan sukayi domin su yiwa jami'ar Musulunci batanci kamar yadda suka saba yiwa Kasa mai tsarki batanci domin cimma wata boyayyar manufa ta su Babbar kafar yada labarai na duniya irin BBC hankali ha zai kama ba ace sunyi kuskure wajen fitar da tarihin mutumin da suka shekara 10 suna tattara tarihinsa, mutum wanda yake mafi hatsari a cikin al'umma wanda ya kawo bala'i da masifa a doron kasa Bayan haka, Qarya suke da sukace Muhammad Yusuf karantarwan Ibnu Taimiyyah yake bi, babu alakar Boko Haram da karantarwan Ibn Taimiyyah balle kuma Sahabban Manzon Allah (SAW) Sannan BBC Hausa sunyi rashin adalci da suka kawo tarihin Muhammad Yusuf ba tare da sun hada da Maigidansa Zakzaky ba, Muhammad Yusuf a gurin Zakzaky ya fara koyon akidar karatun Boko Haramun ne, da haramcin aikin gwamnati karkashin gwamnatin Demokaradiyyah, domin Muhammad Yusuf sai da ya zama wazirin Zakzaky na jihar Yobe gaba daya Kuma ana cewa ai Muhammad Yusuf a hannun 'yan izala yayi karatu bayan ya bar Maigidansa na farko Zakzaky, Izala ne ta kawo Boko Haram, to su kuma 'yan Izala wa ya kawo su, amsar shine darikun sufaye, don haka mas'alar ba wai tana ga kungiya bane, domin duk inda anka je aka dawo za'a samu 'yan izala sun fito daga kungiyoyin dariku ne, daidai ne idan akace darika ne ta kyankyashe 'yan Izala, saboda haka asalin akidar Boko Haram Muhammad Yusuf ya samota daga gurin Zakzaky ne, wanda shi kuma Zakzaky ya karbo kwangila ne daga Kasar Iran Gareku BBC Hausa, idan cikakken tarihin Muhammad Yusuf da kuma tarihin Boko Haram, da 'Yan Kanamma da Ansaru kuke bukata to kuyi magana a nuna muku inda zaku samu, tarihi ne hadi da bincike mai zurfi wanda aka share shekaru sama da 12 ana tattarawa, kuma za'a wallafashi idan lokaci yayi, amma ba nan kusa ba Daga karshe ina kira gareku da ku ji tsoron Allah BBC Hausa, ku kiyaye, kunga yadda kuka zubar da mutuncin kanku a sanadiyyar kokarin yin batanci ga wadanda kuke adawa da su

Page 6: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...

Muna rokon Allah Ya bamu ikon yin adalci wa kowa Amin See Translation

Page 7: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...
Page 8: Datti Assalafiy August 1 at 12:25 AM MUTUN UKU NE SUKA ...