Top Banner
AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM AMANA TA CE DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT WWW.AREWAFLEX.COM 1 WHATSAPP 08105882006
82

amana ta ce - ArewaFlex

Jan 19, 2023

Download

Documents

Khang Minh
Welcome message from author
This document is posted to help you gain knowledge. Please leave a comment to let me know what you think about it! Share it to your friends and learn new things together.
Transcript
Page 1: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

AMANA TA

CE

DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT

WWW.AREWAFLEX.COM

1 WHATSAPP 08105882006

Page 2: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

By ©Rash Kardam Safiyan yau Jumma‟ah antashi da sanyi, kasancewa

yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassan ne ya fito daga dakinsa cikin manyan

kaya, yayi shiga ta alfarma, dining yaje ya zauna hajiya fatima ne zaune

tana jiran mai gidanta, bayan yazauna ta masa sannu, ya amsa cikin sakin

fuska ya kalleta yace Fatima ina Auta take, tace tana sana‟arta har yanzu

inaga bata farka ba, cikin kulawa ya kalli fatima yace hajiya ina fada miki

kulum ki ringa kula min da Auta, cikin daure fuska tace Alhaji kulum haka

kacewa yarinya duk ta san garce sakalci ya mata yawa ta girma aman

kamar wata jaririya, Alhaji ya nisa yace hmm fatima akwai maganar dana

ke so muyi da Auta da Ammar, ana cikin haka sai ga Ammar ya shigo cikin

ladabi ya gaidasu, suka amsa da sakin fiska, ya kalli Hajiya yace Mum ina

Auta tace tana daki tana sana‟ar ta na baccin sage barinje na tasota,

Ammar ya mike da nufin komawa falon Abba yace aaa Ammar bama haka

ai kaima dana ne don ina jinka ajikina kazauna mu karya tare, ana haka

sai ga Mum tafito Auta na biye da ita, yau anyi sa‟ah harta yiwanka da

wuri bata tsaya baccin gadonta ba, cikin zazza kar muryanta ta gaida Dad

dinta da Mum san nan Ammar cikin kulawa ya amsa, kusa da Dad ta

zauna suka karya bayan sun gama suka koma falo, dad ya zauna mum na

gefensa Ammar na kasa tana zaune, Autar Hajiya na kusa da ita, Abba ya

dago cikin muryansa mai sa sanyin jiki kalo daya zaka masa ka gane yana

cikin taradadadi, Zainab ya ambata, Autar Hajiya sai da taji sunan har

cikin ranta tasan dad baya kiran sunan ta haka kurum sai da dalili, ta

amsa da na‟am dad, Dad ya kalle ta yace Zainab ina son insanar dake

wani abu, sanana inaso ko bayan raina Auta kikasance mai hakuri da

biyya ga wanda zakiyi tarayya dasu san nan ki rike mutuncinki, karki sake

kiyi watsi da tarbiyan da muka miki, nasan ki amma ina son ki kara rike

mutun ciki, ki rike Adu‟ah a duk inda kike, Zainab idonta duk ya ciko da

kwala don tun da take da dad bai taba mata zance makamancun haka

ba,maganar dad ne ya katse mata tunani, Ammar ya kira ya amsa, dad

yaci gaba dacewa Ammar kai kadai na yarda da kai acikin wayanda

mukayi tarayya, kaine ka rike min “AMANA” ta don mutane yanzu ba

yarda, san nan ko bayan raina banyarda ka bar Zainab ba ga

“AMANARTA” na baka kai kadai nasan zaka kula min da ita, cikin sanyi jiki

2 WHATSAPP 08105882006

Page 3: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Ammar yace dad mai yasa kake irin wan nan maganan Dad yayi

murmushin manya yace Ammar da Zainab atare, yace kukadai zan sanar

da maganan nan kusani akwai wayanda suke min barazanan kashe ni da

iyali na akan dukiyata, da nanema da gumi na,nikuma naki amsamusu

sabida mutuwa da rayuwa tana hannun Allah, ba wanda ya isa ya kashe

wani face da izinin Allah. Cikin damuwa Auta da Ammar sukacewa

suwaye dad murmushi yayi yace ka kyalesu kawai zan sanar muku amma

bayanzu ba, hajiya ma tayi musu nasiha sosai, dad ya mike ya fita hajiya

tayi daki Auta kuka takeyi Ammar ne ya rarrasheta sai da tayi shiru kafin

ya fito harabar gidan nan sale suka fara masa kallon bansa da kuma zaka

sani yau, musa kam dariya yayi sosai kafin yace mun kusa ganin karshen

wan nan rigima taka da kafafa kamar gidan ubanka, an samu gidin zama

sai nuna isa kamar dan gd ko ta kansu bai bi ba ya wuce dakinsa shidai

yana fatan Allah ya tsaresa da sharrin masu sharri. Dad bai dawo ba sai

kusan 10 lokacolin Auta tayi bacci hira sukayisosai da Hajiya kafin yace

bari ya watsa ruwa bayan yayi wanka hajiya fatima tafito cikin kayan

baccinta mai daukar hankali ta nufi dakin Alhaji sun yi hira sosai kafin

suka kwanta, Misalin karfe 2 gari yayi shiru sai sai hadirin daya hadu gari

yayi baki2nan take ruwa ya tsinke sosai kamar da bakin kwarya, kowani

mutum na gidansa yana bacci, wata bakar jeep ce mai bakar glas na ga

tanufo gaye din gidan Alhaji Al-hassan sai da suka fito duka kwan kwasa

wa mai gadi ya bude musu suka shiga, duk da ruwan da akeyi bai dame

musuba kalo daya zaka musu kasan ba alkairi bane, atare dasu, sun rufe

fidkokinsu da marks bakinsu da kwayan ido su da kofar hancinsu ke waje,

magana sukayi tsakaninsu wanda sukazo a jeep dasu sale da musa, da

alaman dai sun san da zuwansu, bayan sun gama ne, suka nufi cikin gida

ko da suka shiga dakin Alhaji suka nufa suka samesi da hajiya suna tare,

Ammar ko yatashi tun karfe daya yasoma sallah nafilan da yasabayi duk

dare bayan ya idar duk da ruwanda da akeyi yaji alamar shigowan mota

da sauri ya leka nan yaga wasu da bakaken kaya sun rufe face dinsu duk

abunda sukayi na kallonsu nan yaga sun ciro bin diga, yana kalon sun

shiga ya bude kofar dakinsa cikin sanda ya kwanta a kasa yadoma tafiya

da ciki kamar yanda sojasuleyi a fagen yaki cikin fulawas ya soma bi ko da

3 WHATSAPP 08105882006

Page 4: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

yaje ta kofar baya ya shiga yayi sa‟ar kofar abude take nan ya tura a

hankali, daman duk wanda yashigo ta baya dakin Auta zai fara samu don

haka ya tura kofar a hankali. yaganta tana bacci, a hankali ya soma

tashita, cikin ikon Allah ta mike ba gyan gyadi, ihu zata sa ya toshe

bakinta yace Auta kina jina wasu mutane sun zo gidan nan da kuma da

alamar wayanda dad yafa da.suna son kashesa ne, nan cikinta ya fara

rawa idontaya ciko da kwalla, yace dau hijab diki mu leka muga don

musan abinyi, kasa dauka tayi shi ya daukar mata ko ta kalmi bata tsaya

dauka ba suka nufo falo a han kali suka leka, nan suka ga abunda ya

razana su dad ne aka samasa bindiga da Hajiyasuna kara lekawa nan suka

ga fuskan Baba Sani da yayansa iyaka, alokacin sukadana kuna mar

bingigan tass kake ji karan harbin bindiga, nan take auta tasaki kara atake

suka juyo gurin da sukaji kara suna fadin suwaye suka nufo gunsu. Yan

uwa amin afuwa za ku ga ban2 dana farkon dana soma sakewa, yanzu na

dawo da lbr daga tsakiya neamin afuwainaga hakan watakil zaifi. Shin su

Autar Hajiya da Ammar suna kubuta daga sharrin mutanen nan? bacin

gashi gate din gdn a kulle. Suwaye wayan nan mitanen? Mai nene

alakarsu da Dad? Waye Ammar? Don son jin amsarnan kubiyo Yar Gidan

Kardamawa. Taku akulum mai kaunarku ®WWA® Rash .A. Kardam

[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rash Kardam

Tass kake ji karan harbin bindiga nan take Auta tasaki razananen kara, da

sauri suka juyo girin da sukaji karan suna fadin suwaye, suka nufo gun,

Ammaryana ganin haka yaja Auta tana turjewa ita sai taje gun su Dad da

Hajiyarta, dakyar ya shigarda ita dakinta yasaka key ya kullesu, ga ruwa

sai sauka yakeyi ana tsawa, nan yarasa yanda zaiyi Adu‟ah ya tuno na ne

man tsari daga abokan gaba ya fara karantawa, autakan sai kuka take,

ana cikin haka su Kawu Sani suka iso kofar nan suka fara jijjiga kofar, Auta

ko kara sautin kuka takeyi Ammar bai san lokacin daya daka mata tsawa

tayi shiru don kukanta har cikin zuciyar shi yake tabasa, nan ta damke

bakinta, duk ya rue yarasa ya zaiyi gashi ba hanya, kasu Baba Isiya da sani

su jijjiga kofa ga harbin suketayi, kiris yarage su balla kofarnan take

dabara ta fado masa da sauri yayi gun Waldrop, ya zazzagar da kayan ciki

kasa da kyar ya turo ya jawo ya kawo zuwa bakin kofarya tokare, nan ya

4 WHATSAPP 08105882006

Page 5: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

janyo dress miro shima ya tokare nan ya dafe kansa sai ga wasu zafafan

hawaye:'(:'( ke zuba yana kiran sunan Allah ya kawo musu mafita. A bakin

gate kuwa mai gadi da sale suka leko ganin su Alhaji an sheka kiyama

suka sheke da dariyasukace yau ina kudin ka ya dawo namu, gumus ne

ya fito yace kuba mu karfe ina tunanin akwai wasu agidan nan zamu balle

ko fa, don yar Alhaji na tare da wani Sai a lokaci idi yace

kai:oops::oops:munyi kuskure daya da muka bar dakin Ammar bamu fara

ta kanshi ba barinje na dubo shi, ko da yaje dakin ba ammar nan yace duk

yanda akayi Auta tana tare da Ammar amma bazasu gudu ba, don gidan

nan na rufe ba gurin tsira dariyan mugunta suka farayi, wani katon karfe

suka samo wanda duka daya zasuyi wa kofar su balle, nan suka nufo cikin

dakin da karfen. Ammar kuwa adu‟o‟i yakeyi can ya tuna windo dakin na

glass da sauri ya mike nan ya fara dube2 ba wani karfe a dakin wanda zai

fasa ga shi sukuma sun kusa balle kofa duk ya kalli ko ina na dakin ba

wani abu, sai can ya kalli Bedside drawer, da sauri ya dauko ya zubar da

kayan ciki, ya nufi windon da karfin ya buga tare da bissmila bugu biyu

yayi mai kyau wundon ya balle sosai yanda zasu wuce sai da ya leka ta

baya yaga ba kowa kafin ya dauko Auta ya sanyota ta waje tasauka kenan

yana shirin fita wani kwanban da bai gama balle ba ya yankeshi nan sai ga

jini sosai gashi kwalbar ya shiga sosai har sai da yace washhhhh, lokacin

su baba Sani suka balle kofar suka nufoshi. ®WWA® Rash Kardam

[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Ya balle window din ya fara fitar da Auta kafin ta zo fita

wani kwalban glass a jikin window din ya yanke shi ya shiga sosai, ya ji

zafi harsai da yace washhhh, dai2 lokacin su baba sani suka balle kofa

suka nufo shi cikin zafin nama ya dirka ga jini sai zuba ya keyi sosai, da

sauri Ammar ya yakwanta a kasa ta gefen window, cikin hantsari ya fisgo

Auta ta fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2 da wani dutsi nan ta buge

bakinta sai ga jini, kara tasa yayi sairin toshe mata baki, su gumus da

kawu isiya suna isowa harbi suka fara amma bai kai ta inda su Auta suke

ba, baba sani ne ya ciza yatsa don ya ji haushi ga window ya musu

kankanta baza su iya fita ba da sauri yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri

suka fita ga ruwa haryanzu zuba yakeyi sosai. Ammar na ganin sun bar

5 WHATSAPP 08105882006

Page 6: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

window yayi kokarin rashi ga jiri na debansa don jininsa ya zuba sosai, ga

Auta kuma jiki ba kwari, ya mike yana tan gadi ya dagata kasa tsayuwa

tayijijjigata yayi da kyar sai ta sauke ajiyar hrt kafin ya mikar da ita suna

mikewa suka hango motar su baba sani sun nufosu, nan ya fara janta da

gudu tunda daga hayin rigasa layin waya suke gudu sai da suka wuce

kantin yawo, kafin suka kara gudu dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta

fadi da sauri ya dauketa ganin in yace zai miki hanya zasu kamasa sai yayi

gurin wani sabon gini wanda dogayen ciyawasun bullo agun gabansa

kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan ya kaisu gun ya tsuguna ya tare

Auta da numfashinta ke shirin daukewa abunka da rashin sabo ga razana

don Auta in banda girkida take taya hajiya bata wani wahala, tasaba da

rarrafen carpet tun tube da waya, baran da ta rage ita daya ma Dad da

Hajiya ba irin gatan da basa mata. Su baba sani da suka iso gurin nan suka

fita ga ruwa na sauka sosai duk dube2 da sukayi basu gansu ba, Ammar

kuwa suna gurin a tsugune da ke Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma

ta fito sabida ruwan da ya dameta a gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda

ta hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta danna mata cizo, har saubiyu duk

da zafin da taji tayi saurin damke bakinta, Ammar na ganin haka ya kara

matse bakin nan kuwa kunamar ta kara yanka mata cizo, sai murkususu

take tayi, gumus da duna sukace alhaji ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne

mesu in baku mu kawo maka gawarsu ba to zamu maka da lbr

mutuwarsu, nan suka tafi da motar suka bar su gumus a gurin, sun dade

suna dube2 sosai agun kafin suka soma fita, Autakuwa wuya yayi wuya

bata san lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara da sauri su gumus suka

juyo nan suka fara nufo gurin da sukaji karan, Ammar na ganin haka ya

mike yasoma jan Auta suna kara gaba kawai suka ga kato kogin ruwa ne a

gabansu ga su gumus sun nufosu. Abun gwanin tausayi nikaina Rash

bansan lokacin da na fara zubar da hawaye ba. Allah sarki su Auta da

Ammar Allah ya kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai din Ameen. Sai

dare zakuji ni Taku a kullum mai kaunar ku ®WHW® Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta numfashin ta na

kokarin daukewa da sauri ya sugunaakasa ya ajiyeta acikin tabo ga jini

6 WHATSAPP 08105882006

Page 7: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

yana ta zuba daga hannunsa, Gumus suka nufo su da sauri nan ya harba

bindiganya sake harba wa yaji bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya

wurgar da bindigan akasa ya nufosu ko da yazo daman Ammar na ankare

yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon Allah karfin yazo ma Ammar ya

wurga shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan gumus na ganin haka dake

yana haskasu da touch light, ga shi gumus nata fanjam aruwa dake shi bai

iya ruwa ba, kuma ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun ruwan ko ta kan

su Ammar baibiba ya je gun dan uwansa don ceto rayuwansa, Ammar na

ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma

tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya

auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura

suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba

da tafiya. Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan

ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace

sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka

sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na cirokakai kajimin wayan nan sai

kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar

mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina

yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa. ko da suka isa

nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don

daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan

sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukagaabunda ke faruwa dariya

sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama, Baba sani yace ya ina fatan kun

sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu

inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi

murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka

shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai

dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo

cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan

taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa

kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi

maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina

yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu

7 WHATSAPP 08105882006

Page 8: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka

shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus. ®WHW® Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba

kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko

da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-

hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa

zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota

koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so

zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo

musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku,

nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu

sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa. Da safe

yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwardon haka suka yi

cirko2 gashi jiya anyi ruwasosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji

Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-hassan a masallaci ba kuma duk

rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy

wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don

dukda karan ruwan sama dake zuba naji ihu san nan naji harbin

bindigasun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu

shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga

masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da

tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun

wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi

ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo

suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka

suka fara, alhaji abubakar makocin dad policene nan take ya kira ja mi‟an

tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza

kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi

ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi

ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun

dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi

dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi

8 WHATSAPP 08105882006

Page 9: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar

anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da

baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka

rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan

nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka.

haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike. Ammar da auta

kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don

asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwaba ya kwantar da Auta ya

yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse

ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya

sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam

yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan

taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo

daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba

mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a

hanya.Rash Kardam [9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Motar suka shiga nan mutum min yace

subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi

wa inna ilaihi raji‟un abunda ya furta gashi sunyi nisa sosai, sun shiga jeji

don sun bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba kwari yace wa driver dan

Allah ka tai make mu wlh fitowar gaggawa ne ya kama mu bakosisi ajikin

mu, driver ya narko ashar yayi, aefa baka isaba zan dauko ku a bati ne ba

ko sisi mai na tsada kuma niman kudi na fito, waya sani ko dan iska ne ma

kai kasato musu yarinya inazaka da wannan yar gashi jikinta duk jini,

kalala ta mata rayuwa, ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar ya baci

don tunda yake ba abundaya tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya tsani

zina a rayuwansa mezaisa ya aikata cikin bacin rai yace kaii Malam ya

isheka in har bazaka taimaka min ba karka min wan nan zaton, nan

mutumin yace anyimaka kuma zata fita anan ba wlhsai kabani kudina,

nan ran Ammar yakara baci wai shi dayake nima da guminsa ga kuma

Zainab yar gata gabada baya wai yau sune a wulakance ga shi an kashe su

Alhaji shikenan Zee sa ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji hawaye:'(:'(:'(

wasu na bin wasu, sai a lokacin ya kalli agogon hannusa mai kyau yace

9 WHATSAPP 08105882006

Page 10: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

ma driver bani da kudi amma ga agogona in zaka karba yafi karfin

kudinka, driver yace nagani ko da ya karba yagani yasan zaiyi tsada

dayawa nan yace to shikenan yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku sauka

anan tsabage bacin rai yace barin musauka anan, ya dauki Auta suka fita,

gefen hanya ya kwantar da ita lokacin gari ya waye sosai, sai alokacin

yaga kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma ya kumbura sosai, gashi yayi

ja abunka da farar mace, gindin wata katuwar bishiya yaje ya shinfida

fallen zani ya kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa ga hannusa yana

masa zafi sosai, bayan ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga ruwa don

yasha yakuma ji alwala. Acikin garin kaduna kuma Alhaji Abubakar ko

ince Inspector Abukar shiyatsa akan gawan su dad har akayi zana idarsu

aka kaisu makwancinsu na gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan uwan

dad sun taru a gidan ko da Sadiya yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita

yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba tashiga tashin hankali don su na

shishiri sosai, Inspector Abubakar daya koma gd ya tausaya ma yarsa

bulkisu don kawar Autace sosai tayi kuka kuma nan ta dauki aniyar saita

dau fansa akan duk wanda ya aikata abun, bayan kwana uku da rasuwan

su Dad yan uwansa sukace su duk wanda yayi abun nam sun barshi da

Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har saida Inspector Abubakar yaso ya

ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na uku, tasami Abbanta akan ita ta

canza ra‟ayi daga kan Science courses, yanzu Law zata karanta don

tazama barrister don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta, hakkunta da

cutar da ita da akayi, kuma tace Abba ni ajikina inajin Zee bata mutu ba

ko ga yanayin statement din da aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba

nisan yana tare da ita kuma bazai cutarta ba da yardan Allah don yana da

hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji dadin maganar yarsa Bilisu wanda

ake kita da futuhatul-khai, yamata Adu‟an Alkairi da fatan nasara. Su

baba sani nan suka fara kiciniyan raba dukiyar dad har yaso su samu

sabani da baba isiya akan wanda zai zauna a gidan dad da kyar Baba isiya

ya hakura akan shi za a bashi motar dad babban ya rike. Rayuwa kenan

wai naka najikinka shiyake son ganin bayanka basa tunanin suma zasu

mutu ba tsoron Allah wan nan wani irin zamani ne burin wasu mutanen

su ci “Amana” yan uwa muji tsoron Allah musani Amana tana gefen siradi

10 WHATSAPP 08105882006

Page 11: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

da Zumunci duk wanda ya karya daya aciki to yasan makomarsa, don

ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a kasan gadan siradi duk wanda yaci

amana ko ya bata zumunci ko da ya kusa karshen haye gadanne haka

kugiyar zata finciko shi wasu kafin su isa duk sun yaga naman jikinsu,

„Yasalam‟ yan uwa muji tsoron Allah mu gyara rayuwar mu musan man

zumunci da Amana mu kiyayesu, ya Allah kasa mudace da karshe mai

kyau Ya Allah ka daura mu akan hanya madaidaiciya Ameen. Ammar sai

da yayi tafiya mai nisa kafin ya ga wani rafi nan ya rasa ya zaiyi ya debi

ruwa ya kaima Auta tasha ko zata ji dama2 ga tausayinta shikam kasa sha

ma yayi in har Auta bata sha ba ba zai iya sha ba, ya sanya hannumsa

biyu ya debi ruruwan yanufi gunta tun kan ya isa ruwan ya zube nan yaji

wasu hawaye:'(:'( sun zomasa. Yana zuwa kusa da ita ya ga sai wani irin

nishin azaba takeyi kamar wai shirin mutuwa Ammar baisan lolacin da

yasaki kuka kamar karamin yaro yana cewa Zainab dan Allah kar ki tafi ki

barni ke kadai kika ragemin bani da uwa ba uba, gashi sun kashe mana

Dad da Hajiya in kintafi ina zansa kaina kuka yakeyi sosai da sosai. Nima

Rash bansan lokacin da nasaki kukan tausayi ba. Allah sarki rayuwa juyi2

Allah ka kawo masu Auta da Amar mafita Ameen. ®WHW® Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Nan yasaki kukamai ban tausayi, jijigata ringayi sai yaga

tasaki ba ko alamar motsi atare da ita, da sauri ya dauketa yayi gun rafin

da ita yana isowa yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a gora, tsohon

nan, ganin halin da Ammar ke ciki yasa yace subhanallah bawan Allah mai

yasa meta Ammar kasa magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin wani,

tsohon na ganin halin da Ammar ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da

bisimillah ya watsamata sau 2 nan take ta saki ajiyar zuciyamai karfi,

muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari duk ya mutu, ahankali take magana

sai da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta kafin yaji mai takecewa wayyo

kafarta, ammar da sauri ya riki kafar sai a lokacin tsohon ya l ura da kafan

yace yasalam mugani ya rike kafar wan nan ae cizo kunamane ya daneta,

yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata, ammar ya dauketa suka bi tsohon.

A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani sun shiga sabon rayuwa mai dadi

da dukiyar da suka dade suna mafarkin samunsa, Sadiya sam nataji dadin

11 WHATSAPP 08105882006

Page 12: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

yanda Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan uwansa ba, tunda ba a ga

Autaba kuma hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba, abin duniya duk ya

isheta, haka rayuwa ta kasance musu cikin nishadi har sun manta da

wasu wai su Al-hassan da fatima da wata diyarsu Zainab bare Ammar dan

kallo. Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi tafiya mai nisa sosao kafin

suka shigo wani karamin kauye wanda gidajen ciki baifi a kirga ba, in kazo

gida daya sai kayi tafiya mai nisa kafin ka iske digadaya, ko da suka isa

kofar wani diga an masa rufi da da ciyawa sai katangan kara aka dan

zagaya gidan naki biyu ne a gidan sai dakunan kaji da baru yan kanana da

agwagi, suna sallama wata yar tsohuwa ta fito daga dakin danake zaton

nan ne gurin kwanan su, tace lale maraba baki mukayi, ganin Ammar rike

da joda ga jini ajinsu duka yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan, tsohon

nan yace bakine da sauri ta dauko taburman sakar kaba ta shinfuda

musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho nan daki ya shiga ya dauko wani

yar jakar fata, ya dauko magani da nan ya kama kafar ya matse gun cizon

saiga karin ya fito nan ya sake matsewa har sai da Auta tayi kara ta kan

kame Ammar sai zufa tayi, saida yacire yashafa mata magani, san nan

yasa inna laure ta dafa Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a kofi ya

saka magani yabama Auta da kyar ta iya shan maganin tana runtse ido.

®WWA® Rash Kardam [9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Bayan Auta tasha maganin, sai aka

dawo kan Ammar nan shima ya kuncedaurin da yayi ma ciwonsa, tsohon

nan da naji inna laure nakira da malam, ya dauko wasu magun guna, ya

wanke masa ciwon da wani farin ruwa, nan ya haungo karamin glass ya

shiga hannun, sai da ya dauko aska ya ciro glass din, duk da Ammar na

miji ne sai dana ga indonsa yayi jajazur da alamar yana jin zafi sosai,

baran ciwon ya kwana shiyasa, Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa kanta

tayi tana kuka maras sauti…, wai yau itace a kungurmin kauyen da ko

wuta babu bare ruwan fanfo, kafin asauko gun kwanciya mai kyau, nan

take kalaman Dad dinta ya fado mata, inda yake mata nasihan sa na

karshe akan ta yi hakuri a duk inda tasamu kanta, sabida yanayin rayuwa.

Allah sarki duniya kenan wai ace su baba sani su zasu kashe iyayenta

akan dukiya da son duniya, mai sukamaida zumunci ne ga cin “Amana”

12 WHATSAPP 08105882006

Page 13: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

wan nan wani irin rayuwa ne sam tausayi ya kaurace a idon jama‟a basa

tunawa zasu mutu su koma ga Allah, in har kayi mai kyau zaka taras,

kwanciyan kabari ma akabar mutum dashi babban aiki ne bare ace ka

aikata mumunan abu har akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa inna

ilaihi raji‟un duniya tazo karshe wayan nan abun duk alamun karshen

duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace da karshe mai kyau ameen.

Hawaye ke gan garimata daga idonta, tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana

share mata hawaye, tana daga ido taga Ammar ne, shima hawayen

yakeyi sai alokacin tasamu tasaki kuka mai ban tausayi, shima kukan

yasaki, an rasa mai rarrashin wani. Malam da inna laure sun zuba musu

ido sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada musuba suna cikin tsananin

tashin hankali, nan take ina kaure ta fara hawayen tausayi, malam idonsa

yayi ja sosai, malam kenan akwai tausayi ga taimako. malam yace bawan

Allah kai na mijine ka kasance mai juriya a kowani hali duk da bansan mai

yasame ku ba aman da alama kuna cikin tashin hankali, kuyi hakuri,

kusani duk tsanani yana tare da sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah komai,

zai yi muku saukin Al‟amarin, haka rayuwa take kowa da irin jaraban da

ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya baku ikon ci, Ammar ya amsa da

ameen. Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar bahonta da tsage aka

nane shi ta surka kafin ta kaima auta bayi, sai da ta taimaka mata kafin ta

kaita bayi tafito ta barta nan ta dauraye jikinta, don ruwan da dumi sosai

ya gasa mata jiki kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito inna tasake sama

Ammar ruwan ta kaimishi shima wankan yayi, bayan yafitoa wanka suka

shafa mai dake lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi kadan. Malam ne ya

hau kekensa yaje can kauyen da gabansu anan ake samu shago, yasayo

musu suga, yadawo inna laure ta musu surki mai dumi sosai, don ya ware

musu hanji, abinci ta dauko musu dambu tayi daman, kuma ta danyi da

yawa, san nan Malam ya karamusu da nashi, aiko sunci danbun sosai don

yunwa sukeji, sai da suka gama cin abincin, san nan sukayi god iya ga Allah

da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya juyo ya gode ma Malam, cikin

kulawa malam yace karkada mu ni domin Allah na muku, ita rayuwa

bakan wa zai tai make ka nan gaba, kuma dukiya da dan mitum, da dabba

ba a musu keta, ku kara gode ma Allah ammar sai da yaji kwalla, asai ana

13 WHATSAPP 08105882006

Page 14: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

samun irin wayan nan mutane a zamanin yanzu, Hamdalah yasakeyi ga

Allah da ya ciyar dasu. Inna laure ta gyara daya dakin nan dama da

kyausa, in sunyi baki anan suke kwana, ta kwantar da yar katifar bonun

da ke dakun tayi shinfidi akan gado, inna laure kenan duk da acikin kauye

suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata tsab2 gwanin burgewa, ga

kamala da kyautawa. Malam yace ga daki an gyara zamu kwana da kai

inna laure kuma sai su kwana da kan warka, kafin in Allah ya kaimu waye

wan gari, sai kubamu tarihin ku da abunda ya baroku da gida, Ammar

yace to, Malam ya kara cewa meye suanan ka..? Amar ya nisa yace

sunana Ammar ita kuma kanwata Zainab, Malam yace aaa babban suna

gareta, sunan Mahaifiya ta gareta, Allah sarki Uwata zan kiraki da shi, har

cikin ran Auta taji sunan da irin kauna da suka gwada musu, haka ta shiga

dakin inna laure ta kwanta don huce gajiya. ®WHW® Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Bacci tayi sosai akan yar katifan inna, sai magriba ta

farka tayi sallah, bayan ta idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai laushi

miyar danyan kubiya yaji man shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci suka

koshi, sai da sukayi isha‟i kafin Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta

kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa, Ammar ma dakin suka shiga

shida malam suka kwana, Auta bata farka ba dai asuba da inna ta daga ta

tayi sallah bayan sunyi sallah, ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu

malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don ba halin taya inna girki,… Bata

da lfy, inna ta musu dumame da kunun tsamiya, nan sukaci duk da

damuwan da suke sai da sukayi santi don inna gwanar iya girki ce,… sai

bayan da suka karya kafin malam ya umurci Ammar da ya basu tarihinsa

dana Auta, ammar ya gyara zama nan take idonsa ya kawo hawaye, da

bai zubo ba ya fara dacewa, Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen dan

maiduguri ne iyayena yan mai duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da

baya, baba na ya kasance dan gidan sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu

ya haife su, Uku matabiyu masa matan akwai Ya fanna, da da hajja gana

da Yakura, sai wan babana sunasa hashim sai babana mai suna Sa‟ad,

mahaifina ya taso cikin kulawa da kaunar mahaifinsa kasan cewar yana

da nutsuwa sabani yaya shi da suke uba daya wato hashim, hakan yasa

14 WHATSAPP 08105882006

Page 15: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

suka tsani baba na da mahaifiyarsa don shikadai ta haifa sauran hudun

duk yayan kishiyarta ce Hajiya faima,… duk tsanar da suka masa bai

damesa ba ya nimi ilimin boko da na addini bayan ya kammala karatun

degree dinsa ya dawo gd, sai mahaifin sa ya masa Auren gata da

mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja faty mahaifiya kenan ta kasance

mace ce mai kamala da kyautatawa ga hakuri da juriya ga sanin darajan

dan adam, lokacin auren kudin da sarki Abdallah Saraki ya kashe ba

karamin tada hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace ita mai yasa baza

ayi auren danta ba, sarki yace a yanda bai nitsu ba shine shaye2 yar wa za

a hada shi da ita, tun daga wan nan lokacin suka dau tsan gwama suka

daura ma kakata da da mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu ba,

kwanaki sun ja yau wata 5 da auren mahaifina da umma na nan ta fara

laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi, bata son shan ruwan fanfo sai na

rija tunda suka lura da hakan, sukayi makircinsu aka bata ruwan gdn gaba

daya don karta samu na sha, haka kullum sai anje nimota ta a gari don in

bata sha ba tashin hankali ne, haka rayuwa tayita tafiya. Sarki Abdallah

Saraki, ya yanke shawaran sauka a mulki sai daura dana Sa‟ad Saraki akan

mulkin gwaza, tun daga randa sarki ya yanke hukunci, hankali hajiya

fatima ya tashi, nan suka soma shiga bokaye, sai da suka san makircin da

sukayi mahaifina ya dau mahaifiya suka bar garin bashi tun daga lokacin

ba asan inda mahaifina yake ba, bayan tafiyan mahaifina bakin cikin yasa

yagamu da ciwon hawan jini, harya makance da ganan kuma Allah ya

karbi abunsa,…… Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina ba sai kanon

dabo tunbin giwa ko da mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi yan Bauchi

ba fa, nan ya samu wani mutumin kirki ya rikesa a unguwar Dakata, haka

yayi ta rayuwansa da umma na harta cikinta ya kai na haihuwa, nan

laraba ta tashi da matsanacin ciwon mara nan sukayi asibiti, ana kaita ta

haifi danta, tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah ya karbi abunsa, asai

masalan da aka samu lokacin tana mai duguri, maganin da aka a rijiya ta

sha don karta haihu dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta haifen lokacin

ya mata illa sosai, shine sanadin mutuwarta. ®WHW® Rash Kardam

[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Bayan anyi zana idarta matan da babana ke gidan ta

15 WHATSAPP 08105882006

Page 16: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

karbe ni haka ta raineni har na girma na kai 15 yrs lokacin ina secondary

school, haka zamu fita aiki mudan samo abunda zamuci sam baba na yaki

aure, ana cikin haka malam suka shirya komawa garinsu, don suma

mazuwa ne, yan jalingo ne, tunda suka shirya tafiya, mahaifi na yace na

shirya muje muga yan uwansa, tunda ga ranan ya nimi kudin motan

tafiya muka shirya ranan asabar 12 /3/ 2012 muka tafi mai duguri tun a

hanya mahaifina ya ke cemin gabansa na faduwa, ko da muka isa mai

duguri, muka shiga motar gwaza, muna isa yaga masarauta ya canza nan

ya samu lbr rasuwan iyayensa, mahaifiyar sa ma bata dade da rasuwa ba,

gidansu ya watse nan mukayi kuka tare, daga nan yace mu wuce cikin

mai duguri, washegari muna zuwa, cikin garin mun sauka a tasha, kenan

nace ma baba na ina jin fitsari, nan yace inje bayan gidan tashar na tafi

kenan, kafin in dawo naji karan wani abu dammm, gurin ya dau hayaki

asai bomb ne ya tashi tare da mahaifina, Innalilahi wa inna ilaihi raji‟un,

abunda na furta kenan nan aka tattara wayanda suka tarwa tse ki gawan

mahaifina ban samu gani ba tun daga nan na shig gararin rayuwa, kwana

na 2 a mai duguri a tasha na dan samu taimakon kudi na hada da nawa,

nan ji a tasha ana mitar Kaduna haka kurum naji garin ya min, nan

nashiga motar, Kiran sallah da akayi ne ya sasu mikewa malam jikinsa

yayi sanyi alamar tausayi, inna kam harda hawaye Auta kam kuka takeyi

shabe2 don sai yau tasan tarihin Ammar, Bayan sun dawo daga sallah

malam yace su huta sai gobe yaji lbr Auta da zuwan ammar kaduna, nan

inna ta daura musu abinci,.. ta girka musu, dan waken dawa da wake ba

karamin, dadi yayi ba, don sunyi santi inna ta iya daka yaji, don harda yar

bushahen namanta, takesawa acikin yaji sai yayi zakwakwai, gwanin

santi, Da la‟asar haka sukayi sallah sukazo zauna malamyace zashi dibo

ruwa nan Ammar yace zan bishi, suka dau jarkuna zuwa rafi, suna yar

hiran duniya akan abunda ke tafiya gar suka dawo saida sukayi sawu 3

nan inna ta dafa musu ruwan zafi sukayi wanka,… Malam suka fita zuwa

wajen gd, suna fita suka hango yan matan kauyen sun taru a dandali, tun

daga nesa suka fara gulman Ammar yau malam ya samo santalelen

saurayi, wan nan tafara naa ne wancan na nawane, najaat tace kai

kustsaya kuga duk cikin ku kunga da wanda ya dace sai ni, dake duk suna

16 WHATSAPP 08105882006

Page 17: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

tsoronta ba wanda ya tanka, nan malam fa Ammar sukazo suka wuces7

zuwa shagon kauyen, garin suka sayi taliya, malam kenan akwai kokari.

®WWA® Rash Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Suna hira da Malam har suka dawo

gida,…. da daddare basu wani hiraba sanadin hadarin da ya hadu, daki

suka shiga suka kwanta ba a dade ba ruwa ya sauko sosai, haka aka

kwana ana ruwa, da asuba malam sukaje sukayi sallah, inna da zainab

sukayi acikin gd, haka suka yi koko da kosai shuka karya, bayan sun karya

sukayi wanka,.. Bayan sun kan mala komai lokacin gari ya dan sha, kafin

suka fito gidin biyar kofar gdn kasancewar garin ba mutane da yawa, don

gida daya na da rata tsakaninsa da wani gd,.. bayan sun zauna malam ya

bukaci ammar da ya cigaba da lbr sa… Ammar ya cigaba da cewa bayan

na mai dugri mun dau hanyar kaduna, sai dare muka iso kaduna don

driver ma na gudu sosai, ko da muka isa garin kaduna, mun sauka a kawo,

nan kowa ya fita don ya tafi girin da yazo, ina ina tsaye ni da wani a

gefena sai ga mai taxi yazo, yana fadin Abuja Road Magajin, nan mutumin

yace nan zaije, take nima na shiga taxi din munyi tafiya mai nisa ina kale2

don yanayin garin yayi kyau sosai, ahaka dai muka iso magajin gari nan

mutum ya sauka nima na sauka, ko da na fito na ra sa inda zani, hakan

yasa nazo masallaci nayi sallah kafin na bar masallaci don na fara jin

bacci, kofar wani shago na samu na kwanta don na gaji sosai, kwanana 3

a gurin ganin kar mutanen gurin su zargeni yasa na dau ledata na fara

tafiya, nayi nisa sosai kafin naga wani guri mai gine2 na sama ga jama a

sosai, daga nesa naga an rubuta “CHE CHENIA MARKET” da manyan

harufa, nan nasamu na kutsa, kusa da shagon mai takalma na zauna. na

kwana biyu ina zama a gun har na dawo dan aika a gun, abinda na lura a

kwai wani shagon takalma da less da material, saman shagon an rubuta

“ZAINAB FASHION DESIGN” a bunda na lura akwai wani alhajin da ke

yawan zuwa da yarsa wata kyakyawa na karshe, suna sayan kaya ne ko

mai sukeyi ban sani ba, tun da na kalli yarinya naji ta kwan ta min a rai ina

sonta da kanwa, hakan yasa duk randa zasu zo in sun sai kaya zanje in

dauka musu in gaida alhajin ko da babanta zai bani kudi bana karba, sai

yayi da gske nake karba, hakan ya mana masa dadi, har yasoma

17 WHATSAPP 08105882006

Page 18: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

tambayata inane unguwan mu, nan nasoma hawaye ganin haka Alhaji ya

kama hannuna muka nufi motarsa, munyi tafiya mai nisan gske, har na

fara tsoro ko dan yankan kaine, nan nakama adu‟ah neman tsari, mun isa

wani unguwan da ba mutane sosai, sai da mukazo kofar wani katon gd

mai kyau horn yayi aka bude kofar, gate din, gd ba laifi kam yayi kyau

sosai. Munshiga cikin gd mata kyakyawan mace ta fito da murnanta, tana

sannu da zuwa Alhaji, nan ta kalleni, tace Abban Auta ina kasamo wan

nan yaro mai kyau haka, Alhaji yace bari mu zauna tukun. ®WHW® R ash

Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Muna isa gd wata mace kyakyawa ta

fito, tace sannu da dawowa Abban Auta ya hanya, cikin sakin fuska ya

amsa lfylau Alhamdulilah, tace ina kasamo kyakywan saurayi haka, d ad

yace mushiga ciki tukun, Allah sarki dad gwanin taimako, ko da suka shiga

cikin gd abinci ta kawo musu nan Ammar ya faraci daman da dan yunwa

ajikinsa, har saida dad ya tausaya masa sosai, bayan ya sun ci abinci ne

dad yace suje falo koda sukaje nan ya tambayi Ammar mai yasa yake

kuka da ya tambayesa, san nan ina iyayensa, nan idon Ammar yaciko da

kwalla, dad ya rararshesa, Ammar ya basu lbr iyayensa dad saida yayi

kwalla ya tausaya masa, kafin yace ya kwantar da hankalinsa zai rikesa,

bisa “AMANA” nan Ammar yayi godiya dad ya kaishi dakin da ke waje

gefen na masu gadi ya ce ya zauna anan. Dad ya saya ma Ammar kaya

bana wasa ba haka ya cigaba da rayuwa acikin gidansu Auta gashi sun

shaku da Auta sosai, a iya zamansa a gd yanda yasamu lbr a gun dad wata

rana suna zaune ya soma bashi lbrsa dake sun saba sosai2 dad ya ja shi

ajiki,.. Ammar sai da ya kurbi surki mai zaki yaji suga kafin ya ci gaba da

cewa barin baku lbr Auta a takaice Wacece Auta Zee Asalin Alhaji Al-

hasan Kano haifefan dan garin kano ne, zamane ya kawo su kaduna dake

yayi karfi anan yake kasuwancin sa, tun da ya dawo kaduna bayan

rasuwan iyayensa , sai ya dibo yan uwansa ya sasu akan dukiyarsa,

mahaifiyarsh ita kadai ta haifa yayinda yake da yayu yan uba wato Sani da

Isiyaka uwar su daya yayinda Sani shine babba sai Baba isiya ka, Baba sani

yana da yaya 4 Sadiya itace baba sai kabir san nan Anas sai Autarsu

Sa‟dat sun kasance abin so gun iayensu da kulawa Baban Auta shi ya

18 WHATSAPP 08105882006

Page 19: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

dauki nauyin karatun Sady ya hada su da Auta gashi jininsu yazo daya

baka rabasu ko ina taresuke,. Baba isiya kuma matarshi daya da yara 2

Fauziya ana kiranta da pinky sai kan warta faima sina kiranta da faty,

haka rayuwa tayita tafiya. Dad ya kasancr mai yawan taimako da son

talakawa sabanin yan uwasa da ko kyauta yayi sun rinka mita kenan basa

son ganin wani ya rabe shi baran in yana taimaka masa, tun randa suka

san dad ya kawo gdn suka fara hada rai in ko mun gamu zagi da hantara

ba wanda ban sha duk in kauda kaina sabida dad ya rikeni da “AMANA”

hakan nazamo mai aika a gd kuma wani lokaci mina tare da auta da Bilisu

kawarta yar makwabtasu wato yar inspector Abubakar bilki kasancean

sunan maman babanta ne shiyasa suka boye sunan ana kiranta da futha

wato fatuhatul-khair, ba karamin shiri futha da Zee Auta sukeyiba, haka

Ammar yana ji da ita. Hajiya Aysha itace maman Auta ita kadai dad ya

aura tun aurens da yan watanin Allah yabata cikin cikin ikon Allah cikin

baizo da wani laulayiba, nan tayita kula cikin koda wata haihuwanta yazo

nan ranan nakuda ta kamata basu jima da zuwa asibiti ba ta haifo yan

biyunta kyawawa mace da na miji murna gun dad ba‟a magana nan suka

dawo gd, tun kafin suna na mijin ya rasu ya rage sai mace, mum tayi kuka

daga karshe ta hakura ranan suna yar taci sunan zainab zainab wata ta 4

ta kamu da rashin lby, asai bana tashiba basuyi dogon jinya ba Allah ya

karbi abusa, tun bayan rasuwansu hajiya bata sake ko bariba sai bayan

shekara 5 ta samu cikin Auta nan suka dau son duniya suka daura akan

cikin nan bayan wata tara ta santalo yarta kyakyawa nan taci sunan

Zainab, haka sukayita rai non xee harta girma. Tun da na dawo gd Alhaji

ya mai dani makaranta nan nacigaba da karatuna ina dawo inyita wasa da

Zee da futha, ko muyita karatu haka rayuwa tayita tafiya Su baba sani

basuda birin da yawuce suga na bar gun dad don ba zan manta ba akwai

randa suka min sharrin sata ranan nayi kuka kamar raina zai fota.

®WISDOM HAUSA WRITERS. Rash Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Duk wani

abun da zasu min na kanyi, hakuri in jure don ba dansu nake zama ba,

haka rayua tayi ta tafiya har na gama HND a gidan dad na karanta fanni

business, yayin da Zee Auta ta gama secondary school dinta ita da Sadiya

19 WHATSAPP 08105882006

Page 20: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT

WWW.AREWAFLEX.COM

da futha, ranan murna ba a magana don sai da dad ya shirya mana

kayatacen liyafa, bayan mun gama mun dawo zaman gida sai Auta da ke

zuwa islamiyya, ni kuma duk wa aiki ina yi duk da cewan sun hana ni yi

amma nakan sa kaina wani lokacin. samun shigan da nayi a gdn shi ya

daga wa maikatan gdn han kali har suke ga su da suka dade ba a musu

abunda ake min, tun daga ranan suka fara kule2 na hanyar da zan bar

gdn. Baba sani da kawu isiya burinsu yanzu shine tayaya dukiyar dad zai

dawo hannun su don kulum samun cigaba ya keyi, kuma ba abunda suka

tsana irin yawan sadaka da kyautata wa mutane, acewar su baisan zafin

dukiyar sa ba, sun sha zuwa su samesa gameda ya daina yawan rabar da

dukiyan sa, yaki, ya ce in dai akan wan nan ne kar su sake tun karansa,

tun daga lokacin suka fara kule2 na makircin kawar da Dad. Basu tashi

razana ba sai ran da dad yace musu zan fara aiki, a gurin kuma yanzu zai

bani manager a company nin, ko kuma duk wani shiga da fuce kudi

yazama ta hannu nane, ko wani kayan da za‟a saya duk zai dawo hannu

na, ran da dad ya sanar min bakaramin murna nayi ba har kuka nayi, asai

akwai irin su dad a duniya, asai bazan yi maraicin iyayeba, dad yayi ta

lalla shina,. Han kalin su baba sani ya tashi matuka, nan suka fara shawar

su jefa dad acikin ruwa nan baba isiya yace tayaya zamu jefasa, haka

sukayita shawar wari, har baba sani yace mufara masa baraza ya daura

mu a kan dukiyar sa, ko ya bamu in yaki sai muje gd mukashe shi da

iyalansa da dan koran da ya daura akan dukiyar, nan sukace gakan za‟ayi,

tun daga wan nan rana suka soma kiran dad suna masa bara zana, akan

dad ya basu dukiyar sa yaki, don har nima a sha yimin barazana akan na

bar gdn dad amma naki don da Allah na dogara nan da dad zai rasu ya

kiramu ya bani AMANA zee san nan yasanar mana ana masa baraza,

amma yaki fadan ko suwaye, bayan da ya fita ne na kirashi a waya na

tambayesa da farko ya ki fada min sai da na sanar masa cewa nima ana

min baraza na, na basa lbr kafin ya ban lbr komai yace da kar in sanar da

xee hankalinta zai ta shi, da daddare suka zo don kashe mu gaba daya

20 WHATSAPP 08105882006

Page 21: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

cikin ikon Allah ya kubutar da ni da Auta kuma a lokac in taga wayan da

suka kashe mata iyaye, dali2 da yasa yanzu na sanar mata kenan wannan

shine lbr mu, Malam da inna laure suka dago fiskansu cike da kwalla ga

tausayi auta ma kukan take ni kuma hawaye ne, wani na bin wani. Malam

yace Allah ya jikan iyayenku, san nan a duniyar nan har ana samun

marasa imani irin wayan nan mutane sun ci AMANA ga bata ZUMUNCI da

sukayi ba ko tausayi a ransu sai son duniya, kuyi hakuri da rashi, da sannu

Allah zai toni asirin su ya kuma saka muku, Allah ya jikan su muka amsa

da Ameen. Yan uwa amin afuwa na rashin jina kwana 2 waya tace ba

charged, kuma ban samu zama ba. Luv u all my fanz ®WISDOM HAUSA

WRITERS Rash Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Bayan sunyi sallah isha‟i suka dan yi

hira kasancewar lokacin damina hadiri ya hadu aka soma iska, dole yasa

suka shiga dakunan su don bacci, ruwa akayi sosai washe gari da safe

bayan sun karya ne, Malam yayi shirin zuwa gona nan Ammar yace zai bi

shi suka tafi tare, inna da Auta sukayi aikin gd. Haka rayuwan su ya

kasance acikin kauyen cikin kwanciyan hankali, yau kwanan su 10 kafar

Auta har ya warke, Ammar ma ciwonsa ya bushe har yayi bawu, nan

yasoma tunanin mafita don zamansu kauyen kaduna sam baiyiba, don

marasa imanin nan suna sanin yana cikin kauyen to zasu iya turowa a

kashesu baki daya, malam ya samu ya masa baya ni yana so su kara gaba

don in mutu nen nan suka samu lbr zasu iya turo wa a kashesu malam

yace hakane jiki ba kwari ya dau ko yan kudinsa da ya tara na kayan

gonan da ya sayar ya basu yace suyi guziri inna kam da taji zasu tafi har

da yar kukanta don sun shaku auta ma tayi hawaye, washe gari alhamis

suka fito da ga kauyen nan suka shiga motar zuwa rigiyar malam wani

kauye da ke jahar bauchi, a cikin motar suka zauna shiru b a mai magana

sai yan motan da suke hira duniya. Haka har suka iso wani kauye wai shi

na bardo, nan yaga ana sauka kawai sai yace bari su sauka gurin nan suka

sauka, koda suka sauka gefen rumfunan garin dake bakin hanya ne ya

sayo musu fura da nono roba biyu ya ba ma zee ta amsa, tafara sha

kenan sai ga hawaye, ammar na ganin haka yace Auta hakuri zakiyi shi

rayuwa haka take yau dadi gobe ba dadi mukasance cikin gode ma Allah,

21 WHATSAPP 08105882006

Page 22: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

sai ya kara wada yar mu cikinta yayi sanyi amma takasa shan nono, wai

ita ce yau a titi a kuma kasuwa take cin abu, rayuw kenan Allah ya jikan

su dad, ganin taki sha yasa Ammar yakasa sha shima, don baya kaunar

ganin zee cikin tashin han kali, nan2 sai yashiga damuwa. haka suka bar

gurin suka dawo gindin wata bishiya suka zauna, lokacin sallah yayi ya

nufi masallaci, yayi sallah dake a gefensu yake bayan ya idar ya dawo

auta tayi alwala ta shinfuda dan kwalin zanin da inna ta fata ta daura, tayi

sallah, haka har dare yayi koda aka watse gashi basu san kowa ba,

Ammar ya duba musu gurin wani mai shayi da benci a gun nan ya hada

ma auta kwaya biyu yace ta kwanta, haka ta kwanta idonta na zubar da

hawaye, tabbas tasan ammar ne kadai ya rike iyayenta da gsky, Allah ya

saka masa da dawai niyar da yakeyi da ita, Allah ya jikan iyayenta da nasa

Ameen, Ya Allah ka bani abunda zan saka ma Ammar da shi, kuka ne yazo

mata marar sauti haka tayi mai isarta daga baya tayi shiru, ammar ko

kasance wan benci biyu ne a gun mai shayi ba wanda zai kwanta yasa ya

dan zauna ya jingina da jikin falangen gurin shayi haka har bacci ya

daukesu. Cikin dare misalin karfe daya da rabi, cikin bacci Ammar ya rika

jin ihu daga nesa tun abun na nesa har ya matso kusa sai auta ma taji ta

tashi, ihun yayi yawa gashi gudu sukeyi sai a lokacin yaji ana cewa barawo

barawo, yace ma auta ta tsaya kar ta fito jikinta sai bari yakeyi nan ya fita

itakuma tana lekawa, aiko yana fitowa sai ga wani tutum da gudu yabi

bayan gurin shayi ya gudu, ana haka sai ga mutanen sun yi kansa suka

nan suka fara dukansa suna shine barawon, auta na gan in haka tafito da

gudu ta na ihu, wayyo Ammar dina ba barawo bane, wayyo dad kuzo ku

kuga halin da muke ciki zasu kashe shi kansu tayi gadan2 tana so ta kutsa,

da kyar ta samu tashiga dai2 wani ya kai masa duka da dorina kenan ya

sauka akan Auta nan tasaki wani razanen kara. ®WISDOM HAUSA

WRITERS Rash Kardam [6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Wani kara tasaki, sai a lokacin suka

kula da ita, take suka haskata da toci sai sukaga macece, wani daga

cikinsu yace mai ya kawo wan nan guri, sai da yace tsaya in ga barawo

nan tukun don wancan gajeren wando ne ajikinsa, yana haskawa ko ah…

ah.. wan nan ba barawon bane to ina yayi, sai dayan yace wan can na da

22 WHATSAPP 08105882006

Page 23: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

kirar gutun mutum, auta ko sai ihu take, ammar ko motsi ba yayi sana din

dukan da aka masa harda bora, wasu ice haka akayita kwana masa. A

kaduna kuwa sadiya Al‟amari abban ta ya daure mata kai don yasaka

dukiyar auta gaba sai ci sukeyi, a ko a jikinsu, wata ran kam ma intasoma

masa zancen auta ya hauta da fada kenan, haka yasa ta soma zargin wani

abu a tare da su, Wani yammacin asabar sun fito gidansu futha suna

tattaunawa akan batun auta da yanda zasu bi al‟amarin kenan sai suka

hango abban sady, tun daga nesa yasoma wurga mata wani kallon

tuhuma, ganin haka yasa tayi sallama ma futha tashiga gd, aiko kamar jira

yake yazo ya fara zazzaga mata bala‟i akan tafita harkan futha ko ya saba

mata, shi baya son kawancen su, ganin su tare ma baya so, sady tace kayi

hakuri abba ina tarayya da ita ba dan komai ba sai tun auta ta nan m una

tare mun kuma shaku, abban sady yace hungo nan uwaki da autan nace

uwaki da auta kar ki kara kira min sunan wayan nan banza mutanen, nan

take idon sady ya kawo hawaye ita kam bazata manta auta ba aminiyarta

jininta, anya baba na da imani kuwa ko tausayinsu babu a zuciyarshi ko ya

manta dukiyar iyayenta yake wada kansa shi, ya Allah kasanya mana

tausayi da imani a zukatan mu Ameen ranan tayi kuka haka ta yini

sukuku, sai yamma tayi shirin issalamiyya ta tafi ko da taje nan ta saida

wa malaman su akan sutayata adu‟ah ta kuma musu bayani ko mai ake

ciki, tun daga ranan ya zamana kulum a makaranta bayan an gama karatu

sai anyi ma auta da iyayenta adu‟ah. Futha kuwa kwana 2 taji sady shiru

nan tashirya ta shiga gdnsu aiko nan sukayi karo da abban sady, tun da ga

nesa yasoma hararanta, tana isowa kusa yace kee wajen wa kika zo cikin

ladabi tace baba kawar Auta ce nazo gun sadiya ne, yace maza ki juya kar

na kara ganin lafarki a gdn nan yata batayi kawance da ke ba don ban

yarda da kee ba. ran futha in yayi dubu ya baci haka ta juya gd jiki ba

kwari kuma tana tunani akan al‟amarin nan, anya ba hannu baban sady a

kisan su abban auta, to tabbas ko ma miye sai na binciko ko da hakan

yana nufin rasa raina ne ya Allah ka bayya na gsky. Muta ne da ke gun

duk suka soma watsewa ganin baya motsi gashi sun dakesa ba akan wani

laifi ba, gudun shiga Case, auta ko in banda kuka da ihu ba abinda take sai

kiran sunan Allah ga idonta har ya kubura yayi ja ga ammar shi da

23 WHATSAPP 08105882006

Page 24: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

matatce marabansu kadan ne, wayyo Allah na ka taimaka min ka min

agaji in ammar ya tafi bani da wanda zan kalla inji dadi, rayuwata zata

zama abar tausayi Allah kaine gata na ka tai make ni ammar dina ya tashi,

cikin kuka take jijiga Ammar ga hawaye ga majina duk sauka sukeyi,

Ammar dan Allah ka tashi kar ka barni ka manta Dad ya baka “AMANA

TA” ka tashi ka kula da “YAR AMANA” ka kuka take sosai mai ban tausayi

tana ta surutai amma shiri ganin haka yasa takara fasa wani kuka mai ban

tausayi wanda ni kaina Rasheedah ban san lokacin da na fara zubar da

hawaye ba, gsky Auta da Ammar kun ga jarabawar rayuwa ga wlh Allah

sarki auta abun tausayi, Allah yasa ammar dinki ya tashi Ameen.

Jumma‟at Mubarak 2 all my muslim sisters n brothers. ®WISDOM HAUSA

WRITERS Rash Kardam [7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Kuka take sosai ammar ko motsi

baiyi ba nan takara jin natsara su baba sani suka jefasu cikin irin wan nan

halin, wani bawan Allah ne mai tausayi ya dawo yace bai war Allah daga

ina kuke, cikin kuka tace ka taimaka min dan uwana ya t ashi shikadai ya

rage min an kashe iyayenmu, nan kukanta ya tsananta cikin tausaya wa

yace ki tsaya tai mako daya zan miki yanzu ga gidan mai gari can barin je

na kirashi da gudu ya tafi ko da yaje ya jima yana buga kofar kafin aka

bude, masa, mai gari ya fito suka gaisa nan yasa sai damasa cikin damuwa

mai gari ya dauko garensa ko da suka zo har lokacin ammar bai farfado

ba, hakan yasa suka daukesa zuwa asibitin garin nan aka bashi agajin

gaggawa, bayan sun dan masa treatment ne suka shin fidesa akan yar

gadon asibiti, auta ko in banda kuka ba abunda take, bayan ansa masa

ruwa mai gari ya musu sallama akan da safe zaizo duba su, auta kasa

bacci tayi ga haddiri ya hadu nan akara walkiya da sauri ta haye karamin

gadon duk tsoro ya ci kata baran data ga wajen asibitin jeji ne, nan ta kan

kame ammar sosai hawayen ta na sauka a akan kirjinshi cikin barci yaji an

kan kamesa, a han kali yasoma bude ido yaga duhu da kyar ya iya daga

hannunsa yaji auta ne nan kuma yayi kokarin mikewa kansa ne ya masa

wani nauyi ga sara masa da yakeyi, a hankali ya shafa kan yaji bandeji ne

an daure, sai a lokacin ya tuna mai ya faru hawaye ne yasoma zuba masa

shima tabbas yasan suna cikin wani yanayin da Allah ne kadai zai fiddasu.

24 WHATSAPP 08105882006

Page 25: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Auta jin alaman na motsa hannu yasa da sauri ta shafi fiskansa nan taji

hawaye a hankali ta daga hannun ta tasoma share masa hawaye tana

cewa kayi hakuri Allah zai saka mana kaji kuma Allah yana tare damu

yaga halin da muke ciki ba zai bar mu haka ba, nan ya karajin jikinsa ya

mutu ga auta da ta kwanta masa ajiki bai san lokacin da ya sauke ajiyar

zuciya ba, har azuciyansa yana son auta ko da aure zatayi ba iya bayar ta

ga wani ba don bai son wani yaci Amanar da dad ya basa ko in auta tace

bata sonsa to dole ya hakura don ba zai takura ta ba, gwanda ya shiga ko

wani irin hali ne da ya sata a damuwa. a hankali ya kara kan kameta a

jikinsa wanda sai da itama taji wani shock ya ziyarci jikinta ajiyar zuciya

tayi ahaka suka kwana yau kam bacci mai dadi tayi ajikin Ammar wanda

rabonta da ta yi tun iyayenta suna da rai, sai da asuba ta mike da ta fiti

kofar asibitin in da taga randar ruwa ta diba tayi alwala ta shin fida dan

kwalinta tayi sallah, bayan ta idar ne ta zo da ruwan ammar da kyar ya iya

tashi sabida jikinsa yayi tsami tana zuba masa ruwan yayi alwala yana

kwance yayi sallah don kansa ya masa nauyi. Sai da gari ya waye sosai

gurin karfe 9:00 mai gari yazo duba sa da yar kununsa a kwanon sha da

kosai nan suka gaisa bayan sun gaisa ya ke tambayan su mai ya kawo su

gari da har zasu kwana a kasuwa nan auta ta basa lbr ya tausaya musu

sosai, nan ya musu sallama akan darana zai zo dubasu auta haka take

kula da ammar dan kudin da malam ya basu shi suke yasan abun da ya

dan musu su ci, kwanan Ammar uku a asibiti aka sallamesa jikinsa ya

warke sai tabo, ko da suka fito a asibiti gdan mai gari ya nufa ya masa

godiya san nan yace yana so su kara gaba don yana son cikin birni inda zai

samu sana‟a yayi da karfinsa, nan mai gari ya ce yanzi kana fita sai garin

bauchi shine babban gari, nan yaji yana son garin don ya dade y ana jin lbr

garin bauchin yakubu ga Addini ka mutunta mutum ga iya karama baki,

ga masa waina sai wanda kazaba, nan yayi godiya mai gari ya rakasu suka

shiga motar bauchi. Rash Kardam [7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Mota su ka shiga, a

hankali suke tafiya, haka kurum ya tsinci kansa da farin ciki, tun a hanya

yaji yana son garin ya burge shi. Auta ma haka abun yake tana gefen

Ammar ta dan jingina kanta a kafadarsa, haka kurum take jin sanyi a

25 WHATSAPP 08105882006

Page 26: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

zuciyar ta, nan ta fara tuna irin rayuwan da sukayi abaya lokacin iyayenta

suna raye, ku ina zataje a mota suke tafiya mota mai AC ba hayaniya,

amma yau gata a motar kasuwa, Allah sarki yarinyan da taso cikin gata da

kulawa ya daya tilo yau gata a cikin gararin rayuwa Allah ya kawo masu

sauki Ameen. Karfe goma da minti sha uku, suka iso cikin garin bauchi,

driver ya sauke su a waje tashar mota na winti market, nan suka sauka,

kowa ya kama gabansa, Ammar ya riko hannun Auta suka bar gurin, titi

suka tsallaka suka zo ta gefen stadium akwai dan guri nan suka zauna,

kallo daya zakayi ka ga kamanin su auta yanda ya canza sunyi baki ga

rama da sukayi sosai. Sun dade a gurin sosai, amma sun rasa inda zasuyi

can yace bari yaje ya nimo musu abinci, tace to gefen gun masu sai da

jarida da gyaran mashin ya ga mai sai da shinkafa da wake nan ya saya

musu roba biyu da pure water kwaya 2 ya kawo musu, haka suka ci

sukayi godiya ga Allah ya mayar wa masu shinkafa ya karbi canji ya dawo,

haka suka zauna sai da aka kira sallah, nan ya sake saya m ata ruwa tayi

alwala shi kuma ya tafi masallacin da ke gefe yayi sallah, bayan ya dawo

suka zauna hira ya rinka mata yana bata dariya don ya debe mata kewa

sabida yaga damuwa a idonta sosai, haka suka yini har dare agun suka

kwanta. Da gari ya waye sallah yayi yace ta zauna a gun kartaje ko ina

zaije ne man abunyi ko da dako yasamu don su rinka samun abunda za

suci da in da zasu zauna, haka ko akayi ya shiga cikin kasuwar winti, haka

yayi yawo sosai amam shiru ba lbr aiki sai azahar ya dawo yaje ya sayo

musu shinkafa sukaci, bayan sunci tace Yaya na anyi nasara kuwa cikin

mutuwar jiki yace ina Allah baisa an dace ba, idonta yaciko da kwalla tana

shirin yin kuka ya girgiza mata kai alamar aa, yace ko kin manta Allah

yana tare da mu bazai barmu haka ba, kuma duk bakin da Allah ya tsaga

bazai hana shi abinci da zaici ba. haka suka sake kai dare nan suka sake

kwana. Washe gari ma haka yafita yayi yawo har ya gaji gashi yan kudinsa

sun soma karewa saura dari biyar, yau sai bayan la‟asar ya dawo dake ya

ba ma Auta naira dari don tasayi abunda zataci ko da yadawo yasamu

tana bacci akan yar fallen zanin da ta shimfida tausayinta ya kama shi,

Allah sarki auta yau itace tamkar wata tsintaciyar mage gwamma shima

namiji ne, idonsa ne ya ciko da kwalla a zuciyarsa yake adu ‟ah Allah ya

26 WHATSAPP 08105882006

Page 27: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

kawo musu dauki baisan hawaye yana sauka da ga idonsa ba saiji yayi

auta na share masa hawaye itama idonta yaciko da kwalla, tace Yaya na

sai dayaji sanyi har cikin ransa, mai yasa ka kuka ban son ganin hawayen

ka, in kai kayi hawaye wazai rarrashe ni, kaine mai sani farin ciki, Allah

gatana kaine gata na, yaya na waya taba ka karkasa kanka cikin damuwa

Allah zai kawo mana mafita yana tare damu kaji, kaman karamin yaro ya

daga mata kai, tace kayi min murmushi, ammar baisan lokacin daya

murmusa ba, itama murmushin tayi ta rike hannunsa tace Ya Allah kaja

kwanan yaya na kabani abunda zan saka masa dashi. ®WISDOM HAUSA

WRITER‟S Rash Kardam [7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA

CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Hancin ta ya lakace yace Ameen

amma kwanan mu gaba daya, haka suka zauna cikin farin ciki har dare

yayi suka kwanta. Da safe ammar ya sake fita nan ma ya barmata kayan

karin kumalo ya fita, nan yayi ta yawon niman aiki da kyar ya samu wani

shago zasuna debo kaya daga stored suna kaiwa cikin shago amma ba

kullum ba sai randa za a saka kaya a shago ko sun dawo daga sari, haka

ya dawo da murna yake sanarmata, nan ta tausaya masa tace Yaya na

zaka iya yin dako kuwa kai ya daga mata yace eh kan wata, in dai zamu

samu abunda zamuci Alhamdulilah. Washe gari haka suka tashi kudin su

ya kare sai naira hamsin shinkafa ya sayo ma auta ya zauna yasata a gaba

taci, tace aa sai dai su ci tare fir yaki don ba zai ishesu dukansu ba, auta

taki ci ganin haka yasa ya dau cokalin roba ya fara bata lbr abun dari ya

yana bata a baki tana ci har ta cinye , ta kalli kwanon tace kai yaya na

gashi kasa na cinye kai ya girgiza mata alamar kar ta damu, haka sukayi ta

hira har dare, Futha ce ta fito sanye cikin shiga ta alfarma ta shiga

motarta ta nufi makarantar da tafara zuwa, bayan sunyi lectures kenan

tafito tana zaune, kiran sady ne ya shigo bayan sun gaisa ta tambayeta

kwana biyu tace lfy nan suka taba hira ta hakuri gameda abunda babanta

ya mata nan sukayi sallama ta dau ko hanyan gd tun daga nesa ta hango

wata sabuwar mota honda ta hadu motar blue kalo daga gidan su Auta

tafito wanda yanzu su Sady ne acikin gdn, sai da tazo kofar gidansu ta

tsaya don ta karbi lab top dinta da tabada ya duba mata, bayan ta karba

ta fito taga wan nan Honda tatsaya dai2 ita nan aka zug e glass wacce ta

27 WHATSAPP 08105882006

Page 28: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

gani a motar bakara min mamki tayiba da ace itace a wannan motar,

pinky ce yar kanini baban Auta wato yar Baba Isiyaka, hy tace mata sai a

lokacin ta dawo daga duniyar tunani gaisawa sukayi ya kwana biyi tace

lfylau ya school tace Alhamdulilah, sun dayi hira kafin sukayi sallama,

futha ta tafi tana tsananin mamaki sosai da sosai pinky ce haka harda

mota lalle sun samu duniya tabbas dawata a kasa dole ma tabi didigi

haka taja motarta tashiga gida tan tunani kala2. Can cikin dare wani

hadari ya hadu ga iska daya taso sosai, Yaff yaff yaff ruwa da iska yasoma

zuba, kan kace me sai ga ruwa ya barke baka dan ba, nan Ammar suka

farka kafin sunimi matsuguni rua ya soma dukan su bakadan ba duk inda

zasu fake ankulle nan suka dun kule a gindin shiya ruwa nan dukansu

Auta ta kan kame ammar tana yar kuka ga ruwa sai dukar su yakeyi wani

tsawa aka sake sosai wanda yasa Auta kara rugume ammar har sai da yaji

tsikar jikinsa ya tashi yaso ya ture ta don yanda yasoma feelings, ga wani

murdawan da maranta keyi alamar period ga ruwa na dukan su gaka

ruwan ya kare akansu tass barin sanyi auta takeyi ga maranta na murda

mata gashi ba kayan canzawa haka suka tsuguna a tsugune har gari ya

waye jikinsu har ya bushe auta kam mara ke ciwo gada2 ga zazzabi na

neman mata mumunan kamu nan hawaye ya soma zuba don tabbas

period dinta ne gashi kudinsu ya kare ga pant daya ke jikinta kayan da

zata canza ma baba gashi kwananta 2 ba wanka sai yau da ruwa ya mata

duka Yasalam!!! Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli khairan min ha,

jikinta yayi zafi sai barin dari takeyi Ammar ko da ya taba jikinta nan take

ya rikice ya shiga da muwa gashi kudinsu ya kare ga auta jikinta yayi zafin

Innalilahi wa inna ilaihi raji‟un yake furtawa a bakinsa. ®WISDOM HAUSA

WRITER Rash Kardam [7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Jikin auta yayi zafi sosai ga ciwon

mara, ammar duk ya rude yarasa me ke masa dadi ga kudinsu ya kare

gefen wani shagon daya ga ba a budewa yaje ya kwantarta lokacin gari

yayi haske sosai ya cire yar rigansa na janfa ya luluba mata nan yace auta

kiyi hakuri barin fita neman kudi ko zan samu sai in saya miki magani kai

ta daga masa hannu sa ta riko cikin muryan marasa lfy tace Yaya na Allah

ya ka fita sa‟a ya amsa da amin, ya fita Shagon dako yaje yayi sa‟a an

28 WHATSAPP 08105882006

Page 29: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

kawo kaya nan ya yasoma aikin kwasan kaya tun bakwai yagara sai karfe

shadaya ya gama nan aka bashi kudin aiki 200 dake kayan ba masu nauyi

bane shiyasa, hamdalla yayi yana shirin barin layin masu kayan zai wuce

yaji wasu suna neman mai zubar da shara nan yayi aikin ya gyara musu

gurin tass suka bashi 50 daya layin ma sun kitashi nan ya fara musu aiki

aka soma kiran sallah ya bari da sauri ya ce zaije ya dawo yana fita

chemist yaje yasayo maganin mura dana zazzabi yabi yasayo musu

shinkafa auta harda tea irin na masu yawo suna hadawa yasa mata da

murna ya kama hanya zuwa gunta. Futha bayan ta huta washe gari tacr

ma Sady tana so su hadu akwai abunda takeson sani, nan sady tace zasu

acikin Kad poly haka ko akayi da yamma suka hadu bayan su n gaisa futha

take bata lbr abunda ta gani Sady tace nima abun ya daure min kai don

pinky bakara min busha take ba kuma Abba na nima yace wai ya sai min

mota ba a shigo da ita bace ni kaina futha yanda suke bushasha da

dukiyar su Auta abun har na razana ni kuma har yanzu sunki yarda ayi

binciken akan wayanda sukayi kisan nan da kuma inda Auta take, futha

tace kar kidamu sannu a hankali komai zai zama tarihi Allah ya toni asirin

duk wannda keda hannu a wannan al‟amarin Sady tace Ameen nan suka

yi hira gameda karatu har sai magrib suka rabu. Baba sani ganin Sady da

futha suna neman dinkrwa yasa ya baza mata kan tsaro duk inda sady

tayi ana biye da ita don kar futha ta gano sirrinsu don bai yarda da ita da

mahaifinta ba suna masa shigan sauri akan al‟amarin, subaba isiya yanzu

abun nema ya samu hankalinsa kwance ke cin kudin da bana saba har in

anzo neman taimako gunsa yana ikirarin sunsan wahalar dayayi yasamu

dukiyar su asama kawai suka gansa da kudi, kutaya ni ji wai har yana

cewa sun san wahalar dayayi, baba isiya har wani yar tumbi yasaka yayi

fresh ko mai ya dai2 har ya manta da wani alhaji Al -hassan. A bauchi

kuwa Ammar da murnar sa ya nufo gun Zee Auta ya musu samuwa don

shi ko ta kansa bayayi yafiso yaga ita taci kafin sai yaci, yazo tsallaka titi

har ya kusa tsallakawa sai ga wani mai mashi ya yanko aguje ji kake kiiiii

mai mashin ya shiga da Ammar da sam idonsa ya rufe baya ganin hanya.

Yan gurin nan suka dau salati suna tafa hannu wasu suka yanko da gudu

suka zo ba da taimakon gaggawa Allah sarki kowa da irin jarabawar da

29 WHATSAPP 08105882006

Page 30: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Allah ke masa a rayuwa kamar yanda Ammar da Zee suka shiga haka

wasu ke cikinta kowa da kalar nasa ya Allah ka jarrabe mu dai2 da karfin

imanin.mu Ya Allah kabamu Abin da zamu iya Ameen Ya Allah. ®WISDOM

HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Kiiiii kake ji karar

mashin ta tashi sama da ammar nan mutanen gurin duka dau salati, wasu

da gudu sukayi gurin, abinci kam duk ya zube, nan mutane sukayi kansa

cikin ikon Allah bai ji ciwo ba sai dai ya dan buge kafarsa gefen hanya aka

maidashi mutane sai sannu suke masa Ammar na dawo hayya cinsa sai ya

hango robar abinci ta fashe maganin kam bai san ida ya yarshi ba, nan

take wasu zafafan hawaye suka soma gangaro masa a zuciyarsa yana

gode ma Allah daya sa yana da sauran rai in da Allah yaso sai kafarsa ta

cire ko hannu yana da kyau a kowani hali ka tsinci kanka to ka gode ma

Allah sai ya kara maka, cikin ikon Allah mai mashin ne ma ya dan kurkurje

nan ya ba ma ammar hakuri don yanzu fitowarsa bai da ko sisi ajikinsa

Ammar yace ba komai haka ya mike ya na din gisawa ya sake zuwa

chemist ya sayo paracetamol da da maganin mura na ishirin ya sayo ma

auta shinkafa talatin ba ko ruwa nan ya laluba aljuhunsa ya ga biyar

hamdala yayi ya sai mata pure water biyar da sauri yana din gishi ya nufi

gunta. yasamu duk ta dawo wani iri dagata yayi yana mata sannu abinci

ya fara bata da kyar ta iya ci kafin tasha magani ya maida ta ya kwantar

nan yaje yayi alwala yayi sallah bayan ya idar yayi nafila ya na gaya ma

Allah kukansa kafin ya dawo gurin auta ga yunwa tasoma damunsa sai da

yaga bacci ya dan dauketa kafin ya sake komawa cikin kasuwa ya yi

sharan yayi sa‟ah mai shagon mutumin kirki ne ya basa dari buyu nan ya

bashi sauran abinci ammar yayi godia yaci kafin ya sake suwa wani gu ya

musu aiki nan ya.samo dari uku nufo hanya. Tun daga nesa ya hango auta

rike da cikinta tana juyi da sauri ya karasa gunta,nan yasoma mata sannu

yariketa kuka tasoma masa duk ya rude ya tambayeta mai ke da munta

tace cikinta ganin yanda take juyi yasa ya dauketa da sauri ya nufi titi nan

rake aka zuna musu ido dake haka ya nufi chemist da ita nan mai chemist

ya soma dubata aiko yace Malam period dinta ne zaizo nan ammar ya

zare ido yaya zaiyi ba pant ba gun wanka mai chemist ya bata magani tun

30 WHATSAPP 08105882006

Page 31: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

agun tasha ya dan kwantar ta akan benci sun dan dade don ciwon ya dan

ragu sai rashin karfi ajiki nan ya cemasa kudin magani 200 haka ta bashi

nan suka mike zasu tafi kenan yaga shini ya bata gun da ta zauna nan ta

zare ido yau yaga ta kansa ya zaiyi kenan Yasalam Auta ko tsaban kunya

kasa daga idonta tayi sai hawaye nan ta fara Allah ya isa masu baba sani

duk sune ummul aba isin sata cikin wan nan hali. ®WISDOM HAUSA

WRITERS Rash Kardam [7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Ammar gaba daya ya rasa mai ma

zaiyi ne sun dan dade agun mai chemist daya ga basu tafi ba ya lura da

matsala dake ustaz ne yasha Sunnah ya koshi cikin kulawa yace malam lfy

dai ko ammar ya dago idonsa da ya cika da kwalla ya ma r asa mai zai ce,

mai chemist yace ya kamata ka kaita gd don tayi wanka ta huta ammar

cikin muryan sa na rawa kamar zaiyi kuka yace mu baki ne a garin nan

bamu da kowa cikin tausayawa yace ayya sai a lokacin ya lura da yanda

jikin auta ya baci nan ya ce masu ammar zan muku taimako daya ga gd na

banisa kazo muje gun matana ta taimaka mata da kaya ta gyara jikinta

ammar yaji dadi yacd ba matsala nan ya riko hannun auta suka bi mutu

min nan gd sa na bayan stadium plat ne ciki da falo sai stored sai kitchen

nan ammar ya tsaya daga waje shikuma sukayi sallama suka shiga da auta

nan wata mata baka mai dan kyan jiki gata da sakin fuska ta fito tana

musu sannu dazuwa cikin harshen fullanci ya mata bayani nan naga

fuskan Rahmat ya bayya na tausayi tace yar uwa shigo da ke bayinta na

falon ne nan ta hada mata ruwan wanka ta kaita bayin shiko mai chemist

ya kowa waje gun ammar suka dan fara hira. Rahmat ta ciro mata sabin

pant guda 4 da Alway ko amfani da shi batayi ba ta dauko mata riga da

siket daya da dogon riga dake da ka dan zata fi auta ki ba nan ta samata a

wata yar jakan biki mai zip da hijab daya da sabulun wanka sinki da na

wanki biyu nan ta saka mata riga da siket na eglish wears wanda tasa da

hijab mai hannu blue yadin plan tuyobo bayan auta ta gama wanka nan

tabata pant tasa ta bata mai da powder tasha da lip stick kai kar kuso

kuga auta nan ta yi kyau abunka da farar mace ga kyau azuciyar rahmat

tana yaba kyau irin na auta abinci tabata nan taci sosai ta bata zobo

yasha hadi kafin ta dauko jakan ta bata lokacin har ta dauraye mata

31 WHATSAPP 08105882006

Page 32: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

kayanta sunsha ta nuke tasa mata a hakar tace ki duba waje kice musu

kin gama nan auta ta leka tun da tafito ammar ke kallonta sai murmushi

yakeyi ga idonsa ya ciko da kwalla rabonsa da yaga auta fess haka tun

suna gun su inna laure a kauye yau har yar kyau tayi, auta tazo da sauri

tasa hannusa ta share masa kwalla tace yaya na kabar kuka nima zaka

sani kuka murmushi yayi yace babyn dad yau kinyi kyau sosai tace ta

gode duk abunda sukeyi mai chemist na ganinsu duk sun bashi tausayi

nan ta sai dama su sakon rahmat mai chemist yashiga gd ya fito masu

abinci sai da su kaci kafin Ammar ya masa godiya auta tafito suka kara

gaba. Rayuwa kenan * * * * * * Sady abun duniya duk ya isheta yanzu

bata isa tafita ba babanta zai dameta gashi yace mat ukar ta hadu da

putha sai ya yanka ta kuma motar da zai bata ma ya fasa duk ita bai da

meta ba sai sauyawan babanta anya yana da gsky yake haka yazama dole

insan sirrin boye tana cikin wan nan tunanin pinky tazo cikin masu

matsatsun kaya da kyar ta ke motsi cab su pinky an samu duniya yanda

akeso rawan kai ya karu bare ga mota a hanu….lol… Hira sosai sukeyi

anan sady take lbr ta ma pinky sauyin iyayensu pinky kafada tada ga

alamar ko in kula cikin isa tace ni ba damuwata bane tunda zanci mai

kyau insha mai kyau bani da matsala ga motar da zan shiga ko ina ba

sa‟ar dazata min raini kin ga ni ba damuwata bace kawai ke ma ki share

kizo ayi harka dake sis sady tace ni kyale kyale baya gabana gasky nakeso

tafito kuma zanyi iya kokarina pinky tace ae saikiyi ta ka i nan tafice

tashiga motar ta tabar gdn. Almarin futha kuwa jaratu tasa a gaba don ta

cimma burinta shiyasa ita ko saurayi bata kulawa karatu takeyi ga yawan

adu‟a Allah ya bayya na Auta ya karesu a duk halin da suke. Baba sani ko

yanzu an waye daga zuwa wan na hotel din sai gdn wacce bazauran shida

baba isiyaka holrwar su suke acewarsu Allah ya basu kudi dole suyi

abunda ransu keso, Allah ta kyauta ya Allah kar kabamu kudin da baza

mu kasheshi ta hanyar halal ba ameen. * * * * * Auta dun yitafiya kadan

donsu koma inda suke zaune bayan sun isa gun ammar yace zai sake

komawa kasuwa ko zai sami aiki nan auta ta bata rai tace ka huta ai tau

mun samu abunda zamuci kuma gobe ba zamu rasa ba don duk bakin da

Allah ya tsaga ba zai hana shi abinci ba nan sukayita h irasu gwanin

32 WHATSAPP 08105882006

Page 33: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

burgewa daga gani yau suna farinciki ammar yace to kimin afuwa nima

naje cikin kasuwa a kwai bayan gidan wanka da akeyi na kudi nima in

samu nayi wanka auta tace sai ka dawo Allah ya kare nan ya mike yaje ya

biya naira 20 yayi wanka ya fito ya dawo gun autarsa suka cigaba da

hiransu. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:38PM, 9/20/2016]

Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Haka

suka yi ta hira kulum ammar sai yaje dako ganin ba zai fiddasu ba ya nimi

gurin mai sai da kayan fruits da kayan miya suka fara sayarwa yazana

yaro agun nan ya na dan samu har mutu min ya kaisa gidansa da ke

bayan winti market daki biyi ne daya ciki da falo shida matarsa sai daki

daya karami ba ko flasta su ammar ke ciki kulum matarsa sai tasa auta

aikigata da kazanta auta bata iya gani sai ta gyara gurin wanki yaranta

tace sai tayi tun auta bata iya ba harta saba ko kadan bata fada ma

ammar ba don zai iya cewa su bar gidan ita kuma bata so suyita yawo a

titi wataran tayi kuka ta share hawayenta haka ta yita hakuri gashi abinci

dan kadan take bata kamar na dan yaro karami sai dare ammar ya

somata na ma da madara haka sukayita rayuwa kwanaki sun wa watanni

sun tafi har sun kai shekara a bauchi ba abunda ya canza sai baki da

sukayi da ramakam akwaisa duk da ammar na iya kokarinsa akan auta

duk abun da yasan zai mata kyau sai ya sai mata har yasata a wata

islamiya dake bayan unguwan tana zuwa, shiko riga mai kyau bai damu

da kansa ba wataran har mita take masa kayansa kala uku rak itako ya

cikata da kayan ado duk iya samu kudi ma ita yake kashewa hakan yasa

sa‟dat shiga tashin hankali don mijinta baya kashe mata kudi haka gashi

yaron hannunsa yana hidima wa kanwarsa nan take lbr wa makwabciyar

ta tace ke sa‟adat bazaki ganeba ne haka kurum zai na kashe mata kudi

batare da yana latsata ba daki daya fa suke kwana in baki shawara yau ki

fito ki lekasi kigani nan suka tafa sukayi shewa hakao akayi daddare ta

fito cikin rashin sa a taga ammar a waje yake kwana auta tana ciki sai

datayi haka har sau uku awajr take ganinsa sai randa akayi ruwa shine

taga ya kwana a daki ko da taleka taga shi yana bakin kofa auta na

karshen daki ba haka taso ba amma tsabagen makirci irin nata nan tafara

habaici ma auta akan ammar na aikata masha‟a da ita ranan tayi kuka

33 WHATSAPP 08105882006

Page 34: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

amma ta danne bata fada ma ammar ba don tasan yana da zuciya sosai

haka sukayita rayiwa abunu tausayi. Abangaren ammar kuwa kasuna

tafiya dai2 har yayi customer a kwai wata hajiya datake yawan sayan

kayan salad da fruit agunsa da vegetables har sun saba wataran kam

yarta take turowa tasaya agunsa hakan dai yaci gaba da dana‟arsa, auta

ko sai rama take kulum in yasata a gaba yana tambayanta tace bakomai

haka zai gaji ya kyaleta. * * * * * Zaune yake a gaban kayan fruits wata

bakar HONDA CRV TA cike da nuna isa da gadara take taku tun daga nesa

mutane ke kallonta sabida ta tafi dasu ga ta da kyau tafiya take kamar

bazata taka kasa ba kai daga ka ganta kasan naira ya zauna ma iyayenta

da fatarta sannu a hankali ta tsaya tana kallon yar fruits don ita bataga

wanda mum tace tazo gunsa ba har taxo zata juya ta hango wani dogon

saurayi fari mai kyau tamkar sharukan kalo daya za kamasa ya tafi da

tunanin mace don daga ka gansa kasan baragon namiji bane kuma mijin

nuna ma sa‟a ne kasa kyafta idonta tayi akansa shiko bai ma san anayi ba

wai kunu a wani gida, ko tan tama babu shine Ammar din da mum take

sayan kaya a gunsa, woow amma guy din ya hadu matsalar daya ne

rashin naira sai da taji wani mai saida fruit na gefen ammar yana cewa

hajiya kaya za a baki kafin ta dawo tunaninta a gada ran ce ta isa gun

ammar tace aslm ya kk tambaya nake wai wani shi ammar fiska ba yabo

ba fallasa yace eh nine ammar din lfy cikin isa tana satan kallonsa tace

hajiya Maryam Alkali ne ta aiko ni wacce take sayan kaya a gunka yace ok

ina jinki nan tace wai ka hada mata kaya kamar yanda take saya nan

Ammar ya hada mata kaya masu kyau ta bude jaka ta dauko kudi ta basa

tsabagen kallon da take masa ta yarda posd din ta garin mayar wa jaka

bata sani ba sai da ta bar gurin zuciyarta cike da tunani ammar har ta

tada motarta ammar yaga poss ya bita amma ina tayi nisa nan ya budr sai

yaga ID Card dinta da dunanta Munayshat Alkali nan yaga complement

card dinta da address dinta da sauri ya tsari mai mashin ya bi bayanta. 1

To masu karatu danso musan wacece Munayshat? Kuma wacece Hajiya

Maryam Alkali? 2 Shin munayshat son Ammar takeyi zai amsa kuwa to ya

rayuwan auta zai kasance Kubiyo Yar gidan JARAWA don jin yanda zata

kaya taku a kulum mai kaunarku Yar Mutanen Kardam. ®WISDOM HAUSA

34 WHATSAPP 08105882006

Page 35: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

WRITERS Rash Kardam [7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Ganin tayi nisa yasa ya bi bayanta da

gudu sukeyi da mai mashin amma ta musu nisa sai da sukaje G R A

adjacent da government house naga naga sun nufi wani katon kwalta ne

a shimfede kafin suka iso kofar wani hadadden gd harda security a kofar

ginan tun daga kwanar shiga gidan zaka ga arubuta Hajiya Maryam Alkali

house, da manyan zane, nan ya sallami mai mashin ya basa N100 kudin

mashi mai gadi suna ganinsa suka tashi nam sukace wajen wa yazo yace

gurin wacce tashiga da mota mai gadi yace ka bar gurin nan bazaka shiga

ba nan suka fara iskanci ma ammar ransa har ya baci ya juya zai tafi sai

daya mai gadin yazo ya tambayesa nan yace wacce ta wuce da mota

yanzu baka mai gadi yace ai gidan nan masu tuka mota suna da yawa nan

ya sake duba sunan yace Munayshat ok lfy dai ko yace lfy wa za a ce mata

nan yace ace Ammar mai kayan fruits nan security ya shiga nan yayi karo

da Aunty Mamu a falo ga Kausar a gefenta nan yace Aunty wani ne yazo

gun munayshart wai Ammar mai sayarda fruit nan hajiya maryam ta

fadada murmushinta ayya ammar lfy daiko yace eh wai abu yakawo ta

nan aunty mamu tace kaje ka shigo dashi, kausar mikewa tayi ta nufi

kitchen don dauko mult mai sanyi tasha, Bayan ya koma ya shigo da

ammar gasky gdn ya tsaru a kwai naira a gdn sosai don ya hadu iya

haduwa da sallama suka shiga cikin falon da yasha blues da yellow da

bakin labule ga kujeru luntsuma luntsuma suma colours din blue yasha

gyara ga kamshin da yake tashi ya duka ya gaida ta nan yace shai data

mata yarta tazo sayan kaya gashi ta yar da poss dinta nan tayi godiya ta

karba hauwa mai aiki ta kira tace ta kawo masa abinci yace ya gode hajiya

ta bata rai ammar ae mun zama daya ka dauken tamkar uwa a gunka

cikin jin dadi yayi godia hauwa ta kawo masa zobo daman shi ma aboci

zobo ne ya sha kayan hadi nan ya dauka ya sha gashi da sanyi nan ya

wani lumshe ido alamar jin dadi, Kausar ta fito rike da malt a hannunta

tun da ta nufo falo ta hangi wani hadadden saurayi ajin karshe ga kyau sai

da ta furta woow a zuciyarta nan take taji ya tafi da ita amma jin kai ta

danne ta shigo da sallamarta dake ita tana da hankali sosai ta gado halin

Aunty Mamu ne gefen mum dinta ta zauna cikin isa tace masa sannu da

35 WHATSAPP 08105882006

Page 36: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

zuwa yauwa yace a takaice dai2 nan munayshart ta shi go cikin wasu

matsatsun kaya riga da wando na English wears tayi kyau sosai don suna

da kyau ba laifi sai dai matsalar rashin gashi don sai da ta hada dana doki

tun da taga ammar tashiga wani yauki tana karairaya wanda shi bai san

tanayi ba ma nan Mamu ta bata poss dinta nan tace la ban lura ba ko da

ta bude taga kudinta ba a tabasu ba 80k ne a ciki don harda zonen gwal

dinta da yakai 60k aciki kirar dubai sai daukar ido ya keyi nan tace lah

mum gsky na da AMANA kiga ga kudi kusan 80k ga zobe na nagode duk

da nasan koda bata sukayi banda wasu matsala amma gsky da kanuna

naji dadi nan ya mike da nufin tafiya cikin sanyin murya yace hajiya zan

tafi tace angode kausar kam kasa motsi tayi sabida zakin muryansa amma

dake ita tana da kamun kai ga jan aji shiyasa t ake buyewa har ya kai kofa

Aunty Mamu tace Ammar in bazaka damu ba ina son zan tambayeka cikin

ladabi yasoma takowa ya dawo in da ya zauna ya sake zama kansa a kasa

ammar dan Allah ina son kafadan gsky waye kai daga ina kake don daga

alamar baka dade da fara sayar da fruit ba don na dade ina zuwa gun

bana ganinka san nan yanayinka baiyi kama da wahala ba a kwai wani

boyayen sirri atare da kai cikin nutsuwa ya daga fuskansa nan suka hada

ido da munaysharr da ke wurga masa shu‟umin kallo Kausat ma kallonsa

takeyi ajiyar zuciya yayi kafin ya sake sukiyar da kansa cikin nutsuwa ya

fara magana. Happy Jumma‟at Mubarak2 All My Muslim Sisters n

Brothers ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:39PM, 9/20/2016]

Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Cikin

nutsuwa ya fara magana ni Sunana Ammar Sa‟ad Saraki iyayena asalin

yan mai duguri ne nan ya basu lbr shi dana Auta ko da ya gama yana dago

kai yaga Hajiya Mamu harda hawayenta Kausar ko kuka take mara sauti

don tana da tausayi lokaci daya taji tana son auta ta tausaya mu bare

Ammar da shi ya ke mai rike AMANA munayshart kam ko a jikinta ita dai

Ammar take so nan taji wani kishi auta ma takeji sabida kulawar da yake

nuna mata, hajiya mamu ne ta katse musu tunaninsu ta hanyan cewa

Ammar lalle kun ga jarabawar rayuwa Allah ya jikan iyayenku san nan ina

son in bazaka damu ba zaka dawo gdn nan kana mana aiki sai ina baka ko

da 20k nasan a wata sallaman da mai kaya yake maka bazai wuce haka ba

36 WHATSAPP 08105882006

Page 37: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

san nan zan rikeku tamkar yayan dana haifa a cikina haka kanwarka za mu

bata kulawa godia yayi sosai kafin tace yanzu ya tashi yaje ya sallami mai

kaya daga nan su hado kayan su taho dashi ammar tsaban murna kasa

magana yayi sai hawayen farin cikin gdy yayi sosai kafin ya mike ya fita

yana yam sharan kwalla Kausar duk ya cikata da tausayi munayshart

kuma murna takeyi zata samu damar wayar dashi daga nan sufara

soyayya haka ta mike ta nufi dakinta kausar ko kitchen tanufa don taya

hauwa mai aiki girki don ita duk mulkin ta da jinkanta bai hanata aikin gd

sai dai bata son raini gsky wan nan kena. * * * * * * * Ammar da murna

sa ya koma cikin kasuwa nan yayi bayani wa mai fruit ta wani waje yana

murna ta wani waje yana bakin ciki don zuwan Ammar bakara min alkairi

ya samu ba ga customers da ya samu ga kasuwa ta bun kasa sai da y a

dauki 5k ya basa kafin ya hada masa kayan fruit nan sukayi sallama ya

nufi gd da farin cikinsa nan ya shigo da sallama, auta na daki ta fito ta

amsa da murna ta amshi kayan da ke hannu sa suka shiga daki kai in ka

gansu sai sun burge ka ka dauka Mata da miji ne nan matar mai fruit ne

ta fito da yar kujeranta don taji mai yake wakana tayi gulma nan taji

shewar auta da sauri tafara dogon wuya don taji meye amma hakan bai

yuwaba sai ta mike taje ta tagar dakin tasa kunnen ta dai2 lokacin tace

barin hada kayasai mu tafi ko mai ta tuna sai tace tsaya nan tafito da

sauri abun da ta gani ne yasa ta turus don matar mai fruit ta gani ta

window ita ala dole sai taji mai suke cewa sa‟dat na ganin auta ta ganta

jikinta ya dau rawa ta fara in ina dam….. Kwaro….na…ga… Auta tayi

murmushi tace dama sallama zan miki don mun samu wani gun nan zamu

koma da zama cikin zare ido da dafe kirji sa adat tace kenan kina nufin

gdn nan zaku bari kafin tabada amsa sukaji sallama mai gdn ne da wata

matashiyar yarin ya wacce bazata wuce21 yrs ba bakace kyakyawa ba

laifi daga ka ganta tasamu karatun boko da gogewa kalon sama da kasa

ta somayi ma auta ko ba a fada mata ba tasan wannane auta doguwar

rigane ajikinta baya da kauri sosai tayi rolling sai key din motarta dake

hannunta nan takegaban auta ya buga, Cikin isa take magana ina Ammar

din kice munayshart ne tazo tafiya dashi in ji mum auta jiki ba kwari ta

juya zuwa dakin ta kira ammar da ke nike kaya duk sunyi cirko2 a waje ya

37 WHATSAPP 08105882006

Page 38: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

fito yana ganin ta ya dan sake fuska bayabo ba fallasa ci kin in ina tace

mum ne tace inzo in taho daku murmushi yayi wanda ya bayyana kyansa

yace ba matsala mun shirya nan auta da hijab dinta ki rataye a kofa ta

tsaya kamar gunki tana kallon ikon Allah ammar hanin tayi kasake yasa ya

ajiye jakarsu yaje kofa ya dauko hijab dinta ya sanya mata nan take fiskan

munayshat yaso ma canzawa don tasan sai tayi da gsky akan auta nan

tukun yana samata ya riko hannuta daya hannu ya dau jakarsu duka fito

nan ya ga motarta ta dazu ne nan ya bude baya zasu shiga tace no

ammar ka dawo gaba ganin irin wan nan abunda munayshat keyi yasa

auta azuciyarta magana wannan ko wacece haka tasan auta da ammar ba

mai rabasu sai Allah ko ina tare muke ayya tasan ni YAR AMANA SA CE

kuwa amma barin fara gwada mata nawa salon cikin shagwaba da

bubbuga kafa na zo gun ammar na riko hannun ammar wanda har jikinsu

yana gogan juna nan ta kwantar da kai tasoma masa magana cikin

shagwaba Yaya na ni ni ni ni ni ni. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash

Kardam [7:39PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Ya ni ni ni mu zauna a baya kar ka barni

ni daya wani gululun bakin ciki ne ya tokari munay badan taso ba ta hada

fusaka tashi mazauni driver ta daura belt ta fisgi motar da karfi sunyi

tafiya mai nisa kafin suka iso kofar wani katun ka tafaren gd dake auta

tasaba da naira bata wani razana ba hakan suka kutsa kai gd sai da sukayi

packing sannan suka fito munay a gaba tana wani karai raya har suka

shiga falo nan ba kowa karararwa ta danna sai ga hajiya mamu na

saukowa daga matakalar benin gdn cikin shiga ta alfarma fuskarta dauke

da fara‟a tana ganin su tayi gun gun auta tana fadin Zainab sannu da

suwa hannu ta tariko ta zaunar da ita kusa da ita nan ta kira hauwa tazo

ta kai auta dakin da ke kusa da na munay bayan tayi wanka kinzo kici

abinci haka akayi hauwa ta kaita daki ammar kuwa a dakin dake wajen

amma kofa biyu ne daya zaja shiga ta falon gd san nan akwai kofar da ke

kallon harabar gd nan aka masa masauki, auta wanka tayi sosai ta wanke

ko ina na jikinta ga sabulu mai kamshi bayan ta gama tazo ta shafa mai

san nan tasa dogon riganta da dan kara min hijab tagama kenan hauwa

tazo tace suje dining taci abinci nan suka fita hajiya mamu ne kadai a

38 WHATSAPP 08105882006

Page 39: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

falon duk dari2 takeyi don bata saba da suba amma haka kurum take jin

hajiya mamu a jikinta don ta mata tarban mutunci wacce ta dauko su ne

kwai ke mata kalon wulakanci kuma taga alaman zasu shafa da ita sai dai

auta ita sam bata iya hayaniya ba haka ta rinka cin abinci dari2 ana haka

sai ga kausar tashigo da sallamarta da alaman daga wani gu take washh

tace sannu mum na dawo hajiya mami tace sannu da dawuwa mikewa

tayi ta haura sama sam bata lura da auta tazo ba dakin mum dinsu ta

nufa ta ajiye mata aika kafin ta nufi dakinta wanka tayi ta hau online tana

duba sakon da ka turo mata a whatsapp da viber da fb nan ta yi ta reply.

auta bayan ta gama hauwa tazo ta tattara kwananukan auta binta

kitchen tayi tare sukayi wanke2 bayan sun gama ne suka dawo falo

lokacin munay ta fito cikin wash matsatsun kaya sai wani kwarkwasa

takeyi suna hada ido da auta ta sakar mata harraa wanda saida auta

jikinta yayi sanyi nan ta sun kuyar da kanta daki ta koma, Munay tace

hahaha yariya zaki gane kurenki don sai kin gwammace kida da karatu

ammar ma yaci sa an ya min shiyasa zan ragar nasa anma yanda yake

sonki ba zan lamunci ganin yana nuna kulawa ga wata ba azuciyarta take

magana. Ammar ko dakin da aka basa ba laifi ya hadu sosai nan yasa tan

kayansa wanka tayi da man akoshe yake kwanciya yayi yana tuna

rayuwansa na baya ga wani irin son auta da yake ji ama yana tunanin

hanyan da zai fada mata in ya tuna yanda komai nata yake sai yayi

hamdala don tabbas yasan ba zai iya bada auren auta ma wani ba har sai

in yaga yashi sonta da kaunart zai iya hakura san nan kuma wanda zai

taya shi rikon AMANA TA haka yayi ta tunani kala2 sai da aka kira

magriba ya mike ya nufi masallaci don gabatar da sallah bai dawo ba sai

da yayi isha‟i nan yasamu an kawo masa abinci zama yayi yaci kafin yayi

godiya ga Allah da ya kawo musu sauyi a rayuwansu. Hajiya mamu ne ta

fito falon nan ta tarar da kusar tana jiran su fito sai da tasa hauwa ta kira

wanda yanzu ake kira da Zee nan ta fito kenan sai ga munayshart sai wani

cika takeyi tana batsewa ita a dole yar gidan ganin auta ta fito yasa tazo

da sauri ta mangajeta nan ta tafi luuuu… ®WISDOM HAUSA WRITER Rash

Kardam [7:39PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Luuu ta tafi zata fadi cikin ikon Allah ta

39 WHATSAPP 08105882006

Page 40: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

rike karfe matakalan benin bata kai kasa ba duk jikinta sai bari yakeyi

amma ta gode ma Allah da ya kareta yasa bata fad i ba kasancewan ba

wanda ya gansu wani kalon warning munayshat ta mata kafin ta wuce ta

sauka ta karasa table auta jikinta yayi sanyi sosai nan taji wani sabon

hawaye yana shirin zubo mata kamar zata fasa sauka sai ta tuna hajiya ce

ta kirata in bataje ba ta kyauta ba a hankali ta sauka ta hango su a dinin

cikin nutsuwa ta karasa sai da ta gaida hajiya mamu sannan kausar da

fara a ta amsa munayshat kam wani sako ta amsa mata ta gefen ido nan

ta sunkuyar da kai hajiya mamu tace yata kisaki jikinki ki dauka k ina gd ne

ki daukeni tamkar mum dinki ga aunty ku kausar nan sai wan nan sis dinki

Munayashat muna hada ido ta sakar min harara to na amsa ma hajiya na

mata godiya nan mukaci abinci bayan mun gama munay ne tafara tashi ta

nufi dakinta kafin hajiya nan kausar tace ya karin hakuri nace

Alhamdulilah tace bakomai mun zama daya ki dauke sis dinki kai na daga

mata nan tace da safe zamu fita sai ki sai abun da baki dashi to na amsa

nace Aunty Kausar sai da safe tace Allah ya kaimu a hankali na haura

sama gun dakina kamar munafuka ina shiga na kwanta ina tuna irin

tsanana danake hango irin tsanar da munay take min a idonta nan naji

wasu sabin hawaye suna zubo min kofar naji an turo da sauri na daga

kaina munay na gani fuskanta ba ko alamar anuri nan gabana ya fadi,

kafarta daya ta daura akan gadon daya kuma na kasa ya tsanta ta nunani

da shi kee duk randa naga kin nuna shigewarki a cikin gd nan sai kin raina

kanki san nan ke zakina gyara min dakina da wanki under wears dina da

nawa san nan kika kuskura kika fada ma mum nasaki wayan nan aiki ko

Aunty Kausar sai kin raina kanki san nan bana son kina shige ma Ammar

don ba tsaranki ba( jama‟a kutayani jin karfin hali anan harda kashe

kamar ba tare ta gansu da Ammar ba) Kuma bana son in ina falo kina

yawan zuwa kinji ko idan kika kuskura kika tsallake doka daya to zaki

gamu dani sannan kika fada ma Ammar wlh wlh wlh kinji sau uku na

rantse sai na kulla miki sharrin da bazaki iya warware ba sai kowa ya

tsane ki kuna jina ko cikin rawar murya mai shirin kuka na daga kai wani

harara ta sake min da baki na miki magana ko da kai nan nace da baki

tace to da baki zaki amsa min nan nace mata to ta rike kunne na in kunne

40 WHATSAPP 08105882006

Page 41: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

yaji jiki ya tsira kai na girgiza mata kafin ta sakar min wani rankwashi

wanda har kwakwalwan kaina sai da naji shi. Ammar ko ya na kwance sai

juyi yakeyi duk ya damu da kewar auta wanda in da sabo to ya kamata

ace ya saba don baya ganin wata mace sai ita hakan yayita sakawa da

kwancewa ganin ba zai fiddashi ba yasa ya dauro alwala ya soma nafila

daga nan yasoma rairo karatun al-qur‟ani mai girma da muryansa mai

dadin sauraro dake yana da hadda akansa abun sai wanda yaji(ya Allah ka

azurta mu da ilimi mai albarka da amfani amin) sai da yayi adu‟o‟i mai

yawa kafin ya shafa sannan ya kwanta yana mai tunanin abunda ya aik ata

a ranan na alkairi da istigifari har bacci ya daukesa Zee auta ko duk da AC

dake dakin bai hanata zufa ba sai gumi ke keto mata tana kuka marar

sauti wayyo Allah na yau nayi rashin iyayena yau gani cikin kunci kun tafi

kun barni ina ma da zanbiki yau na fada rayuwan da bansan wata irin

kunci zanulyi ba dad dina ka tafi kabarni wayyo Allah na ka kawo min

agaji. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:44PM, 9/20/2016]

Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Washe

gari Kausar ta dauko wasu katanta masu kyau ta ba ma auta san nan tace

tayi wanka zasu shiga kasuwa hajiya ta bada kudi ayi mata sayya godiya

tayi sosai daki tashiga tayi wanka wani dogon riga tasaka dark blue da

gyalansa tayi rolling bakaramin kyau tayi ba nan ta fito dai2 lokacin

munay tashigo hajiya da kausar suna ganinta suka fara tafawa kausar

tace Zee kinyi kyau baka danba hajiya mamu tace Masha‟allah gsky kinyi

kyau yata wani bakin ciki ne ya daki zuciyar munay don ta tsani ace ga

wanda ya fita kyau ita gani take tafi kowa kyau nan ta gode musu ta

karaso suka shiga motar kausar suka nufi kasuwa sunyi sayya sosai kafin

suka dawo gd suna shi gowa ta hango ammar a gate suna zaune da mai

gadi nan tayi gunsa da fara a suka gaisa kausar ta karaso suka gaisa,

ammar yaji dadi ganin auta cikin farin ciki sosai nan yayi godia ma kausar

sosai don yaga tana da nutsuwa ba kamar Munay da rawan kai ya mata

yawa ba nuna isa haka suka nufi gd bayan sun huta auta ta nufi kitchen ta

taya hauwa aiki bayan sun gama ta je dakin Munay ta gyara san nan suka

ci abinci rana. * * * * * * Hajiya Mamu ta bama ammar driver gd tana so

sai taga yanayisa kafin ta daura sa akan dukiyarsa kafin Ahyan ya dawo

41 WHATSAPP 08105882006

Page 42: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

daga turai tun da yakusa zuwa ganin gd kafin ya koma duk yanda sukayi

to. Haka rayuwa tayi ta tafiya auta na cikin kunci amma ta boye sai dai

tayi fari sosai ga hutu amma fa ta rame sabida damuwa haka take

bautawa munay ko tausayinta bata ji baran itaga ba mum da kausar a gd

tana mata ba dadi kam. Haka rayuwa yayita tafiya yau sun dauki shekara

2 a gidan yanzu hajiya tasa ammar akan karamin shagon kayan ta wanda

yake cikin garin bauchi mall ne babba duk abun da mutum kenema zai

samu hakan yasa ammar baya zaman gd sai shago yanzu hajiya tana jiran

Ahyan in yazo zasu yi magan daga na Ammar sai ya fara harkokin kasar

wajen kawai tunda taga yana da AMANA. * * * * * Yau gd an tashi da

shiri don gobe bros dinsu Ahyan zai dawo daga turai kausar ne taja auta

sukaje kasu nan suka suyo kayan vegetables nan kausar ta umurci auta da

gobe zasu shiga kitchen tunda taga auta gwanar girki ce kuma ta iya sosai

Munay wani haushin auta take ji don bataso ta kusanci Ahyan don tasan

zai yi wuya yaga auta bai kyasa ba tunda tana da kyau dai2 gwargwado.

Washe gari duk inda kaleka agidan kamshi yakeyi Kausar da auta ne a

kitchen sai sarrafa girki sukeyi abun sai wanda ya jiyo don ina daga nan

yawuna har ya tsinke bayan sun gama suka jera komai a inda ya dace nan

kausar tace auta ta shirya da ita za aje dauko Ahyan wanka tayi sosai kafi

tayi kwalliya Munay ko tace duk yanda zatayi sai ta han ata zuwa don

bazasu tafi da wan nan mai kodaden fuskan ba, sai da munay ta shirya

kafin tazo dakinta ta shigo ko sallma babu ta kali Zee Auta tabbas kam

tayi kyau amma sai tace ko tsari bakiyi ba ina zakije da kodaden fuskan ta

ki mai kama da na biri wlh na kuskura na ga kin saka kafa kin bimu sai

Kinyi na dama da mata harara sama da kasa tace sannan kuma kisani

daga yau bake ba kwaliya bake ba zaman falo kinji ko auta da idonta ya

kawo hawaye ta daga kai da alamar eh kafin munay ta gita a dakin falo ta

fito tasamu kausar ta fito nan tace ina Zee take Munay tace ai bazata ba

ko mai yasa oho kema kya gayyaci wannan kofadiyar kausar kalon

tambaya ta mata duk da haka bata daddara ta haura sama tasamu auta

ta kifa kanta tana kuka kausar da sauri ta hau kan gado lfy zee auta tace

kaina ke ciwo bazan samu zuwa ba ba yanda kausar ta iya dole ta hakura

ta sauko ta ja mata kofar suka nufi AVUBAKAR TAFAWA/BALEWA

42 WHATSAPP 08105882006

Page 43: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

AIRPORT BAUCHI, kausar ke jan motar suka nufi airport suna isa suka

samu jirgin tasauka har fasinja sun soma saukowa tun da suka iso na zuba

ma kofar sauka inga masu fita tun daga nesa na hango wani guy shidai ba

fari bane amma ba laifi ya hadu sosai yana da tsayi da fadin kirji fuskansa

dauke da murmushi hannu sa rike da wata jaka yana sanye da jar riga da

yar bakar falmara yana sanye da bakar wando jeans da takalminsa baka

da ratsin ja abun sai wanda ya ganin tun daga nesa na hango kausar fara

ary ya karu da sauri ta mike tanufi wan nan guy din mai kice da kyau don

kalo daya zaka masa kaga hutu da wayewa sun masa yawa ga boko

kunnesa makale da yar manne kana gani kasan yana taba rayuwa sosai

amma fa ya hadu ba laifi. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam

[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A.

Kardam ®WWA® Kunnensa makale da dan kunne manne ka na ganinsa

kasan yana taba rayuwa yahadu ba laifi sai dai bai kama kafar Ammar ba

don ammar na daban ne shi, kausar na hango ta nufi guy din nan tana

fara‟a tana isa kusa dashi dukayi shaking din hannu tace ur wlc bros

fuskansa dau ke da murmushi yace tanks my lovely sis munay ce ta iso da

mirmushinta amma sai wani kwar kwasa take kai ka dauka gun sau

rayinta zata tana ziwa tace ur wlc tanks yace mata Kausar ta karbi yar

jakar hannunsa kafin suka rankafa zuwa inda motarsu take suka nufo gida

cike da murna. Zee auta tun bayan fitarsu ta ci kuka har tagode ma Allah

ita yanda rayuwa ke zuwa mata kenan tana fita a wannan zata shiga

wancan amma zata daure ko kadan barata bari ammar ya sani ba don ta

ga yana cikin kwanciyan hankali. Matsawan ya sani dole ne subar gidan

ko ya dau mata ki ni kuma bazan zamo silan rugujewan farin cikinsa ba

tunda baya son ganina cikin damuwa hmmm a hankali na sau ke wani

ajiyar zuciya tare da cewa ya Allah gani gareka ka fiddani a cikin wan nan

hali, Alhamdulilah ala kuli hallin. Saukowa nayi daga kan gado na nufi

dakin munay duk ta birkita kaya haka na tattara na shiha toilet shima duk

ta bata sai da na gyara mata kafin na tafi na Aunty kausar na ita ma na

gyara mata duk da yana gyare bayan na gama ne na fito na nufi cikin na

debi abinci na ci na yi wanka na kwanta don banson in ketare dokar

Munay banson abunda zaisa ta wula kanta ni bayan nayi wanka Al -

43 WHATSAPP 08105882006

Page 44: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

qur‟ani na dauka nasoma karatu har zuciyata, tayi min sanyi nan na

kwanta kan sallaya bacci ya dauke ni ban farka ba sai karfe 2:30pm

wanka nayi ina son in fito falo ina tsoron karo da su manay ga warning

din da tamin kar in sake inyi make up kuma kar na hadu da Yayan su

Ahyan ko mai yasa oho ni ina ruwa na ma da shi gashi tasa nayi nisa da

Ammar dina dole wanda kullum muna tare da shi ga kulawar da yake b

an na musamman nan take naji wasu kwallan ta kaici yana zubo min na

goge hawayena na jingina da gado na fara yan adu‟ah dana saba ina mai

adu‟ah ma iyayena da sauran musulmai. Sannu a hankali suke tafiya yana

kallon yanayin garin kunnensa dauke da ear peace yana bin wakokin

Arjuli siyn shararen mawakin da ke raira wakokin India Ahyan yana son

wakan sa sosai don shi ya raira wakar Ashque ma, a haka har suka iso G R

A, a hankali Kausar ke tukin har suka zo kofar gate din su horn tayi cikin

nutsuwa kafin mai gadi ya bude musu kofar gate din taje tasamu parking

tayi parking da murna ya fito yana kiran Mum yayi cikin gd hajiya mamu

ta fito da murnanta ta tari danta nan ta kawo masa ruwa mai sanyi sai

kaga bakin hajiya mamu har kuni danta namij i tilo ya dawo yau kam

murna ba a magana sai da ya huta kafin suka nuna masa dining kausar da

munay suna gefensa Mum dinsu da kanta tayi serving dina sosai ya ke cin

abincin yana santi bayan ya gama ya nufi dakinsa ko ina a gyare sai

kamshi ya keyi wanka ya shiga bayan ya fito ya yi sallah sannan ya sake

fitowa falo hira suka dan taba kafin H Mamu tace yaje ya huta nan ya tafi

dakinsa kausar itama dakinta ta nufa. Rash Kardam AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Kausar tana shiga dakinta ta ganshi a

gyare ko ina murmushi tayi Allah sarki baiwar Allah gsky auta tana da

halin kwarai ko jikinta barin dubota yanzu haka halan ko abinci bata ciba

dakin auta ta leka ta ganta jingine da gado ta lumshe idonta da alamar

kamar bacci take amma ba baccin take ba fr idge taje ta dauko mata

kunun aya ta nufi kitchen ta dauko mata abinci da plate ta dawo dakin a

hankali ta ke tada ta Zee ta bude idonta taga Kausar ce murmushi tayi

tace Aunty Kausar kun dawo lfy ya hanya kausar tace wato ko ki fito ku

gaisa da bros ko auta tace zanje in gaida shi Kausar tace to tashi kici

abinci na san yanzu haka ba abinda kika ci ba musu auta ta mike taci

44 WHATSAPP 08105882006

Page 45: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

abinci sukayita hira harsai la‟asar kausar ta nufi dakinta don ganatar da

sallah la‟asar auta ma sallah tayi bayan sun idar ne suka shiga kitchen

sukayi abincin dare bayan sun fito ne auta ta koma daki don yanzu ta

hana kanta zaman falo bata son hayaniya sam. Ammar business ya zauna

ga shago sai kara habaka yakeyi abun sai son barka burinshi kulum

autarsa ya ganta cikin farin ciki san nan komai ya samu ita yake sayama

wa haka account dinsa ma da sunanta ya bude duk kudin da ake basa

nasa yana sawa a gun kamar kulum da ya saba zuwa sari kano yaje yayi

sari nan ya ga wasu dogayen riguna masu kyau haka ya saya musu su uku

Zee Auta maroon da ratsin golden colour na kausar baki na munay ash da

ratsin baki sosai yayi sayya yana ta sauri ya dawo don ya gana da dan

hajiya mamu wato Ahyan don shima ya nuna nasa farin cikin dawowarsa.

* * * * * Kaduna kuwa haka rayuwan futha da sadiya ya kasance yan zu

futha ta gama diploma har tasamu Admission a degree tana gamawa zata

tafi school of law haka tacigaba da gu danar da yan bincikenta don ta dau

ma kanta alkawari sai ta gano wanda ya kashe ma auta iyayenta. Sadiya

ma haka abun yake karatunta take cikin kwanciyan hankali amma sai dai

kulum tunaninta autar ta awani haki take ga iyayenta ku su nuna

damuwarsu a kan magana gashi dukiyar sai habaka take abinda ya daure

mata kai yanda taga wasu mutane tu da alamar ko bacun ransu baba isiya

da Abbanta basa son gani gashi kuma mai gadin gidansu Auta da sun

dawo sun dinke da iyayenta kuma wani abun daure kai yanda pinky

kewasa da naira ba mai kulata sai kara daure mata gindi akeyi in yau ka

ganta awan nan motar gobe da wancan kawaye kuwa sai yayan manya

take harka da su abun sai hmmm don yanzu ji take da kanta tana kallon

Big Girl ce ita ga naira ga hutu. Ammar ya dawo yayi murna da ganin

Ahyan sosai ya kawo tsara ba masu auta da kausar san nan yanzu an

yanke shawarar zai fara fita waje nan yayi murna da godia san na n ya ce

ma auta ya kamata suje kauye su gaida su Inna larai da Malam don su

musu karamci da bazasu taba mantawa ba, hajiya mamu ya samu ya

mata bayani tayi murna san nan ta basu goma na arziki sukai musu nan

kausar tace zata bisu tunda gobe zasu dawo munay sai wani yatsina take

ita ala dole tana kyamar yan kauye, Tunda Ahyan ya dawi ko da wasa

45 WHATSAPP 08105882006

Page 46: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

basu taba haduwa da auta ba yau kwanansa 4 ya ba masu kausar hakuri

akan kayansa ran Thursday sai iso sukace ba matsala, Ammar wanka yayi

sosai haka ma auta sunyi kyau kausar ta dau Camera don tana son zuwa

kauye ran asabar da safe suka dauko hanyan suwa kauyensu Malam suna

masu farin ciki. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam

DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT

WWW.AREWAFLEX.COM

[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam: [10:47AM, 4/5/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Sai karfe 12:00 suka

isa garin sun samu su inna cikin lfy bakaramin murna sukayi da ganinsu

ba nan ina ta musu tuwon geronta mai kaushi miyar danyen kubiya ga

man shanu sosai su kaci suna zuba santi baran Kausar ma tafi kowa santi

don ta dade bata ci irin wan nan abicinba ga surki yaji suga sosai koni

rash sai da na lashe baki don yawuna yana tsilo tsabar kamshi ya ishen.

Sai da suka huta bayan sunyi sallah asazahar tukun ammar ya basu

tsarabansu nan sukayita murna kafin suka fara hiran yaushe gamo nan

ammar ke bama su inna lbr bayan barin su garin sun tausaya musu sosai

sai yamma sukayi wanka suka fita zaga gari dandali suka nufa tun daga

nesa suka hango yam matan garin sunyi wanka masu sayar da abinci na

sayarwa abun dai sai kun gani. Najaat ce da tawagar kawayenta tunda ga

nesa ta hango ammar da su auta zunguro ummen da zulai kaii kalli

wancan kamar wanda suka taba zuwa maciya da malam la shine dan birni

kai kali wancan auta ta nuna sina kama da wan nan yar India mai

gashinan ga kawarta ma kamar yar india nan suka saki baki sai kallinsu

suleyi haka su auta da kausar da ammar sukayita hotuna sai magriba

sukamar dandali suka dawo gd bayan sunyi sallah ne suna zaune suna

hira sukaji surutun mutane da yawa kuma mata sai azo a dan lekasu a

koma can dai abun yayi yawa sai malam ya mike ya a hankali ya fake aiko

lokacun su najaat suka leko karaf malam ya rike ta waye nan tafara inda2

daman tazo gaida ina ne sai taga yan birni malam da ya gane waye sai ya

46 WHATSAPP 08105882006

Page 47: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

kyaleta yace su bar labe ba kyau nan suka shiga cike da murna suka gaida

su inna sai satan kallon ammar sai da suka dade sosai kafin suka musu

sallama suka nufi gd su malam ma sukayi sallama wa su auta suka shiga

dayan dakin inna da kausar da Zee suka kwana daki daya da safe inna ta

soya musu kosai da yar tsame ta musu kunun tsamiya haka suka karya

cikin farin ciki daga nan suka fara shirin dawuwa bauchi, Su inna sun cika

mu da tsaraban kauye su daddawa ne wake gyada kuka harda zuma,

Wanka sukayi sannan ammar ya ciri 10k ya bama malam inna ko 5k godia

sukayi sosai kafin suka rakosu gun motarsu suka dau hanyan bauchi. Tun

bayan da su kausar suka tafi kauye da yamma ahyan tazo cin abinci ya ga

ga abinci har abinci a ido yana sawa a baki yaji ba test karshe haka ya

hakura tea ya hada ya sha mum ma da tana sawa a baki ta ajiye gashi

hauwa bata nan ta shiga cikin gari yau munay ce tayi abinci sai da ta sha

tea kafin ta kira munay tayi mata fada akan ta dage ta koyi girki din girki

shine mace kiga kausar da Zee mana yanzu ina ne zasuje baza suyi abinci

wa mitum yaci har yana santi Munay sai zun bura baki takeyi ita a dole an

mata fada ta tashi ta nufi daki sai kunkuni takeyi haka dai a daddafe suka

kai washe gari Mum ke musu abunci ahyan ma ya masu kausar ta dawo

don yafi gane cin abincinta sai ko in mum ce ta musu yana ci sosai. Ba mu

iso cikin gari ba sai kusan 1:40 dake ba mu fito da wuri ba ko da muka

dawo wanka mukayi muka ci abinci kafin mukasa aka shigo da tsaraba

muka nuna wa mum yau hauwa‟u mai girki ta dawo dan haka daki na

nufa na fara baccin gajiya. Yau kwanan mu 3 da dawuwa daga kauye

kulum gidan mu cike yake da wakar india daga gani nansan yayan su

kausar ke sawa kuma shima da alama masoyin wakokin india ne kulum in

ina daki yasa wataran nayi rawa wataran in zauna ina bin wakar baran

wakikin Arjuly Siyn ina son wakarsa yau tun da safe munay tazo ta min

warning in gyara mata daki san nan in kade mata cikin Waldrop dinta zata

fita sai yamma zata dawo tun da ta fita nasa ka wando wizy da yar rigata

mai dan tsayi ya kama jikina nan nashiga na gyara ma munay daki na fito

zan sauka kasa dauko dauko fresh milk insha don nayi aiki sosai ina

fitowa naji daga wani dakin da ke kusa da down stairs naji ansaka wakar

Vear wai take Surili akhiyon wale, daman mayar wakan ce ko ada nan na

47 WHATSAPP 08105882006

Page 48: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

fara tika rawa irin na wakar don mutum2 ake wakar amma ni daya nakeyi

sai nan take na tsinci kaina cikin ni shadi ina bin wakar ina rausayawa.

®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam AMANA TA CE By ©Rasheedah

.A. Kardam ®WWA® A hankali ya ke saukowa sanye da 3quater da yar riga

mai gajeren hannu, ya jimma a tsaye yana kallonta wannan wacece da

bai taba ganinta ba ko ita ce Zee din da mum ke fada gsky yarinyan ta

hadu ba laifi wani juyinda tayi a rawan sai da yasa Ahyan hadiye yawu

don wannan tana daya daga cikin irun matan da ya ke so ta hada koma2

gyara tsayuwa yayi yana kallinta don baison ta bar rawan, Sam ita bata

san da mutum ba tsakaninta da Allah take tika rawa, Dai2 nan Ammar ya

shiga kallon ta yakeyi cike da so da kauna dake yasan ita mayyar wakokin

india ne ganin auta cikin farin ciki yasa shima ya tsinci kansa cikin farin

ciki sai a lokacin ya lura da ahyan da yayi tsaye yana kallonta nan take

ransa ya baci kishin sa ya motsa bai san lokacin da yaje ya mata wata

damka ba kee baki da han kaline bakisan akwai wanda bai kamata su

kalleki haka ba tsaya wa nayi ina masa kallon tuhuma sai a lokacin naga

ahyan ya karasa saukowa sai min wani kalo yake wanda ni kaina sai da na

tsargu, Munay ce ta shigo ko sallama babu ganin irin hallin da muke ciki

yasa ta nufo ni da sauri kee baki da han kali ne zaki fito cikin irin wan nan

shigan duk ta rude kai ka rantse a kwai mijinta a ciki na fito da wan nan

shigan nan take jikina ya hau rawa da gudu na haura sama ammar kam

dakinsa ya koma ransa duk a jagule ahyan kuma bayana yabi da kallo

yaga duk yanda illahirin jikina yake motsawa tabbas dole yasan abinyi

akan wan nan yarinyan. Wacece Hajiya Mamu?,.. Asalin sunanta Maryam

Alkali haifafiyar garin katsina ce aure ne ya kawota bauchi, Hajiya mamu

ta taso cikin kulawa da tattalin iyayenta Alhaji Alkali mutum ne mai

karamci da sanin ya kamata yana da mata daya mai sunan Xahra mace ne

mai mutumci da kamala shekaransu 2 da aure basu sami haihuwa ba sai

da suka shiga shekara na 3 Allah ya basu haihuwar diyarsu ta farko

maryam inda suke kiranta da Mamu sai bayanda suka sanu shekara 4

Allah ya sake basu haihuwar fatima haka suka taso cikin kulawa da

kaunar juna inda mamu tayi aure ta auri wani shararen dan kasuwa

bayan tayi aure da wata 3 Allah ya bata cikin ahyan haka sukayita tattalin

48 WHATSAPP 08105882006

Page 49: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

cikin har tazo ta haifeshi yaci sunan Ahyan ma‟ana Gift of Allah Bayan

shekara 2 akayi bikin fatima itama bayan aurenta da sheka 4 ne ta haifi

Kausar kenan kausar yar kanwan hajiya mamu ne tunda fatima ta haifi

kausar ta kamu da lalurin rashin lfy bata dade tana jinya ba Allah ya karb i

abunsa nan H Mamu ta karbi kausar ta dawi hannunta sai da kausar ta

kusa 4 years hajiya mamu ta haifi munay haka taci gaba da kula da

yaranta tana basu tarbiya mai kyau mijinta yana kasuwancinsa ka Allah ya

sanya musu Albarka dukiya sai haba ka yakeyi kwanaki sunja lokaci ya tafi

har ahyan yagama secondary nan Abbansa ya fara shirye2 na fitansa

karatu waje yayi hatsari ya rasu tabbas sunji mutuwar nan ba kadan ba

bayan yanyi arba in ne hajiya mamu tayi ciki ciku yatafi karatu kasar waje

nan ita kuma tani mi aiki tana zuwa sam taki aure don tana kula da

yaranta Kausar dake tana kama da mamarta in ka ganta baakace ba

hajiya mamu bane ta haifeta ba don suna kama munay da dad dinsu tayi

kama sam ita halinta ya fita daban bata son kowa a kusa da ita ga jinkai

ga nuna isa kamar yar President.. Lol… Yawancin kawayenta yaran manya

ne bata harka da yaran masu kananan karfi acewarta za a raina ta don

kalin kanta take kamar yar gidan dan gwate ….lol… ®WISDOM HAUSA

WRITERS Rash Kardam [7:54PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Hakan yasa munay bata son talaka

komai nata da yayan masu kudi take harka , Tunda ahyan ya tafi sai sai

suyita waya da yan gida acan turai kuwa ya samu abokai yan duniya

bushashan su kawai sukeyi duk da bai yi wasada karatu ba amma baka

rasa shi gidan faty rawa duk ya iya zuwa amma sam bai shan giya hasali

ya tsaneta sosai da sosai haka rayuwansa ya kasance har zuwa yanzu da

ya rage masa 1 year ya hada masters dinsa shiyasa komai nasa ya ban2ta

da sauran ga wata yar dan kunne manne da ya makala a kunnensa, wan

shine lbr H mamu. Jiki ba kwari na haura dakina tabbas yau na san munay

sai ta min ba dadi ga ammar ransa ya baci anya na kyauta masa kuwa duk

yanda yake kokarin kyautata min ace yau ni na bata masa rai gsky banyi

adalci ba bau kyauta ba take naji wasu zafafan hawaye suna gan2min

kwanciya nayi nasoma kuka maras sauti, kamar daga sama naji an zuba

min dundu har kirjina sai danaji ya amsa munay na gani da bulala ido na

49 WHATSAPP 08105882006

Page 50: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

zaro nan na sauko na hada hannuna biyu na fa ra bata hakuri. kee yar iska

mai kodadden fuska waya baki daman saka wayan nan kayan bare kiyi

make up har ki sauko falo nan take muryana tasoma rawa dan Allah kiyi

hakuri munay ta dago dorina kamar zata zuba min na runtse ido sai

hawaye amma sai naji shiru a hankali na bude idona sai naga tana harara

na tace daga yau ina kara ganinki a tsakar gida sai kin gayama yan

garinku, kinci sa‟an yau yan mutuncina suna kusa da kinji ajikinki ban

tankaba tace kuma ki shirya kabar punishment na musamman. Fuuuu ta

fitanan na saki wani ajiyar hrt nayi hamdala da bata bugeni ba. Ahyan

kuwa yana haurowa sama yana ta bin dakunan da kallo don ya ga wanne

ne wan nan yarinya ta ke ciki har ya iso dakinsa nan ya zauna a yar

kujeran da ke dakin ceke da tunani. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash

Kardam [7:54PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Gsky wannan ta hadu komai nata

das2dashi nan ya kasa shan malt din da ya dauko ya kwanta ko da ya rufe

ido Zee yake gani shi kadai sai wani smile ya keyi wan nan tasa ce dole ya

bi duk yanda zaiyi ya mallaketa. Ammar ko da kyar ya isa daki kirjinsa ya

masa nauyi yashiga tsananin damuwa don karara ya hango tsananin

sha‟awa auta a idon Ahyan kuma gashi da alamar bayida kamun kai nan

ya dau ruwa ya sha ko zaiji sanyi azuciyarsa amma ina nan yakama zarya

a daki yana tunanin abunyi shin ko zai tun kari auta ya fada mata yana

son ta ne wata zuciya tace kar tace bata sona ya zanyi gashi ina tsananin

kaunarta auta tamkar wata bari na zuciyata ce matsawan ba ita ba zan

rayu dai2ba nan ya tuna komai yayi zafi a kwai Allah take ya soma

karanto adu‟ah kafin yaji sanyi a ransa. H mamu ko sai yamma ta dawo gd

bayan ta huta ne ta leka dakin kausar tasamu tana bacci ta wuce dakin

munay bata nan daga window ta hangota a garden, nan ta fito ta nufi na

Zee auta tana kwance da sallama ta shiga jin muryan H mamu yasa ta

mike tana mata sannu da dawuwa bayan sun gaisa tace yana ganki haka

auta ta kalo murmushi tace bana jin dadi ne tace ayya sannu kinsha

magani kuwa tace eh tace to Allah ya sauwake, ameen tace daman ina

son in fada maki gobe zani Sokoto akwai abunda zanyi tace to Allah ya

kare ameen tace kafin ta mike ta nufi dakin Ahyan kwance ya ke akan

50 WHATSAPP 08105882006

Page 51: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

katuwar katifar sa idonsa na kallo sai da ta taba sa tukun ya mike tace

mai kake tunani haka kai ya sosa yace mum ba komai tace fadamin dai

tace ba kimai tace ok daman so nake ka shirya gobe zamuje sokoto da

safe samu fita ido ya zaro nan ya tuna da auta ga dama ta zoma sai yayi

saurin cewa mum gobe ina da abokina zai zo daga abuja kinga in na tafi

ban kyauta ba tace ok zan tafi ni kadai in yaso kafin ka koma sai kaje ka

gaidasu ya ce to, tana fita ta tarar da kausar ta tashi ta fito falo ga hauwa

da munay nan nan ta zauna sukayi hira nan take fada musu tafiyanta

kausar tace zan biki mum munay tace nikam inaga sai bros zai tafi sai

mitafi tare mamu tace Allah ya kaimu suka amsa da ameen tace ma

kausar sai ki shirya yanzu don mass zamu bi ba flight ba tace to da sauri

tayi dakinta ta shirya su munay da mum suka shiga hirarsu. Washegari da

sa ahyan da kansa ya kaisu tashan mass suka shiga mota sai da suka tashi

kafin ya dawo gida, ya yi wanka ya fita yau yana cikin farin ciki yasan yau

zai san yanda zaiyi samu ya biya bukatarsa don tunda yazo 9ja bai samu

ya biya bukata ba gudun kar Mum dinsa ta ganesa. Auto ko sai kusan

10:am ta fito zata gyara ma kausar daki don ta bata sallahun ta gyara

mata ta wargaza gashi suna sauri tazo tasa shiga dakin dai2 munay ta

hada tea zata sauka fafo sukayi karo nan take tea ya zube ajikin munay

cikin bacin rai ta wanke auta da kyakyawan mari har sai da ta rike

kuncinta sai da taji radadin ya ragu ta daga hannu zata rama komai ta

tuna sai ta fasa auta ido ta zaro lalle yau da kin gane kurenki wlh eyeh

lalle kin samu kanki a bakaken larabawa…lol.. Amma zanyi maganinki

fuuu ta koma daki don dauraye jikinta auta na kuka ta gyara gurin da tea

ya zuba sannan ta shiga dakin kausar ta gyara ta fesa room freshener ta

ja kofar ta koma dakinta taci kuka ta gode ma Allah bata sake fitowa ba

sai rana lokacin hauwa ta gama abinci ta debo ta koma dakinta, Bayan

sallan la‟asar munay tayi shirinta ta fito don zuwa gidansu kawarta fiddy

ta zo don ta sa auta ta gyara mata daki ta taba taji ta kulle ta kwansa auta

najinta taki budewa dole yasa ta fita sai da tayi nisa kafin auta ta bude

taga alamar bata nan ta koma ta kwanta ko kofar bata rufe ba. Ahyan

yazo shigiwa anguwan yaga motar munay tafita cikin murna da zumudi

yayi azamar zuwa gd don yaje ya samu biyan bukatarsa gun auta ya dan

51 WHATSAPP 08105882006

Page 52: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

danata don yasan zai huta yanda take ja gata da yalw ar kirji komai nata

dabane wani murmushin mugunta yayi yanufi gidan horn biyu yayi mai

gadi ya bude masa ya nufi parking space ya a jiye motar da sauri ya nufi

cikin gidan har yana tuntube. Nima Rash ina ganin haka na bisa da sauri

don in ga mai zai aikata nan take faba yasoma dukan tara2 bakina yana

raa ina furta bai ra……..pp….. Din…Zee…Aut…..zai… Sai kun jini da

daddare. ®WISDOM HAUSA WRITERS Rash Kardam [7:54PM, 9/20/2016]

Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Da

sauri ya shiga gidan, yayi hanyar stairs a hankali ya ke tafiyar, sai da ya

taba kofar dakinta yaji a bude, kafin ya nufi nasa ruwa ya watsa, ya sanya

kanan kaya maras nauyi, ya nufi fita daga dakinsa kenan, wayar sa tayi

kuka, badan ya soba ya juyo ya dauki wayar, sunan Jenifa ya gani a

scream din wayar, da sauri ya daga daga daya bangaren akace hello my

luv, ya kk? Ya 9ja? yau she zaka dawo ne?nayi missing dinka da yawa, nan

ta fara masa salonta na janye hankali, “take ya manta da abunda yayi

niyya” suka shiga hirarsu ta masoya, bai ankara ba, sai jin ana kiran sallah

mangariba, sai lokacin ya tuna kudirinsa, da sairi ya ce mike yana fadin

oh!!! Shirt, ya tsa ya ciza, kafin ya kashe wayar, ko sallama baiyi ma jenifa

ba, Yana fitowa daga dakinsa ya ga munay tana haurowa, sam bais o ta

dawo, batare da ya cimma burinsa ba, sannu da gida ta masa, ta wuce

dakinta, haka ya hakura yakoma daki, yana jin haushi kansa da ya biye ma

jinifa, (ni kuma Rash nace bawan Allah ko ka manta duk wanda ya rike

Adu‟ah Allah, ba zai kyale mun gu ya cucesaba, sai bisa jarabta ko

kaddara). Ammar ko duk hankalinsa bai kwanta masa, da ahyan sam, ana

sallah magriba ya dawo gida, sai da yazo ya samu auta tana sallah, bayan

ta idar ya tabayi lfy ta, ya ajiye mata abunda ya sayo, kafin ya koma

dakinsa, auta da wuri ta rufe kofar ta, sanin halin munay, kartazo ta

cimata mutunci, aiko munay tana zuwa ta kwan2sa kofar dakin taji akule

ba haka taso ba. ba yanda ta iya taje ta kwanta. gari na wayewa, bayan

auta tayi sallah, ta yi karatunta sannan ta mike taje ta hada tea ta dawo

tana breakfast, sai ga munay tazo, fuskan nan ko alamar murmushi babu,

nan take gaban auta ya fadi, kanta ta sunkuyar kasa, tana zuwa, ta zauna

a yar kujeran da ke daki, ta daura daya kan daya, tana kada kafa. Kee

52 WHATSAPP 08105882006

Page 53: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

waya baki damar da har zakina kulle daki?, ko kin manta da doka na ne?,

auta ta kada kai alamar àa, to maza ki bar cin abincin nan, kije ki hadan

breakfast, cikin sanyi jiki, tace mai zan hada miki?, wani mugun kallon da

tamata yasa ta yi shiru, idonta duk ya kawo kwalla, munay na fit a ta nufi

kitchen, haka soya mata Chief da indomee sai tea da yaji kayan kamshi, ta

kawo mata daki, ta ajiye zata fita munay tace inagama ki dawo kizo

kittara kwanukan kai ta kada mata, ta fita da sauri, sabida kukan da ke

shirin zuwa mata. “Allah sarki rayuwa nikuma haka Allah ya tsara min, Ya

Allah ka bani ikon hakuri”, kuka tayi sosai kafin ta share hawayenta, ta

nufi dakin munay ta debi kwanukan kenan, munay tace dan ajima kimin

girki da dan yawa, don ina „suspect” din a kwai bakin da zanyi in sunzo,

san nan ki tabbatar yayi dadi, in ba hakaba, kin san saura ta fita, adakin ta

je ta jiye, falo ta gyara, bayan ta gama ta nufi dakin ammar ta gaidashi,

ciki2 ya amsa nan ta bashi hakurin abunda ya faru, sam ba zai iya fushi da

autarsa ba, dole ya huce suka danyi hira, kafin ta dawo cikin gd. Ahyan

kuwa tun daren jiya, ya gama kwanton baunan sa, Allah bai bashi sa‟a ba

yayi ta zarya amma ta rufe daki, dole ya hakura ya kwanta cike da haushi.

auta da wuri ta daura girki, ko ina a gd sai kamshi ke tashi, bata gama

girkin rana ba sai 3:40 tashiga tayi wanka, ta dauko kayan da Ammar ya

musu tsaraba tasa, gata fara ga kayan maroon da baki, bakaramin kyau

ya mata ba, “(ko kai mai karatu katsara irin wan nan kaya a idonk ya kake

ganin auta zata fito)”. Munay manya bacci tasha, sai da ta tashi wanka

tashiga, tana fitowa ta bude sif dinta tana zaban kaya can idonta ya kai

kan wani green sai lokacin ta tuna Ammar ne ya sayo musu a dubai da

yaje sari, da sauri ta dauko, nasan yau un yaganni da shi zaiyi farin ciki,

tana sawa tayi make up kamar zata bar kasan. Misalin4:30 wayarta tayi

kara, tana dagawa taga bsty ta ce, da sauri tace ya kun isone?, bsty tace

eh, right!,…. gani zuwa da sauri ta nufi gate, tana zuwa ta hango su,

oyoyo ta musu, kafin suka rankwafo zuwa falo. bayan sun zauna ne

munay tace kee auta!!, auta!! auta!! cikin isa da gadara take kiran, Ganin

bata fito ba yasa tayi hanyan stairs, fuskanta dauke da kwandon bala‟i.

auta ko jin kira bana karau ba, yasa tafito da sauri sam bata lura ba saiji

tayi garam!!….. Sunyi karo da mutum cikin tsoro ta ja da baya kee yar iska

53 WHATSAPP 08105882006

Page 54: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

dan ubakin waya baki damar tafiya kwa2ra agidan nan?, ta sadakar da

duka kwai, duk tsoro ya cikata amma jin ta zagi ubanta yasa taji wani

bacin rai da karfin guwa yazomata. ®WISDOM HAUSA WRITER‟S Rash

Kardam [7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam ®WWA® Da karfin guwa, ta soma zazzaga ma

munay masifa wanda, wanda yasa munay sake baki don bata taba

tsammanin ta iya masifa ba. sai a lokacin taji muryan xarah na cewa

munay kika bar wan nan mai kama da Aljanan, take miki rashin kunya,

daga hannun munay ta kai mata mari, auta ko cikin zafin nama ta rike

hannun, ido munay ta zaro sai a lokacin ma ta lura da kayan jikin ta, aiko

take ranta ya kara baci tayi kam ta da niyar duka aiko auta ta damko ta,

sai lokacin karfi ya zo mata nan ta shake munay, sai ga idonta ya fito

alamar tafiya taji shaka, xahrah da kaltum suna ganin haka, sukayi kan

auta zasu fara jibgarta sai ka ahyan ya shigo ko sallama babu, yana yar

wakansa, ganin abunda ke faruwa, yayi kansu kai!! meye haka? Mts ya

fisgo xahra da kaltum, kafin ya kwace munay, sai haki takeyi, auta ko jin

wuyanta ya bushe ta wuce kitchen ta dauko faro mai sanyi, tana takun

isa, ta zo falo ta taras yana fada wa munay, suna hada ido ta yi mata

gwalo, nan munay takara harzuka sosai, kamar zata fasa ihu. Auta bata

gama gyara zama ba, taji tsayuwar motar Ammar da sauri tayi mike don

bata son ahyan ya tafi ya barsu, zasu iya mata rashin mutunci, kitchen

taje ta dibi rabin girki da tayi wa munay, duk da tasan ya masa yawa,

amma don ta kularta, ta diba da yawa sosai, tazo ta wuce su tayi dakin

ammar lokacin yana cire ta kalmi, da sallama ta shiga, kalonta ya tsaya yi

don tayi kyau sosai, bai san har ta iso gefensa ba, sam ya shagala da

kalonta sai da ta hada hannunta tana tafawa, kafin yayi firgit ya sauke

wani ajiyar hrt, sannu da zuwa ta masa, ya amsa da sakin fuska, kalonta

yayi, ya ce my sis gsky na iya zabe, don kayan nan ba karamin kyau suka

miki ba, murmushi tayi tace na gode Allah ya kara budi, ameen ya ce

barin watsa ruwa, tana zaune ya shiga dakinsa, sai da ya dau 10 minutes,

kafin ya fito cikin kaya maras nauyi, abincin ta zuba masa, nan kamshi ya

fara dukan hancinsa, aiko bai tsaya wata2ba ya fara diban abinci yana

santi, sai da yaci yayi rabi sanna ya sha ruwa, yace Alhamdulilah. Hira

54 WHATSAPP 08105882006

Page 55: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

suka rinkayi yana bata dariya sai kyal2lewa takeyi, sai da aka kira sallah

magriba kafin ta masa sai da safe, ta nufi cikin gd, sai da ta dan leka ta ga

basa nan, ta nufi kitchen da hanzari ta ajiye cooler ta nufi dakinta, key ta

saka tayi sallah haka har akayi isha‟i ta kwanta. Da safe ta hada breakfast

ta dibi nata ta koma daki, bayan ta karya ta koma daki, bata fito ba sai

karfe daya ta daura na rana lokacin munay na bacci, tana gamawa ta diba

ta koma daki, bayan taci wanka tayi ta zauna tana duba littafin adu‟ah.

Sai kusan uku taji tashin mota tasan munay ce, tana tabbatar da ta bar

gidan ta fito ta nufi kitchen ta gyara ta kama wasu ayukan. Su mum sun

isa sakoto lfy, tayi duk abunda ya kaita, da taso su kwana 2 amma sai aka

mata kiran gagawa dole suka shirya don ta jirgi zasu dawo yau din nan 5

jirginsu zai sauka. Auta ko han kali kwance take aikin ta, har da yar waka

ta, ahyan ne ya shigo gd ya leka daki munay yaga bata nan, murna fal

ransa ya nufi dakinsa ruwa ya watsa kafin ya canza kaya zuwa boxer da

singlet ya nufi dakin auta, nan yaga fata dawo dakin ba, buya yayi a toilet.

Auta na gama aikinta ta shigo dakinta, bata rufe kofa ba turawa tayi don

zata koma jimawa kadan ta dauko zobon da taha kafin ya yi sanyi, kan

gado ta fada, bata wani dade ba ta fara gyan2di, a hankali ahyan ya bude

kofar, lokacin bacci barawo ya dauketa, kusa da ita yazo nan ya fara mata

wani irin salon, “(ido na zaro ina rokon Allah ya kubutar da wannan baiwa

daga hannun wan nan maras tausayin)”. Auta kamar daga sama taji ana

mata wasu abun da ya basa tunaninta, a hankali ta soma bude ido ganin

ahyan yasa tasoma kokawan kwace kanta, amma ina yafi karfinta, sai

kokarin rabata da kayanta yakeyi, da kyar ya samu ya yaga rigan jikinta,

ganin daga ita sai bra yasa ta ja da baya ga hawaye da ke zuba, shiko sai

wani dariyan mugunta yakeyi, haka har suka iso bangon dakin, ya nufota

gadan2 tasaki wani razanane kara, Wanda yayi dai2da shiigowan Ammar

gidan, bai karasa parking ba sai ga su haj ia mamu sun iso, auta ganin ba

wanda ya jita yasa takara takarkarwa iya karfinta tasaki ihu ta fadi kasa

sumamiya, shiko hakan baisa ya ci gaba da abunda yayi niyar yi ba. aiko

dukansu da ammar da su hajiya bansan wanda yafi wani gudun shiga ba,

nima ina ganin haka na bisu da mugun dugu har sai da wayata ta fadi.

Mai karatu ban samu daman daukar wayata ba, nabisu don inji gurmin da

55 WHATSAPP 08105882006

Page 56: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

za a toya, kar ya wuce ni, in na dauko zakujini a next page….lol… Taku a

kulum mai kaunarku Yar Mutan Kardam ®WISDOM HAUSA WRIT ER‟S

Rash Kardam [7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam Da gudu suka nufi cikin gidan, duk a rude suke,

ammar garin hawa stairs ya fuge kafarsa, nan take sai ga jini ya soma fita,

amma ko ta kansa bai bi ba, yana isa yaga kofar arufe yayi zaton da key

ne ajiki, komawa yayi da baya yayi wani duka ma dakin, sai yaga ko motsi

baiyi ba kafin yasake naushin, H Mamu ta zo da sauri ta murda kofar sai

gashi ya budu, duka suka shiga dakin, abunda suka gani ne yasa su suman

tsaye, ammar da gudu ya kaima ahyan damka wanda shi gaba daya baya

cikin hayyacinsa yana kokarin kire ma auta skirt yakeyi, ammar ya shake

wiyarsa ya makasa da garu take kansa yasoma zubda jini, ran hajiya

mamu ya baci idonta ya rufe, ga hawaye zai zuba yakeyi dai2 na n munay

ta shigo ganin abunda ammar yake ma bros dinta yasa tafara dukansa

wani naushin da ya mata sai da ta fadi gebe dan azaba kasa kuka tayi,

hajiya mamu tazo tafara taya ammar dukan ahyan, sai da suka ga baya ko

motsin, suka kulyalesa, kausar kam kuka take kamar ranta zai fita, ammar

da gudu ya dauki auta yayi waje da ita wanda marabanta da gawa

kadanne, kausar da H Mamu suka rufa masa baya, akabar munay da bros

sai kuka take tayi. Ni‟IMA CLINIC, ya nufa gudu yakei kamar zai tashi sama

har sai da yan hanjin cikin kausar suka kama disko, suna isa emergency

suka nufa, da sauri nurses suka karfe ta suka shiga da ita, ba a dade ba na

hango Mrs Adul cikin shigan kayan likita, tayi emergency, ammar ko kasa

zaune yayi sai zagaya wa yakeyi, yana hawaye nan wani bakin ciki ya

tokaresa, bai san lokacin da ya buga hannunsa a garu. Har sai da hannu

tayi kass, kausar duk ta tsure da lamarinsa daman haka yake da zuciya, (ni

rash nace hmm). Can Mrs Abdul ta fito fiskan nan baya bo ba fallasa da

sauri Ammar yayi gunta, Dr ya jikintan? Ta tashi kuwa? Atare ya jero

mata wayan nan tambayan, ajiyar zuciya tayi kafin tace Alhamdulilah,

bata tashiba amma zamu ce da sauki, amma meye ya razana ta haka don

tayi dogon suma, amma muna sa ran farfadowanta a kowani lokaci,

aziyar hrt ammar yayi, Mrs Abdul taci gaba da cewa, zamu kaita dakin

hutu ba kuma mai zuwa kusa da ita don bata son hayaniya, suna tsaye

56 WHATSAPP 08105882006

Page 57: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

akazo aka wuce da ita special room, hajiya mamu kam duk takasa cewa

komai wai ace ahyan ne ya aikata haka, ina tarbiyan da tabasa duk yasa

kafa yayi watsi da shi, in sonta yakeyi, mai yasa bazai fada mata, sai ayi

musu aure ba? Dole in gwada wa ahyan bacin raina dole nasan abin yi,

kausar kam kasa hada ido tayi da ammar don tana jin tsanar ahyan amma

sun gode ma Allah da Allah yasa bai kita mata haddi ba. Munay kuwa

ganin kar dan uwanta ya mutu, yasa ta mike tana dingishi, ta nufi harabar

gidan isa mai wanki ta ganin nan ta kwala masa kira, kazo ka taimaken,

sanin halinta yasa ya biyo ta da sauki, sama suka haura nan tace ya

kamata ahyan ahaka suka fito, mai gadi ke tambayan ta, maike faruwa?

Wani mugun kalo tamasa wanda yasa dole yaja bakinsa yayi shiru, sabida

sanin halinta, da gudu suka nufi T.H, suna zuwa emergency ta kaishi nan

doctors sulayi caaa akansa basu dau lokaci ba suka gy ara masa ciwon da

yaji kuma ya farfado amma sun masa aluran bacci, sannan suka nufo

munay suka fada mata san‟nan ta tanadi kayan tea, don in ya farka ta

fara bashi ruwa mai zafi ya sha, nan tayi godiya ta nufi hanyan gd. Ammar

ko ganin an wuce da auta ga kayan da ke cikinta duk ayage yake wani

sas‟san jikinta na aje, yasa ya nufi gd don ya dauko mata kayanta acanza

mata, bai ce kala wa H Mamu ba don wani haushin su yakeji, fita yayi ya

nufi gd a mota don yana hanzari baya son yin nisa da auta, gani yakeyi

kamar za‟a sake mata abunda aka mata, yana isa gd, dakita ya nufa ga

mamakinsa bai ko ga su munay ba amma dake ba damuwar sa bane

kuma baya son ganin su, nan ya dau mata fallen zani da karamar riga, sai

hijab, yazo fita kafarsa ta gogu da takalmin auta nan yaji wani azaban zafi

da sauri ya kali gun, sai alokacin yaga ciwon da yaji, bai tsaya takan ciwon

ba yazo sauka daga stairs yaga munay tana tahowa sai dingishi takeyi,

wani mugun kalo ya watsa mata, fuskansa sam ba ko annuri, kamar

baitaba dariya ba, nan take wani tsoronsa ya dira mata azuciya. Luv u all

my fanz Rash Kardam [7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

By ©Rasheedah .A. Kardam Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron

ammar ta ke baran da ta tuna nashin da ya mata da sauri ta dawo da

baya, ta sauko sai da ta bashi hanya ya fita, sannan ta haura ta debi duk

abunda zata diba ta dau poss dinta dake tana da kudi aciki ta nufi asibiti,

57 WHATSAPP 08105882006

Page 58: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

tana zuwa ta nimi gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa, tana fatan

Allah yasa ya tashi. Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa ajiye ki din mota,

don shikam yabar amfani da abun gidansu kuma yau zaisa afara nima

musu gd, don tabbas shine silan ja ma auta wan‟nan abun, in da bai yarda

yazo gidan nan ba da ahyan bai mata haka ba, ko da ya fita abokinsa

auwal ya kira yace masa gd yake so mai dan saukin kudi, amma ba wanda

yake da mutane da yawa ba, auwal yace an gama zuwa gobe zakaji

“feedback” nan sukayi sallama ya nufi asibiti, yana zuwa yasamu H mamu

suna inda suke sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta, gsky tayi masa

karamci gashi tilon danta na miji ta wasa abunda bata tana zaton zatayi

ba, bata so kanta ba ta bama dan ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika

mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take son yayan wasu ta kuma kula

dasu tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah yasa ja miki ya biyaki da

rikon gsky da kika mana ameen, amma bazan iya cigaba da zama‟a cikin

gidan ki ba, don tunda yasoma kuskuranta, nan gaba zaiyi abunda yafi

haka ni daman hankalina bai kwanta dashi ba, cikin zuciyarsa yake

magana, sai da yaji H mamu tace ammar sannu da dawowa, firgigit ya

dawo hayyacinsa, Murmushi ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi, ammar

duk yaba ma hajiya tausayi lokaci daya duk ya canza kamar bashi ba,

kausar tamasa sannu, ya amsa ya tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu

dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya kamata su je gd su huta, h mamu

tace ina ae ba inda zata zata kwana da auta, tace kausar taje gd, ido ta

zaro don auta bata tsira itama tanaga intaje abunda zai mata kenan bare

uwansu badaya bare uba, don da aure a tsakaninsu, aji yar hrt tayi kafin

tace mum kata kafarki, h mamu dake babbace ta gano kausar kuma sai

taji badadi azuciyarta danta yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da danta

sai Allah duk da taga laifinsa amma sai da taji wani iri, yan‟uwa ya kamata

mu na tausaya wa iyaye mu kyautata musu, don sun sha wahala ba kadan

ba akan mu ya Allah kaba mu ikon tausaya musu da jin kansu, kaman

yanda suka mana muna kanana Ameen). Su hajiya mamu da kausar suka

kwana a dakin masu jinya, shiko zama yayi a kofar dakin akwai chair

azaune ya kwana da safe bayan sunyi sallah yaje ya sayo musu abinci,

suka karya sai ga Dr ta zo nan suka gaidata, suka tambayeta ya mai jikin

58 WHATSAPP 08105882006

Page 59: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

tace musu da sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa ce tayi kara yana

daga wa yaga auwal da sauri ya dauka, bayan sun gaisa y ace my man an

samu gida ku biyu ne aciki amma yace min daki2 ne in kana da tym sai

kazo muje a nan dutsin tanshi ne, yace ba matsala na gode sukayi sallama

ya kashe wayarsa, sai kusan 10 ya bar asibiti direct gun auwal yaje, sun

duba gd ba laifi yayi gashi daki dadai ne, ko wan‟ne da bayi aciki san‟nan

akwai kofa a tsakiya, sai ta waje ma akwai kofa kamar na falo ta wajen

gidan sai yar karamar gate dake gun, kuma gidan na da kyau sai na dayan

yana tsam‟manin ciki da falo ne da bayi, sai kitchen da wani karamin daki

na saka kaya, dake bauchi muna da arahan haya kudin ba masu yawa

bane, 60k ne kawai nan yaga arahansa don inda a kaduna ne abun sai a

slow, nan yace zaibada kudin zuwa jimawa san‟an yasa aka kira masa

almajirai ya biyasu yasa su wanke masa dakin don yau zai kwaso musu

kayansu ko gobe. Yana fita bank yaje ya zaro kudi a account dinsa don

duk wata hajiya mamu na sallamansa da 30k kudin da take basa gashi yau

kusan shekaran su 2 da wani abu, a gidan kunga ya dan samu wani abu,

duk abunda ya kamata ayi anyi, yaje gida dakin auta ya kwaso mata

kayan ta dake sif dinta wanda yasan‟nata ne, shima ya dibi nasa, ya ajiye,

kasuwa ya shiga ya sayo musu katifa manya guda 2, yazo ya ajiye, ya gaji

likis gashi yanzu magriba ta kusa duk da yana lekasu ya tambayi lf y auta,

yanzun ma asibitin ya nufa. Munay tana zaune ta zuba tagumi, ahyan

yasoma bude idonsa, yana kalon dakin da kyau, sannu a hankali ya komai

yasoma dawo masa, kara yasaki yana kiran no! no! no!, ( nikam nace to

no! Din na me nene ko yaso sai ya gama biyan bukatar sa ne? oho, ko

haushin da mum dinsa ta gansa ne? Oho zamuji koma miye nan gaba).

Taku a kulum mai kaunar ku Rash Kardam [7:57PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Ahyan bakaramin

damuwa ya shigaba, yau yasan mum dinsa tayi fishi dashi bai kuma

kyauta ba, dole yaje ya bata hakuri, da kyar ya iya shan tea ya sha magani

ya koma ya huta. Yana isa asibiti ya gaida su H mamu, san‟nan yanufi gun

Dr yake tambayart cikin Zee tace d sauki, dakin ya dawo ya zauna a gefe,

ya zuba ma auta ido ko kyaftawa baya yi,wayar H Mamu yayi ringin tana

dagawa taga munay ce, da kamar bazata daga ba, amma sai ta dauka

59 WHATSAPP 08105882006

Page 60: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

daga daya bangare akace, “hello mum ya kk? Mum duk abunda bros ya

miki ya kamata kiyi hakuri ki tausaya masa, kizo ki ga jikinsa , a kan

wan”nan yar da ba‟a san asalinta ba, sai wai2 amma ki kyale dan ki

wanda kikeso” wani tsawa ta daka mata nikaina sai dana tsorata, wato

munay kema bayansa zakibi ko? Kuma kar in kuskura inji kin kara zaginta

ni baruwana da shi, har sai ya gyara halinsa tukun mtss ta kashe, ammar

har rashi saida yaji taisayinta don tacika uwa ta gari ba mai son kanta ba,

sai yau yaji kara sonta a matsayin uwa, “Allah ya biyaki mum”, kausar ma

jikinta duk yayi sanyi ammar yayi karfin hali yace mum kije ki dubasa da

jiki, duk abunda zaiyi bazaki taba kankare alakar kuba, “hannuka baya

ruba ka yanke ka yar” dan kine dan haka adu‟ah shine mafita, taji dadi

amma bata nuna ba sai kawar da kan ta tayi kamar bata jishiba. Zee ce ta

fara motsi kada2 sai tasaki wani kara take sukayi kanta dukansu, ihu take

tana kiran sunan Allah, sai kuma ta soma cewa Ammar…. ammar…..

Ammar kazo ka kwace ni zai kashe wayyo Allah na, wayyo mum kun tafi

kun barni, ammar da sauri ya je ya kira Mrs Abdul da sauri sukazo allura

ta mata take bacci ya sake daukarta, Mrs Abdul tace karku damu zata

farka cikin hankalinta, ajiyar hrt ammar yayi godia ma Allah dr tafita ta

basu gu. Sai can dare ta farka, taga mum nan ta soma tuna mai ya faru

kuka tayi sosai, mum na lalashinta, tea ta hada mata tasha ta kai mata

ruwan wanka tayi taji dadin jikinta kafin tayi sallah. Ahyan kuwa an

sallamesa cike da tsoro da zullumi ya shiga gd, da farko kam yaki shiga sai

da munay tashiga ta duba masa ko mum na‟nan, taga batanan tukun ya

shiga gidan. Kausar jin munay na gd yasa tadawo kuma hauwa mai aiki ta

dawo yau, tukun ta koma gd, ya rage h mamu ke ajikinta, gsky ta gwada

musu kulawa. Sai can yamma ammar yazo yana gun cuku-cuku neman

shagon da zai dan sari kaya yazuba aciki, ya fara business da yan kudin da

ya tara na albashin da yake samu. Sai da ya gaida h mamu tukun ya yima

auta ya jiki? ta amsa da sauki, sun dan taba hira kafin yace ma mum yana

so zai roki gafaranta don ya mata laifi sai da ya bata hakuri kafin yasanar

mata da hukunci da ya yanke, da farki taso taki akansai dai ahyan ya

bargidan, ammar ya nuna mata ilan hakan san‟nan ta amince, sun na

cikin hira Mrs Abdul tazo ta basu sallama, kaya suka tattara san‟nan ya

60 WHATSAPP 08105882006

Page 61: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

tsara musu napep suka je gudan sai da h mamu ta gyara ma auta daki duk

da a gyare yake kafin ta musu salama akan gobe zata dawo. Ko da ta

koma gd tasamu ahyan ko kalon inda yake batayi ba, da gudu yazo ya rike

kafarta yana bata hakuri tureshi tayi ta wuce idonta cike da kwalla, “a

zuciyarta tausaya masa amma sai ta gwada masa kurensa”. Washe gari

sukaje da kausar suka duba auta tare da kayayaki bayan sun dade suka

musu sallama suka dawo, washe gari ammar ya tattara yan kudin h

mamu da ya sani da wasu ta kardunta ya kaimata yabata hakuri sam bata

so ya bar yi mata business ba don yaron yana da “AMANA”

DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT

WWW.AREWAFLEX.COM

amma ba yanda ta iya haka ta hakura nan ta dibi kudi mai yawa tabasa

yayi godiya ya fito kenan suka tsaya da mai gadi sunyi hira sosai sai kusan

9:00 ya nufo gida ya sai musu nama da yan kayan motsabaki abakin titi

mai mashin ya ajiye shi yazo shiga lugun gd da suka koma wasu yan‟isa

suka tsaresa harda wukakensu suka nuna kudi suke nema baiyi musu ba

ya basu kudin da aka bashi, har sunce ya tafi dayan yace kai tsaya ban…..

Taku mai kaunar ku a kulum Rash Kardam [8:00PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Wani daga cikinsu ya

ce tsaya, baiyi musu ba ya tsaya, daya daga cikinsu yace haka zamu

kyaleshi baiji a jikinsa ba,ammar adu‟ah ya ke tayi na neman tsari, gani

basa kusa da shi kuma yana yin kwana zai shiga gidan da suka kama, fakar

idonsu yayi yasa gudu don ya sadakar ko ya tsira ko su mishi illa, iya

karfinsa yake gudu yazo dai2 shiga gidan kafin ya bude kofar gdn, wani

daga cikin yan saran ya kai masa sara cikin ikon Allah bai same sa sosai

ba, ya shiga gidan sakata. Auta jin haya niya ta fito ita da matar gd sun

tsaya cirko2, nan matan gd take bata lbr yan sara garin nan take auta ido

ya ciko da kwala, yayanta ta tuna ko a wani hali yake oho nan ta fara

masa adu‟a kariya daga uban giji, suna tsaye agun sukaji an rufo kofa

matar rayi daki da gudu sabida tsoro, auta kam ko motsi kasawa tayi da

sauri tayi zaure tsaban dakiyar zuciya tana haska wa taga ammar da sauri

tazo ta rike hannusa tana hawaye shiko ido ya runtse sabida safin ciwo

61 WHATSAPP 08105882006

Page 62: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

sai mai da numfashi yake yi kama hannunsa da auta ta yi yasa ya bude

idonsa, han‟nu da ba ciwo yasa yana goge mata hawaye suka nufi daki,

dan kwalinta ta yanka biyu ta daure masa han‟nu tana masa san‟nu ya

amsa. 3yrs leter Garin kaduna wata kyakyawan yarinya na hango cikin

farin ciki ta nufi gidan inspector Abubakar ko dana kare mata kalo naga

futha ce ta kara girma sosai tadawo cikakiyar mace abun sai mai karatu

ya ganta, cikin murna iyayenta suka tareta bayan yar kwarya -kwaryan

malimar da aka shirya mata, sadiya ma ta hallara inda yanzu tagama

karatunta ta dawo cikakiyar yar‟jarida walima ya gudana cikin kayatarwa.

Baku tambayeni ya labarin pinky yar‟rawan kai, hmm ku biyo ni

kuji.duniya ta juya don yanzu pinky ko yar motar da take ja babu don

yanzu dukiyar baba isiya ta kare ba abunda ya rage masa yanzu sai

diabetes da tasa sa agaba har an yanke kafa daya gasa rai kwa -kwai

mutuwa kwa-kwai, don shi tun daga duniya yafa ganin nasa saka makon

bai ko ina ba matansa sun gujesa don tanzu ba abun duniya. Baba sani

kuwa ba laifi komai yana tafiya yanda ya kamata don har ya manta da

wasu yan‟uwansa da kuma yar‟auta rayuwansa ya ke ci son ransa. Garin

bauchi kuwa ammar da auta ci gaba ya samu cikin she kara biyu Allah ya

buda wa ammar ya albarkaci dukiyarsa da ya nema da guminsa yanzu

shaguna 2 garesa na atamfa da shadda less masu kyau sai na takalma da

jakukuna, wani abun dadi sunan auta yasake mayarwa, haka rayuwansu

ya kasance cikin jin dadi da farinciki, watara na ammar suna zaune da

auta take cemai tana son suje kaduna ko da ba dade wa zasuyi ba, ina

son inga futha da sadiya don nasan bayan tafiyata suna cikin damuwa ina

son inga wasu yan‟uwa, ammar yace ina sane da haka don ba yanzu nake

son zuwa ba akwai lokaci in muna raye don na dau wa kaina alkawarin

matsawan ina raye sai na dau fansa masu Dad da mum kuma sai a n yanke

masu baba sani hukunci dai2 da laifinsu, auta har cikin zuciyarta taji dadi

ta kuma kara masa fatan na sara. 5 weeks leter Ammar ne a shago yana

ta fama da jama‟a cikinsa ya fara murda masa tun na daurewa abun har

yasoma da munsa kafin kace me ammar ya fadi akasa cikin firgici yaron

shaginsa ya dauwaya yana son ya kira auwal abokinsa ya kira auta cikin

rudewa yake mata bayani akan zasu kaishi asibiti, sai da tayi magana ya

62 WHATSAPP 08105882006

Page 63: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

ga ba auwal ya kira ba, da sauri ya kira na auwal akwai yace gani a kofar

Central market din yanzu zan shigo da gudu yazo suka daukesa sai

“NI‟IMA CLINIC” auta cikin rudewa ta kira wayansa nan auwal ya daga

tana kuka tace kuna wani asibiti ne yace suna ni‟ima tace to gata zuwa,

duk da bawani yawo take a gari ba mai napep tatsara ya kaita tana zuwa

ta samu auwal sai safa da marwa yake a kofar emergency, nan yasoma

lallabinta don kuka take sosai, ana cikin haka nurses tafito ta ba ma auwal

ta kardan magani yace bari yaje ya sayo. Dr tace tafito auta na ganinta ta

nufeta tana hawaye Dr ya jikinsa, ta ce da sauki, ke ce matarsa, auta

kamar ta ce aa ta dauka ba wani abu bane kawai sai tace eh nice ok!! Ki

biyo ni office to tace Dr tayi gaba tana binta a baya sai da sukaje wani

office ta nuna mata kujera ta zauna, sai da Dr ta cire glass d in idonta, tace

ya sunan ki madam tace Zainab, Dr tace zainab daga ganin ki kamar

wayyayiya amma kina abu kamar baki san komai ba, ae yanzu kai ya

waye, duk auta na cikin duhu sai da Dr tace mai yasa baki ba wa mijinki

hakkinsa kinsan laifin ki kuwa Allah na fushi dake haka mala‟iku suna

tsine miki, ga shi kinsa mijinki cikin wani hali yanzu in ya fara bin matan

banza fa hakki na kanki, don a yanzu haka sperm ya masa yawa don in bai

samu ya biya bukatarsa ba zai iya shiga ko wani irin hali, auta sai da taji

gananta ya fadi, dake Dr macece nasiha ta mata sosai, tukun tace ta je ta

duba mijinta, sai a lokacin suka ga sun dade sosai kusan 1hrs tana mata

nasiha kwatance dakin da aka kaisa tamata, auta jiki ba kwari ta fito ta

nufi dakin. Ammar ko bayan da aka masa allura ciwon cikin bai dade ba

ya lafa, auwal a gefensa kusan 40 minutes yayi ya farka dake jinisa da

karfi ko alluran bacci aka masa bai cika dadewa ba, nan auwal ya fara

masa nasiha akan tunda auta yakeso ya fito ya fada mata ko yanimi wata

ya aura, sai da yagama maganarsa kafin ammar ya fara magana da ni

bana son takura ma zainab don banga alamar tana sona ba, abunda ya

hanani sanar mata kenan kawai shakuwar da mukayi ne, ni kuma banjin

zan zauna da wata mace kamar bazan iya mata adalci ba, zuciyata z ainab

take so, sai hawaye ya fara zuba masa amma zan bama zuciyata hakuri

matsawan zainab taki amincewa na auri wata ko don gudun fadawa

halaka. Auta da ta dade da isowa tana shirin shiga taji anakiran sunanta,

63 WHATSAPP 08105882006

Page 64: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

nan taji duk abunda suke fada kuka takeyi tana fadi bazan iya ba Ammar .

Hmmm karkuso ku gani alokaci idi na zaro don tsananin mamakin auta

duk halaci da ammar ya miki cab… Ko dai mai take nufi zamuji nan gaba.

Taku a kulum mai kaunar ku. Rash Kardam [8:00PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Ammar abu duniya

ya ishe sa, zaune yak‟e a shago, ya zabga tagumi, wayar sa ce tayi kara ya

duba yaga Auwal ne, ya dauka da sallama sa, daga ban garen Auwal yace”

kana jina Ammar ta fiya ce ta kamani ta gaggawa zan fita zuwa waje,”

kana leka min gun business dina komai ake ciki kana sanar da ni. Ammar

ya ce “ba matsala Allah ya k‟are,” sai ka jini. Hajiya Mamu ce zaune tak‟e

na zarin hukunci da yakamata ta yanke ma Ahyan, ta dad‟e ta na tunani,

kafin naga ta saki wani lallausan murmushi, wanda hakan yak‟e tabbatar

min da ta samu amsa ta. Munay ce ta shigo gdn, H Mamu ta mata kalon

tsaf tana na zarinta, sunan ta kira Munay zo nan, tazo ta zauna, a nats‟e

ta ke kalonta, Munay ina kike yawan zuwa kw‟ana b‟iyu?, ba kya yawan

zaman gida, fada min?, “cikin zafin rai tayi maganar.” Munay duk ta

tsorata da yanayin Mum dinsu, kame-kame ta far‟a yi, tsawa ta sake daka

mat‟a, Mum da… Ma..umm..um.. Wani mari ta sakar mat‟a, kin bar fit‟a.

“sam ni ban yarda da tarbiya kawarki sholly ba. Fada ta mata sosai, ta

tashi ta bar Munay a gun. Ahayn karatun sa yak‟e ba wasa, duk randa

zasuyi waya da “Munay sai ya mata nasiha sosai mai shiga jiki. Don shi

yanzu ya fita harkan yan‟matan b‟ariki, ya kima ga Allah. Auta z‟aune tana

nazarin abunda take ma Ammar sam wani sa‟in bata ky‟autawa amma ta

rasa mai yasa zuciyarta ke sata hakan, abun na da munta, ga wasu

muna‟nan makarkan da rakeyi, wani sa‟in ma ko ta f‟arka, bakinta kasa

furta addu‟a ya keyi. Haka rayuwan su ya kasance, ba d‟adi, don yanzu

“Ammar ya bar shiga harkanta,” tun daya gane bata son ganin sa bare

farin cikinsa. Sam ba zai iya mata wulakanci ba in ya tuna “Dad da Mun

da AMANATA da suka bashi, sai yaji ba zai iya wulakanta ta ba. Munay ke

shirin ta na zuwa gun “Malam don yau‟ne zai gama mat‟a hadin mafani

ta,da in ta tun kari “Ammar bazai iya mata musu ba. Da kyar ta samu ta

fito a gida ba tare da Mum ta ganta ba, ta dau hanyan Firo nane garin da

bokan yake. Tayi tafiya mai nisa har ta kusa g‟arin, tun daga nesa ta

64 WHATSAPP 08105882006

Page 65: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

hango wasu mutane sun taru amma basa da yawa, basu fi su b‟iyar zuwa

shida ba, sai da ta iso kusa ne taga wata motar da tana yawan zuwa gidan

Malam, kamar zata wuce ganin hatsari ne yasa ta d‟awo da baya ta tsaya.

Matar da tak‟e zuwa a motar ne ta yi hatsari, ga wasu muna‟nan magan-

ganun da tak‟e fada, ba dad‟i ji. ” ni Jimma‟i na kashe Farida, ni nayi asiri

ma Sadiq ya bata, ni na haukata zainabu” da sau‟ransu, abun ba dad‟i ji.

“Munay jikinta yayi sanyi, tasoma nadamar a‟bunda tak‟e aikata wa. Kafin

su bar guri “Matar nan ta cika tana ihu tana birgima a cikin dati.( Mata

muji tsoron Allah kar ku d‟auki zuwa gun boka a‟ bu ne mai kyau, tun

daga ranar da zaki sa ka f‟arki sallah bazata karbu ba, ga azaban lahira ga

haduwa da karshe maras ky‟au, muji tsoron Allah mu gy‟ara). Munay ta

shiga motarta, ta dawo gida cik‟e da nadama, kuma yau zata fasa

kwalban da “Malam yace asirin ciki kwalban, zai raba Ammar da Auta.

Kuma zan nimi gafaran su, kar nima nayi irin wan‟nan mutuwar. Garin

kaduna kuwa yau sun tashi da jimami don yau sunyi rashin “Baba Isiya,

Allah ya karbi abunsa.( tabbas duniya ba gurin zama ban‟e, ko kai ko ka so

sai ka bart‟a. Yan‟uwa mubi duniya, a san‟nu in ka d‟auka da zafi, zaka ga

da z‟afi, rayuwa bata da guarantee). Su “Pinky an shiga damuwa,” yanzu

sai Mum dinta k‟adai ta rage mata. “Ya Allah ka jarrabe mu, jarabawar da

zamu iya Ameen”. Auta ce zaune tana sauraron wa‟zin Malam ja‟afar

Mahamud Adam, sosai wa‟azin ke shigarta, gashi yana baya ni game da

yawan Addu‟a da amfanin zama da al‟awala, duk sai taji kamar ta ita

yakeyi, tunani ta far‟a ” Yaushe rabon da na zauna da al‟awa?, Yau she

rabon da na yawaita yim azkhar?. Tabbas ko tantama b‟abu shiyasa nak‟e

yawan ma farkai. “Yaro ne yayi sallama, ana kiran Zainab a waje,” wai

tazo yana jiranta. Wani gaushi ne ya tur‟nuketa, mts tayi tsuka. Taku a

kulum mai kaunarku Happy birthday to you Maman Abideen, i wish you

long life n prosperity. Rash Kardam [8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Auta ta d‟ade a bakin k‟ofar

“Room”, duk “maganar da su k‟ayi taji”.Kuka ta k‟eyi sosai tana fadin

no!! B‟azan iya ba, Ammar. Ta d‟ade a gun tana k‟uka, sai da taji „Auwal

na shirin fit‟owa‟, kafin ta share hawayen ta, nufi d‟akin. San‟nu tayi ma

Auwal, ta b‟aye shi, ya‟ya mai jikin? “Da s‟auki‟ ya bata amsa, a takaice”,

65 WHATSAPP 08105882006

Page 66: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

jikin ta ba kw‟ari, ta isa gun g‟adon, idon sa a lumshe”tamkar mai bacci”

kan “white chair” da ke gefen g‟ado ta z‟auna, sai da aka kira sallah la‟sar

kafin ya m‟ike ta basa “pure water”, yayi al‟wala. Dake ” jikin sa da s‟auki,

“Alhamdulilah”, b‟ayan ya d‟awo daga sallah, ta basa abinci da aka k‟awo

musu yaci. “Kw‟anan uku, aka sallame su, duk w‟ani hidima, “Auwal shi ya

yi musu, har aka sallame su”.*****Kw‟ana ki sun tafi, “Ammar ya daina

gani fuska a gun Auta” ta d‟aina shiga har kansa, duk ” Ammar ya fita a

hayyacin sa, ya rame ga damuwa ta masa y‟awa,” Auta ko bata ma san

yana yi ba”. Yau take “friday” ta fito gidan” Aunty Mamu ta kai musu

ziyara” tun tana napep ta lura da “wani mai jar m‟ota, yana binsu a b‟aya,

har suka iso k‟ofar gidan su, tana sallaman mai napep, zata shiga g‟ida,

sallama ya mata”Assalamu‟alaikum c‟ikin murya mai d‟adi” k‟amar ana

busa sarewa ya mata sallama”, Auta kamar zata shiga g‟ida amma s‟anin

muhimanci “sallama” yasa ta amsa ba t‟are da ta juya ba, cikin salo da

hikima, ya ke mata magana, wanda sai dayasa ta juyo, hira ya soma yi

m‟ata, tana yar dariya, sun d‟ade agun sosai, sai da yama sallama zai tafi

tana juyowa, “Ammar ta g‟ani ido sa c‟ike da kw‟alla ” abun gw‟ani

tausayi,” Auta ko kalo sa bata yi ba, tabi g‟efen sa ta wuce, hmmm nikam

n‟ace “Auta kar ki mana haka”. Soyayya ce mai k‟arfi ta kulu tsakani Auta

da Adam‟s abun ba‟a cewa k‟omai, “Ammar ko ya d‟awo “so silent”

komai ya cakude masa, ga son Auta da ke barazana ga rayuwan sa”, abun

sai Addu‟a. Munay ko duniya tayi d‟adi, yanzu ta samu wata kawa mai

suna Sholly ita ta k‟ara bude mata ido, har kan gaban su kawai suka sani

sune gun malamai, don su samu samari masu k‟udi. Ahyan k‟uwa duniya

ta masa kunci, sam mum ta fita a har kansa, gashi yau saura “3 days” ya

koma “school” duk b‟aya cikin hankalin sa, “ya‟yi nadamar abun da ya

aikata, yanzu a shirye yake da duk w‟ani hukuncin da “Mum” ta yanke zai

d‟auka. “Alhamdulilah, lfy uwar jiki b‟abu mai fushi d‟ake. Nagode da

kulawar ku gare ni, Allah ya bar zumunci” Ameen. Rash Kardam [8:00PM,

9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam

Yaro ne yayi sallama, aka amsa masa,yace”wai ana sallama da Zainab a

waje”. Mts taja tsaki cike da takaici Auta tace”kaje kace waye ne?, yana

fita takama guna-guni ita kadai, ni wan‟nan Adam din ya wani takura wa

66 WHATSAPP 08105882006

Page 67: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

mutum, mts haushi ma yake ban yanzu. Yaro ne ya sake daw‟owa

yace”wai inji Adam. Tace kace masa bata‟nan, Yaro ya tafi bai kuma

dawo‟wa ba. Auta tayi kw‟anciyar ta, tana mai tuna abunda tayi ma

Ammar, kw‟alane ya cika idon ta, tabbas ban ky‟auta masa ba, na dawo

butulu, ta yaya ma hakan ta faru dani?, har na aika ta masa hakan ya

zama dole in basa hakuri, don Ammar shine jigon rayuwa ta da farin ciki

na. Kuka ne ya kw‟ace mata, tana mai tuna iya‟yenta, addu‟a ta musu da

fatan samun Rahman Allah. Munay tana isa gida d‟akin ta, ta shiga ta

kw‟anta a bakin gad‟o, kuka taci mai isarta, tana danasani abunda ta

ai‟kata. Tace “Ya zama dole in‟nimi gafar su Auta, matsa‟wan in basu yafe

min ba, bazan samu Rahman Allah ba, don na shuga gakki su. Kw‟albar

asirin ta da‟uko, ta b‟oye a hijab d‟inta, ta nufi gurden, tana zuwa ta d‟au

katon dutsi, tayi bismilla ta kw‟ad‟a ma kw‟albar, nan take wani bak‟in

hayak‟i ya soma fita, gurin ya fara jujjuya mata, duk addu‟a da tazo bakin

ta yi take yi, sai da ta tsuguna kafin zuwa jimawa ta daina ji, da sa‟uri ta

mike ta nufi d‟akin ta, al‟wala tayi, ta fara sallah tana mai neman gafara

gurin Allah. Hajiya mamu duk shirin take yi ta na jiran dawo‟war Ahyan

zan iya masa hakuri matsawan zai bi umu‟rnina da sharud‟an da zan

gindaya masa to zan iya hucewa. Kausar ce ta i‟so falon tace “Mum na

gama duk aiki da kika sani. Ok!. Wayar ta ne ta yi ringing Ahyan ke

kiranta, ba kaifi da fara‟arta ta d‟au sallamansa. Cikin ladabi yace “Mum

ayini lfy?. lfyklau ya karatu?. Alhamdulilah!! “Mun ma gama yanzu results

muke jira nan da 5days zan dawo, Alhamdulilah!! Allah yasa a ga saka

mako mai ky‟au, Ameen Ya Allah. Cike da murna ya kashe wayar, yana

mai tam‟bayar kansa anya kuwa yau Mum dina ne ta amsa min magana?,

kuma Batare da ta nuna fushinta ba. Hmm!! “Ya zama dole in yi amfani

da wan‟nan lokacin don in wanke laifina. Da wayan nan tunanin yayi

bacci. Ammar ne ke shago duk ya rame ya fita hayyacin sa, waya yakeyi

da Auwal, sun jima suna tat‟tau‟nawa sukeyi sun d‟anyi hira sosai, Auwal

ya ce”ina dawo‟owa gobe fa, don akw‟ai abun da zanyi ran friday. Cikin

farin ciki Ammar ya ce haba? Eh! ya bashi amsa, to Allah ya kawo ka lfy

Ameen. Ya kashe wayar. Auta zaune take ta gama yan aiki da zatayi,

wanka tayi tasaka riga da skirt English wears, sun mata ky‟au. Tana zaune

67 WHATSAPP 08105882006

Page 68: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

taji gaban ta na yawan fad‟uwa addu‟a ta tsanata yi. Ammar ne ya sh‟igo

kai da ka ga yanayinsa baya cikin hayyacinsa, tun daga sha‟ago maransa

ya soma murd‟a masa, da ky‟ar ya‟iya k‟arasowa cikin gd, yana shiga dai-

dai k‟ofar d‟akin ya zube yana fidda wani-irin numfashi, da sauri Auta tayi

kansa, ta rike shi tana kuka, tana cewa”Yaya na dan Allah ka tashi ban son

irin wan‟nan wasan, nasan na maka laifi wlh na tuba bazan sake ba. Ina

sai wani rikon da yamata numfash‟insh‟i ya kara sama-sama, kai in ka

ganshi bazaka d‟au zaka dawo ka gansa da rai ba. Wani kara ta saki dai-

dai lokacin su Hajiya Mamu da Kausar da Munay suka shigo gidan, da

gudu sukayi dakin ganin halin da yake ciki Hajiya Mamu tace “Munay yi

sauriki juya motar nan zamu nufi asibiti da sh‟i. Matan da ke gidan ita da

mijinta suka sh‟igo, mijin shiya taimaka a ka sash‟i a mota suka nufi

asibiti. Dr ranan da suka kawo sh‟i ita suka samu. Emergency aka nufa da

sh”i sun dad‟e a kansa kafin Dr ta fito baalamar dariya a fuskan ta tace

“ma Auta da H Mamu su biyo ta office. Sai da ta zauna ta nuna musu

kujera suka zauna ta kalli Auta ta banko mata wata harara, “ke Zainab

wato ba ky‟ajin nasiha ko. “Anya kina tsoron kamun Allah kuwa?. Sh‟in

kin san hakki aure a kanki kuwa?. Cikin fada-fada take mata maganan.

Zainab ina tausaya miki, Auta kam in banda kuka marar sauti ba abinda

takeyi. Cikin rud‟u Hajiya Mamu tace” Dr ni ban fahimci mai kike nufi ba?,

Ina son ki min karin baya ni. “Dr bata boye ma H Mamu komaiduk ta

sanarma ta, “salati Hajiya Mamu ta saki ta kalli Auta, Zainab yaushe

Ammar ya sama mijinki?. Cikin kuka tace”Mum nifa lokacin da muka

kawosh‟i Dr ne tace ni matarsa ce?, shine nace mata eh! ban d‟auka abin

da zata fada ba kenan. Ajiyar zuciya Hajiya Mamu ta saki,san‟nan tayi

baya ni ma Dr yanda zata gamsu. Dr tace”na fahimce ku amma gsky

Hajiya d‟anki nacikin wani irin yanayi yana bukatar Aure don Sperm ya

masa yawa. Baran yau abun yayi worse, kuyi iya k‟oka kafin nan da

10days ku masa Aure, in ba haka ba zai iya fadawa halaka gash‟i haisai da

ya sumar da sh‟i. Hajiya mamu tace”Dr in Allah ya yarda zamuyi iya

k‟okarin mu ayi Auren kafin 10days din. Right!! Allah ya taimaka ameen

suka amsa.fitowa sukayi daga office d‟in H Mamu tana ta nazarin

wan‟nan Al‟amarin tanaga hadin dazata yi zai‟zo dai-dai lokacin Ahyan ma

68 WHATSAPP 08105882006

Page 69: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

ya dawo Allah yasa su bi umurni na, Ya Allah ka taimake ni akan had‟in

Auren yaran nan da zanyi Amern. Taku a kulum mai k‟aunar ku Rash

Kardam [8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam Munay da Kausar kulum suna hanyan Asibiti a

d‟an kw‟anak‟in da sukayi suna zuwa Asibiti Munay tana sh‟ish‟ige ma

Auta ta kuma bata hak‟uri akan abunda ya faru baya. Kw‟anan Ammar

biyu a Asibiti aka sallame sa, tunda suka dawo Auwal ke dawainiya da su,

sam bai nuna gazawarsa. Yau Ahyan zai dawo H Mamu ta kira Kausar

tace”ina son kiyi girki ma yayanki yau zai dawo, ta da‟uko wasu k‟aya

masu ky‟au tace kisa wannan zakije ki da‟uko sa daga Airport. Cike da

ladabi ta amsa tace”nagode Mum Allah ya k‟ara bud‟i yasa afi haka.

Ameen! Sai da ta gama girki kafin tayi wanka tasa goduwar rigace

bakaramin ky‟au ya mata ba. Key d‟in motarta ta d‟auko ta nufi d‟akin

Mum da sallamarta ta tura k‟ofar ta shiga, tace “Mum nagama girkin na

jera su a inda ya dace, kuma bros ya kirani yace nan da 40minutes jirginsu

zai sauk‟a, ina son inje da wuri k‟ar yayita jirana.H Mamu tace”to sai kin

dawo Allah ya kare, banda tuk‟in gan-ganci. Ta amsa mata da to ta fito

cikin nutsuwa take tafiya harta isa ABUBAKAR TAFAWA/ BALEWA

AIRPORT. Bata dad‟e da zuwa aka sanar nan da 5minutes Jirgin UK zai

sa‟uka. Jirgin na sa‟uka fasinja suka suma fitowa mik‟ewa nayi naje gurin,

sai da mutane suka fir-fito can na hango Yaya Ahyan cikin wata bakar

Suite yayi masifar ky‟au ya kara haske da k‟iba,sai ya dawo min tamkar

wani bako ciiin zuciyata nake cewa”gsky Yaya Ahyan na karshe ne duk

macen da ta same shi taji dad‟i,” Ya Ahyan yana matuk‟ar burgeni amma

kash zai yi wuya na saye zuciyarsa. Ahyan kuwa tunda yake sau‟kowa ya

ky‟alla idonsaa kan kausar sai da ya kusa suman tsaye, d‟an shek‟ara biyu

zuwa uk‟u da yayi baya gari, Kausar ta k‟ara cika da ky‟au tamkar ba ita

bace. Hmmm yace”Kausar ina matuk‟ar sonki tun kina yar yarinya amma

nasan Mum da wuya ta bani ke. Dai-dai lokacin ya iso kusa da ita. Sam

bata san ya iso ba saida ya hura mata iska a idonta wani sas -sanyan ajiyar

zuciya ta saki, sai alokacin ta farga ya iso kusata ita, watsowa yayi dab da

ita har tana jiyo fitar numfash‟insh‟i, ga shi duk ya cikata da kamsh‟in

turarensa Ayhan yace”Kausar mai kike tunani haka?. In ka ji yanda ya ke

69 WHATSAPP 08105882006

Page 70: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

maganar tamkar rad‟a zai mata a‟cikin kunnenta. Cikin jin kunya tace

maba babu ok! Trolley da ke hannu sa ta karb‟a suka sh‟iga mota, tun a

hanya Ahyan ke satar kalonta har suka iso gida. Munay tana jin tsatuwar

mota ta fito da gudu tana oyoyo my bros, tana i‟sowa sukayi sharking din

hannu, suka nufi cikin gd.sai da Ahyan ya huta Kausar ce tayi serving

d‟insa bayan yaci abinci ne ya shiga gaida Mum. Bayan sun gaita H Mamu

take tambayarsa Yaya karatu? Alhamdulilah! Yanzu kam mun kammala

result yayi ky‟au duka suka amsa da Alhamdulilah! Allah ya sanya Al‟k‟airi

Ameen. Mum tace”Ahyan kaje ka huta zuwa dare ina son ganin ka

zamuyi magana, ya amsa da to ya tashi ya nufi d‟akinsa da Kausar ta

gyara masa sh‟i. Ammar kam jiki Alhamdulilah ya war-ware har ya fara

fita, abunka da mai zafin nama. Yana zaune wayars tayi kara Hajiya

Mamu yagani cikin girmamawa ya d‟aga wayar bayan sun gaisa Hajiya

tace”Ammar ya karfin jikinka?, yace da sauki, tace Alhamdulilah! Yau in

ka taso daga kasuwa ina son ganinka da magriba, to Mum zan‟zo in Allah

ya kaimu, yauwa nagode sai‟anjima. Ammar na sallah magriba ya zo gun

Hajiya sai da ya gaisa da mai gadi kafin ya sh‟iga ciki. Munay ya fara gani a

falo yaukam cikin nutsuwa ta gai dash‟i ya amsa ta je kitchen ta kawo

masa drink da abinci, tace”barin k‟ira maka Mum din, bata jira amsan sh‟i

ba ta nufi sama, tana zuwa ta sanar da Mum Ammar ya zo H Mamu

tace”ki kaisa falon baki can zamuyi magana, sannan ki bi kice ma Yayanku

ya same ni acan to ta amsa. Sai da ta fad‟a ma Ahyan tukun ta sanar da

sak‟on Mun wa Ammar, dake ba bak‟oba ne falon ya sh‟iga ya zauna, sai

ga Ahyan ma ya sh‟igo hannu ya mika masa suka gaisa, Mum ne tash‟igo

itama da sallama suka amsa ta nimi gu ta zauna, nasiha ta musu sosai mai

sh‟iga jiki, sunansu tak‟ira d‟aya bayan d‟aya suka amsa ta d‟anyi sh‟iru

kafin tace”na yanke hukunci had‟aku aure da k‟anne ku. Cikin razana suka

d‟ago a tare suna kallonta, sake mai-maita abunda ta fad‟a tayi, Ahyan ta

kanka zan fara, kasani tun lokacin da yar‟uwa ta take raye muka yi

al‟k‟awarin zamu had‟a ya‟yanmu Aure, ina son in cika wannan burinmu,

kuma bin umarni na sh‟i zai sa na yafe maka abunda kayi min, don haka

na yanke hukunci had‟aka aure da yar‟uwan ka Kausar har na sanar da

yan Sokoto. Ba shawara nake baka ba umarni na baka, ta kai dubanta ga

70 WHATSAPP 08105882006

Page 71: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Ammar ta kira sunansa, ya amsa jiki ba kw‟ari,tace”Ammar kaima ina ga

zaka auri Zainab don tafi sabawa da kai ta sh‟ak‟u da kai sosai, Ammar a

cikin zuciyansa yafurta Alhamdulilah!.a fili kuma sunkuyar da kansa yayi

yace to Mum Allah yasa hakan shine mafi al‟kairi!, Ta amsa da ameen.

Tace”don haka kuje ku fara sh‟iri wata sati ne d‟aurin Aure da tarewa.

Sannan bace sai kunyi kayan karya ba a‟a mu al‟kairin abu mukeso suka

amsa da to sh‟ikenan ku tash‟i kuje Allah ya muku albarka ameen. Amm

Ammar ina so ka zo min da Auta da kayanta zata dawo gdn nan harsai

anyi biki sai ka d‟auketa to ya amsa suka fita. Ammar na isa gida wata

zuciya tace karkayi sauri sanarda Auta kai zata Aura halama bata s onka

kawai ka gwadata ka gani. Da sallama ya sh‟iga gidan amam ya d‟aure

fuska Auta da fara ta masa sannu da zuwa, ganin yanayin sa ya sa

tace”Yaya na mai ya sameka? Kona maka laifi ne? Kai ya gir-giza mata

alamar a‟a to mai yasame ka? Dan Allah ka sanar min. Cikin al‟hini ya

soma yimata bayani kam hahiya zata hadasu Aure kuma wata sati duk

Auta ta k‟agu taji da waye yace ni da Kausar da ke da Ahyan what?? Tace

“ina sam bazaiyuba ni wlh bana sonsh‟i. Ina da wanda nake so, cikin

damuwa Ammar yace” wa kike so?.shiru tayi tana kallonsa don bata san

lokacin da ta furta maganan ba, Ammar yayita bata kalamai akan ta d‟au

k‟addara da abunda Allah ya zab‟a mata, Auta kam kuka ta somayi mara

sauti, daren ranan bata rintsa ba. Da safe kuwa idonta duk ya kumbura

Ammar na ganin ta sai duk ta bashi tausayi kamar zai fad‟a mata ko zata

samu sauki, don yana hango tsagw‟aron Sinsa acikin kw‟ayar idinta amma

ya share. Yace”Auta ki sh‟irya zuwa dare ina dawo zan kaiki, cikin fush‟i

tace”ni ba inda zanje kai naga alamr ma baka damuba daman baka damu

dani ba, kuka ta saki mai tsuma zuciya har k‟asan zuciyansa yake jun

kukanta, fita kawai yayi a d‟akin don bazai iya saura-ronta ba. Yinin ranan

bata ci abimci mai ky‟au ba sai da azahar ta samu bacci ya d‟auketa ko da

ta tash‟i bayan la‟asar idonta ya washe wanka tayi takiyin kw‟aliya tace”ni

ba ida zani daman son da Ammar ke min bana gsky bane, hmm ko

ajikinsa bai damuba mts ni haushin Kausar din ma na fara ji. Ni rash

nace”kw‟aji min Autan nan harta na da bakun iya fush‟i Ammar kuma fa

da ya ganta da saurayi yayi yaya?. Da yamma da Ammar ya dawo sunsha

71 WHATSAPP 08105882006

Page 72: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

rikici don fir tace ita ba inda zata je, sai data ga ya bata rai kafin ta fito

tana kuka ta dan debi kayanta kad‟an suka tafi. A gd basu same su ba don

sun fita sayayya tana zuwa dakinta ta wuce, sai magriba suka dawo ganin

karsu fahimci halin da take ciki yaa ta d‟an biye damuwarta ta sake

kad‟an, sukayi hira har zuwa 8:40 Mum ta haura sama Munay ma haka

Kausar da Auta kad‟ai a falo. Ammar ya sh‟igo zai musu sallama ya wuce

yatarab ba Mum ya musu sai da safe ya fita. Biyo sa tayi da ta sha

gabansa kasancewar ida suke ba haske kafin ka isa harabar gdn ne, kuma

tasoma masa tace”ni wlh bana son auren inada wanda nake so kuma

shiya yace yana sona ai, ganin Ammar yayi sh‟iru baice mata komai ba

tasa ta fada jikinsa ta sake kuka nan take Ammar taji lbr yasoma sauyawa,

kara rungume Auta yayi yace”Zainab sai da taji sunan har cikin

kw”anyanta, bata iya amsawa ba sai binsa da tayi da ido yace wa kike

so?, jin tambayar tayi tazomata a BAZATA, shi ru tayi ta kafe sa da ido

ganin yanayin da take kuma ya fahimci sh‟itake so, sai yamata dabara

sunanta yasake kira akaro na biyu kasa amsawa tayi yace”Zainab kina

Sona?.da sauri ta daga kai alamar eh! Lallausar murmushi ya saki ya kara

rungumeta fuskansa ya duko zuwa dai-dai kunne ta yace Zainab nine

mijin da zaki aura, nayi hakane don in ga kina qauna ko ba ky‟a qauna ta.

Dukan wasa ta kai masa a kirji yace”wash ashh kika dake sai na rama zata

gudu ya cabkota ya kara mannata da jukinsa tana kiciniyar kw‟acewa ta

kasa sai da ya bata lafiyayan kiss tukun ya saketa don kar ya wuce gona

da iri. Da gudu tayi cikin gd tana yar dariya. H Mamu ta sanar da kausar

ita ma ba a samu matsala da ita ba. Don haka suka ci gaba da sh‟iri.

Ammar akw‟ati Uku da kit ya yi ma auta bai wani yi kayan karya ba turmi

ish‟irin ya mata sai English wears da ya samata. Ban garen Ahyan shima

turmi talatin yayi da akw‟ati hud‟u da kit komai sai son barka a talakance

ba karya aciki. H Mamu ta had‟a yan Amareta tana ta tsumasu su Munay

sai shirin biki akeyi. Ammar gida ya kama musu plat su kadai ba mai

tsadan daga hankaliba 80k ya samu. Ya sh‟irya shida Auwal sukaje

k‟auyen su Malam ya sanar musu da Inna laure yace”Malam ina son

kazama waliyin Auren mu, yaji dad‟i sosai basu bar kauyen ba sai tare da

su Malam gd da suke ya kaisu d‟aki Auta. Amare liyafa suka sh‟irya sai

72 WHATSAPP 08105882006

Page 73: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

angwaye da suka sh‟irya Dinner. Yau take laraba duk gidan acike yake da

yan biki yan sokoto sun zo, Amare ko Mum ta hana su fita anata gyara su

Ammar da Ahyan sun had‟a kai tare suke komai da Auwal Munay ko da

Auwal tunda aka fara hidimar biki naga abunsu sai a slow. Yau Al‟hamis

takama yau za‟ayi liyafa Mum ne ta kawo musu wani sari mai ky‟au sosai,

masu kw‟aliya suka gyara Amare lokacin da suka fito gun liyafar dake

acikin gd za‟ayi hmmm masu karatu lokacin da suka fito karkuso ku gansu

ohoho abun bacewa komai don sun sha ky‟au kamar ba gibe, liyafa akayi

na gani na fada malama Khadija da Malam Juwairiya suka gabatar da

nasiha game da rayuwan aure. Bayan an tash‟i a gunne sukanufo gida

suna d‟aki munay ke zi-zita irin ky‟an da sukayi tace”Allah yasa wankar

Dinner tafi na yau murmushi sukayi dukansu gabaki d‟aya. Ran jumma‟ah

tun da safe suke aiki dafa abinci yan d‟aurin Aure sai da suka kammala

komai H Mamu tazo tasa Amare sukayi wanka cikin atafa sun sha turare

had‟in yar mai duguri, bayan Sallah Jumma‟ah aka saida Aure Ahyan da

Kausar, Ammar da Zainab daga guri yan d‟aurin aure suka wuce zaranda

holel don gudanar da walima. Da dad‟dare Amare sunsha ky‟au cikin

gown kowacce kala d‟aya da angonta Ammar yasha shadda fari da ratsin

marun yayinda Auta tasha gown fari da ratsin maroon colour aciki ta sha

make-up sosai tayi ky‟au. Ahyan kuma daga nesa na hango shi da farin

shadda yasha aiki da zare blue colour, Kausar ma gown ta sha fari da

ratsin blue colour bakaramin ky‟au tayi ba. Mutar d‟aukan ya biki ne ta

tsaya duk suka debi wayanda suka dace, Munay da Auwal ya d‟auketa a

motarsa yayinda aka tafi da Kausar da Ahyan a motar abokinsa, sai da aka

gama kw‟ashe su kafi naga wata k‟atuwar Jeep baka mai bak‟ak‟en glass

perker ba a dad‟e ba naga wata mata tafito da Auta tun daga nesa take

zuba ky‟ali. Ammar kam sake baki yakeyi yana kallonta baita ba d‟aukar

ky‟an Auta ya kai haka ba, bud‟e murfin motar aka sata aciki, sai da ta

zauna tukum taji k‟amshin da tasaba ji, da sauri ta kalli gefenta Ammar ta

gani yana mata murmushi. Lokacin aka jasu a motar hannusa ya sanya

cikin nata yafara murzawa dake cikin motar ba haske matsowa yayi kusa

da ita ya janyo ta jikinsa ya sanya haske wayarsa ya na haska fuskanta sai

da yagama kalon fuskanta ya gan-garo zuwa bakinta da ya sha jan baki a

73 WHATSAPP 08105882006

Page 74: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

gankali ya soma. Oh!! Na gaji masu karatu sai zuwa page d‟in gaba zaku

jini. Taku a kulum mai k‟aunar ku Rash Kardam [8:01PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Wayar sa ya haska ta

da ita tayi ky‟au kamar ba Auta da ya sani ba, a hankali ya soma bin

fuskan da kalo har yazo dan k‟aramin bakin ta da yasha janbaki maroon,

idonta ya haska yaga ta lumshe su wani kyau na musamman ta kara masa

a hakan, take yaji wani farin ciki ya lulubesa yau Autarsa ta dawo

mallakinsa YAR‟AMANA sa, a zuciyara yace”ina ma da su dad suna yare

suga wannan rana nasan zasu fi kowa farinciki. Ya Allah kajikansu kamusu

Rahma Ameen. Kashe wayar yayi ya kara matso da fuskansa har Auta na

jiyo numfash‟insa, nan take yasoma jin wani abu na tsirga masa, bakinsa

yasa cikin nata yafara mata wasu salon, dai-dai lokacin suka iso, a hankali

ya matsa gefe jiki ba kw‟ari. Duk yan dinner sun shuga su Ammar kadai

ake jira, sai da su Ammar suka d‟au lokaci kafin suka fito Ahyan na rike da

hannu Kausar gsky sunyi ky‟au. Ammar yace”amana afuwa mun bata

muku lokaci. Murmush‟i Ahyan yayi yace “mush‟iga kawai don lokaci na

kara tafiya. Ahayan da Kausar sune a gaba sai Ammar da Zainab, tunda

suka saka kafa acikin hall d‟in na saki baki ina k‟alon Amaren nan, gsky

Allah yayi halita a gun baran na bayannan wato Ammar da Auta. Amrah

ce ta zungureni kai Rash wannan wani irin kalo ne kamar zaki cimyesu,

hmmm nace”My Amrah ke dai bari kawai Amaren ne sun tafi dani sun

had‟u sosai gsky sun dace da junansu. High table din nake bi da kallo

gefen Ammar Auwal ne da Munay sai kujeran kusa da su Jidda da

Ghali(Haughal) na gani, ko da na kali gefen Kausar Raheenat da MY na

gano sai wata kawar kausar da saurayinta. Kid‟a ne ke tashi a gun ko ina

ka duba jama‟a ne suke zaune kowa da masoyinsa ga Mrs Umar ma da

Sojanta sai luv suke sha. „Daya daga cikin abokan Angwaye ya bud‟e taro

da addu‟a, kafin aka soma gudanar ta dinner sai da suka danci abun

motsa baki, aka umurci Amarya Kausar da Angonta suka fara sauka kid‟a

aka sake musu nan fa yan liki suka taso bayan sun taka ne, aka umurci

Zainab da Ammar su fito, tunda aka kira sunasu Auta ta lafe ajikin Ammar

bata son sauk‟a, Ammar ya janyota jikinsa kai ka dauka wani zai kw‟aceta

ita ko ta lafe ajikinsa, cikim nutsuwa suke sauk‟owa abun gwanin

74 WHATSAPP 08105882006

Page 75: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

burgewa ohoho masu karatu naso ace kunje gun dinner nan don duk lbr

da zan baku na Ammar da Auta zai d‟auke mu lokaci mai tsawo. Waka aka

sake musu kan kace me yan likin Ammar da Auta sum taso suka fara

musu har suka zo tsakiyar hall din, a hankali Ammar ke ta kawa amma

Auta taki rawa ganin haka yasa ya kara matsowa kusa da ita ya mata

cakulkuli aiko ta kw‟ato jikinsa nan yafara ju-juya ta, in ka gansu kw‟a

d‟auka salon soyyansu suke zubawa. Haka tarin dinner ta kare cike da

farin ciki suka dawo gida, kyar Ammar ya bar Zee tash‟iga gd. Taku a

kullum mai k‟aunar ku Rash Kardam [8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Hajiya Mamu taso akai amare

yau Amma dare yayi, haka ta hakura. Da safe bayan sun karya ta zo d‟akin

Amaren da kayan fruit ta basu da wani abu kowacce cikin kofi d‟aya, ni

Rash nace “ko miye wannan oho!?. Haka suka yini Mum sai d‟irka musu

abubuwa takeyi tun daya yamma ta hada su a daki d ‟aya ta soma musu

nasiha gami da basu sirrikan saye zuciyar miji. Da dad‟dare aka zo

d‟aukan Amare sunsha kuka kam da ky‟ar aka fita dasu, kowacce akayi

kaita gidanta. Abokan Ahyan ne suka raka sh‟i saida suka dan tsokani

Amarya, da yan barkw‟acin su kafinsuka masu sallama da fatan samun

zuri‟a na gari suka tafi, nima fatan alkairi namusu nafito tare da jan musu

gate d‟in gdn. Na nufi gidansu Auta don inga wainar da ake toyawa ta. Ina

isa na tarar da Auwal ne da Saeed suka rakash‟i, nasiha sosai suka musu

da yan shawarwari kafin suka musu sallama suka fito, Ammar ya musu

rakiya bai wani dad‟e ba ya dawo gefen Auta ya Auna tare da furta

Alhamdulila!. Agogon dake hannusa ya cire yace Zainab kije kiyi alwala

muyi nafila mu gode ma Allah da wannan babban ni‟imadaya mana.

Mikewa tayi ta nufi toilet ta d‟aro alwala bata dad‟e da fitowa ba shima

ya fito suka suka tada kabbara. Raka‟a 2sukayi kafin ya dafa kanta

yasoma karanto addu‟ar da in mutum yayi Amarya ko sabon abu zaiyi

kafin yafara amfani da abun. Ga addu‟ar kamar haka”Allahummah inni

as‟aluka khairi ha wa khaira ma jabaltaha alai, wa „a‟ uzubika min sharri

ha wa sharri majabalta ha alai”. Ma‟anarsa sh‟ine Ya Allah ina rokonka

Alkairinta da d‟abi‟anta akansa, kuma ina neman tsari da sharrinta da

sharrin da ka d‟abi‟antar ta akansa.( yan‟uwa yana da kyau mu runka

75 WHATSAPP 08105882006

Page 76: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

yawaita yin wannan addu‟a yayin da mukayi sabon abu, Addu‟ar tana da

matuakan amfani, Allah yasa mudace Ameen). Sai da ya gama karantawa

tana amsawa da Ameen har ya kai karshe, kitchen yaje ya d‟auko musu

plate ya saka musu kazan da fresh milk mai sanyi yasa musu a kofi, Auta

ta kasa sakin jikinta da sh‟i, naman ya d‟auko yazo dai-dai bakin ta ta

kawar da fuska tana yar murmushi kasa-kasa, cikin zolaya ya dawo ta

gefen da ta mayar fa fuskanta cike da tsokana yace” Amarya yau kunyata

kike ji?. Uhmm ta fada tare da sake mayar da guskanta ta d‟aya barin

mikewa yayi cikin shauk‟in so da kauna yace”baringa ta ina zamu fara, ita

ko sai zi-zilewa takeyi. Rash Kardam [8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Haka sukayi ta hiransu cikin

barkw‟anci, Ammar ne ya mik‟e ya yace barin watsa ruwa d‟akinsa ya

nufa, Auta ma ta mike taje tayi wanka mai ta shafa sai man baki ta

kw‟anta ta lumshe idonta tamkar mai bacci, Ammar ya sh‟igo cikin sh‟irin

kwanciya yayi ky‟au, ya tsaya k‟are ma Auta kallo tayi ky‟au cikin kayan

baccin, wani lalalusan murmushi ya saki ya kashe musu wuta. Ni Rash

nace”oh! Wanan mirmush‟in kam yau na sam Auta sai ta gane kurenta

agun Ammar, bare mai nema ya samu. Da safe na leka gidan Zee Auta na

tarar tayi wanka Ammar ma ya shirya cikin sh‟iga mai ky‟au, yazo dab da

ita yace my swt muje mu yi breakfast, cikin shagwaba tace” ni ni sai tayi

sh‟iru, bai tsaya kara sauraronta ba d‟auketa kamar wata baby sai dinning

ya direta abaki ya rinka bata abinci har sai da ya tabbatar ta kosh‟i tukun

ya ky‟aleta sh‟ima ya karya. Ammar da Zee soyayya suke gudanarwa mai

tsabta, basa son ganin d‟ayansu cikin damuwa komai tare sukeyi in

Ammar na gd. Kw‟aki sun ja, watani sun tafi, shekaru dayawa sun shud‟e,

wani make-ken gida na hango wanda ya tafi da hankali na, ina tsaye ina

kale-kale na hango wata mota k‟iran Toyota Camry 2016 blue colour, ta

sh‟iga wannan gidan, da sauri na da gudu yanda komai gadi ba zai iya

rik‟eni ba bare ya hanani sh‟iga gd, cikin flowers na lab‟e, motar ne ta

karasa sh‟igowa ina kallo tayi parking a wajen ajiye mota, duk na kagu in

ga wacece zata fito ta dad‟e kafin ta bud‟e k‟ofar motar, k‟afarta ta fara

sauko da su Yasalam na furta, masu karatu sai kunga kafar tamk ar na Zee

hrt tsaban kyau…lol… A hankali ta k‟arasa fitowa sai naga wasu yara su

76 WHATSAPP 08105882006

Page 77: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

biyu mata sun fito d‟ayar zata kai 10 yrs karamar kuma zata kai 7yrs yaran

sun had‟u kama, mai gadi ne ya musu sannu da dawowa ta amsa da sakin

fuska, ta nufi cikin gd. Zarah ce tayi nufi stairs tana kw‟ala kira ma nanny

su k‟ira, khairat kuwa dake suka zube a falo ita da Mum d‟inta. Wani

had‟ad‟en guy fa ba zai wuce 40yrs ba ya sauko rike da hannun wani yaro

kamar su d‟aya da sh‟i sai a lokacin na gane ko suwaye AMMAR da ZEE

AUATA da yaransu, duk ta canza ta k‟ara ky‟au ta da girma. Yazo kusa da

ita ya zauna yace”Madam kin dawo ya hanya? Alhamdulilah! Ya kalleta

kafin yace “My Luv ina son yau zanje na taho da su Malam da Inna, don

an gama gyara gidan ansa komai aciki, cikin jin dad‟i tace” Abban zarah ka

ky‟auta Allah ya kara bud‟i Ameen, Zainab Malam sun can-canci haka don

sun mana abunda bazamu manta ba, tace” hakane kam ALKAIRI DANKO

NE book by Ummu Aisha, Baya tab‟a fad‟uwa kasa bamza. A ranar ya je

ya taho dasu Malam da Inna gd ya musu mai ky‟au sunyi murna sosai.

Taku a kullum mai k‟aunar ku. Rash Kardam [8:02PM, 9/20/2016] Rash

Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Alhaji Ammar Sa‟ad

Saraki ya dawo hamshakin d‟an kasuwa mai cike da naira ya sanu ciki da

wajen kasannan, yana da company a yawancin State d‟in dake 9ja. Jerin

gwanon motoci na hango sunyi com boys abun gwanin burgewa number

motar kuwa duk iri d‟aya ne ansa A S Saraki1 har zuwa 10 ya nufi gdn sa,

ko da ya shiga matarsa ceta taso cikin shiga ta alfarma ta y i welcoming

d‟insa, sai da ya huta yaci abinci ya kaleta yace Madam kinyi ky‟au kuma

kulum kara ky‟au kikeyi, cikin salon da ta saba rikita sh‟i ta juya ido

tace”kaima haka sh‟iyasa kulum nake k‟ara sonka. A natse ya kalleta

yace”Zainab ku shirya ke da yara tunda suna hutu nagama yi mana

booking din jirgi ran friday zamu kaduna. Da sauri tazo ta run gumesa ko

mai ta tuna sai tafara zubar da hawaye janyota yayi jikinsa yasoma

lalash‟inta yace”nasan me kike ma kuka ki share hawayenki yanzu ne

lokacin da zamu dau fansa. A yanzu dum wani moving din Baba Sani ina

da lbr akansa kuma Baba Isya ya rasu a razane ta d‟ago amma tuna

abunda sukayi ma iyayenta cikim kasa-kasa da murya tace”to yau ina

Baba Isiya yake gash‟i ya tara da su Dad, rayuwa ke nan duniya ba gurin

matabbata ba ne. Tun ran Alhamis suka je gidan H Mamu suka mata

77 WHATSAPP 08105882006

Page 78: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

sallama tare da musu fatan nasara daga gidan kuma suka nufi gidansu

Malam suma Addu‟a suka musu. Ran friday tun karfe 1:00pm aka kaisu

Airport basu dad‟e ba jirginsu ya d‟aga sai KD, 1hrs ya kaisu cikin garin

KD, wani katafaren gd da Ammar ya gina acikin garin kaduna suka sauk‟a,

garin duk ya fawo ma Auta wani iri basu fita ko ina ba sai washe gari suka

sh‟irya cikin sh‟iga ta alfarma da yan yarasu uku Zarah ce baba sai mai bi

mata Kairat sai Al-hasan mai sunan Dad suna kiransa da junior, yaran

ky‟awawa da su gwanin burgewa. Motocin Ammar ne suka jero zuwa

k‟ofar gdn. Ammar rik‟e da hannu junior sai Auta rik‟e da hannu Kairat

suka sh‟iga mota suka nufi Hayin Rigasa. Taku a kulum mai k‟aunar ku

Rash Kardam [8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By

©Rasheedah .A. Kardam Motoci ne a jere suka sh‟iga layin duk jama‟ar

dake unguwan sai lek‟e sukeyi don basu taba ganin motoci sun jero irin

haka ba, wasu kamma cewa suke yau gwamna ya zo umguwansu, dai-dai

k‟ofar gidan su Auta motar ta perker body gurad d‟insa ne suka fito sai da

suka rarrabu a gun kafin aka bude ma Ammar k‟ofar motan ya fito,

zagawa yayi ya bud‟e ma Zee sai yara suka fito daga motarsu, duk yan

gurin ba wanda ya shaidasu sai dai sunga ansa AS Saraki a jikin motar

kuma suna jin lbrsa. Baba sani dake sh‟irin fitowa yaga mota a k‟ofar gd

sa tabbas yana jin lbr AS Saraki k‟odai mafarki yakeyi ne kam ya san ba

abunda zai kawosa gidan. Ammar ya mika masa hannu suka gaisa yace ka

sai dani kuwa Baba Sani da yayi mutuwar tsaye yace”Eh! A S Saraki da

nake jin lbrsa ne ko? Ammar yayi murmushin kasaita yace”kw‟arai kuwa

nine, mush‟iga daga ciki falo su Auta aka sh‟iga da su sai da aka kawo

musu kayan shaye-shaye sam Baba Sani bai ganesu ba, sabida shekaru

sun tafi da yawa ga naira ya zauna musu, Ammar ganin bai ganesa ba

yace wata kasuwanci ne nake so muyi da kai, na samu lbrka gurin wani

yaron ka mai suna Gumus, ya yaba da kai sh‟iyasa naji ka kwantamin a rai

da mu had‟a business, sun d‟anyi hira kafin yamasa sallama ya rako su har

bakin mota saida suka sh‟iga ya kima gd cike da murna tabbas tsun-tsu

daga sama gashashe, nikam Rash nace”wato mai hali baya fasa halinsa a

ko ina yake”. Sun d‟ansoma tafiya kenan sai ga motar Futha ya danno kai

dake glass gin ta fari ne Ammar yasa aka dakatar da ita sam Auta bata

78 WHATSAPP 08105882006

Page 79: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

lura da itaba sai da yace mata”Sweet kali can aiko ta kalo futa zata fita da

gudu ya riketa yace zaki wargaza mana plan d‟in mu Short note yayi ya

bama body gurad d‟inda ya bata, ko da ta karanta ta bud‟e murfin mota

da sauri ta fito Ammar ya rage glass d‟in motar sa tabbas sune ba gizo

suke mata ba. Ammar yace kin gane a kw‟ai Adress din mu so kizo ki

same mu anan plan d‟in mu zai iya wargajewa ok! Motar ta takoma cike

da murna tana gode ma Allah da ya bayya na mata su Zee dinta Da

yamma Barrister Futha ta nufi gd su Ammar ko da taje sunyi murna ita da

Zee sannan suka bama juna lbr bayan rabo Futha cikin mamaki tace”no

wonder biri yayi kama da mutum dom na dad‟e ina zarginsa kam nan ta

ce bari na sanar da Sadiya don baza a rasa wani evidence a gunta ba,

ringing biyi yayi ta d‟auka sun gaisa futha ta bata lbr komai cikin murna

tace”Futha suna ina nan ta bata Address d‟in gidan bata dad‟e bakuwa ta

iso sun gaisa itama aka bata lbr taci kuka jin Babanta ke da hannu kuma

ta d‟au alwansh‟i basu goyon baya don a kamash‟i, Futha tace”yau

weekend ne bazaiyu ayi karansa ba amma zuwa Monday sai ayi yanzu dai

Ammar duk abun zai zama a hannuka ne duk yanda za‟ayi kar kabari ya

bar gari ko ya ganeka ok! Haka suka watse. Yau monday duk wani

ma‟aikaci ya fita aiki, yau ne su Ammar suka kai karan Baba Sani, police

har gd sa suka je aka kamasa C.I.D aka kaisa, ba irin wahalar da ba‟a masa

ba ama fir yak‟i fad‟ar gsky harranan sh‟iga kotu, kowa ya hallara a koto,

mai gabatar da kara ya tashi ya koro bayani ba alkali, barrister Futha ta

fito ta gaida alkali kafin ta soma yan tambayoyi ma Baba Sani amma fir

yak‟i yarda da sh‟i yayi, rashin wata kw‟akw‟aran shaida aka d‟aga karan

har sai 5/3/2016 haka aka watse amma kotu ta hana belin Baba Sani har

sai ansamu gsky. Taku a kullum mai k‟aunar ku Rash Kardam [8:02PM,

9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Yau

takama ranar da za‟a koma kotu,tun da wuri su Futha suka hallara don su

had‟a shaidar da Ammar yace ya samu amma shiru bash‟i ba lbr sa, sai

dab da za‟a sh‟iga ya k‟araso gunsu jiki ba kw‟ari ya iso Futha cikin

damuwa ta ce”ya dai ina fatan ansamu nasara. Ammar yace”wa yanda

zasu taho da su gumus da Duna da su baba mai gadi na kira wayarsu a

kashekuma bawani lbr, wani iska mai zafi ta furzar tace”ga Sady sh‟iru

79 WHATSAPP 08105882006

Page 80: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

itama bata iso ba, dai-dai lokacin aka sh‟iga kotu mai gabatar da kara ya

karanto kara da akeyi, lauyan mai kara ta fito bayan ta gabatar da sunan

ta ta zauna, lauyan mai kariya sh‟ima ya gabatar da sunansa, nan aka

nemi mai kara ta gabatar da shai du, sh‟i alkali ya ce”rash‟in wata

gamsash‟iyar shaida kotu zata… Bai karaba Sady tash‟igo cikin hanzari

tace ranka sh‟idade akw‟ai shaida a tare da ni, gabad‟aya aka juya ana

kalonta, a hankali ta zo gaban mutane d‟auke da wata envelope ta mika

wa Alkali ta sake bash‟i wasu kaya tace”ranka sh‟i dad‟e ni d‟iyar wacce

ake kara ne, sanan bin ciken danayi, na samo wad‟anan kayan da su akayi

amfani gurin kashe Alhaji Al-hassan da Matarsa sanan hatta bindigar da

akayi kisar akw‟ai sanna akw‟ai ta kardan da sukayi tsakani mahaifina da

Marigayi Baba Isiya akan zasu raba dukiyar Mahaifin Auta. Wayar Ammar

ne yayi k‟ara yana dubawa yaga number Kabir ne da sauri ya d‟agawa

yace kana ina? “Gani a k‟ofar kotu muna tare da su gaba d‟aya, right! Sai

da ya nimi permission ya sai dama Futha ga sunan azo dasu, batare da

bata likaci ba ta sanar da alkali ga wasu saidan ma an taho dasu, nan ta

bukaci a had‟a ta da police suka fita aka sh‟igo dasu, Baba sani ya cika da

tsanani mamakin gani su Gumus Da Duna da Masu aikin gdn, nan aka

gatar da su, alkali ya ce”bisa ga kw‟araran shaidar da aka samu na Sani da

laifin kashe d‟anuwansa da Matarsa, kotu ta yanke masa hukun d‟aurin

rai da rai, alkali ya mike kafin sauran mutane suka fito, Auta rungume

Sady tayi tana kuka irin wanna jahadin da tayi, suna fitowa daga kotu

gidansu Futha suka nufa sai da suka ci abinci tukun Auta suka koma gdsu.

Auta bata bar garin kaduna ba saida ta raba ma Matar Baba isiya da Su

Sady sauran duk‟iyarta ta mallaka musu don su samu abun rayuwa, cike

da farin ciki suka dawo Bauchi Ammar ya kalli Auta yace”Alhamdulilah!

Yau na sauke nauyi da nayi ma kaina alkawari shekara da shekaru. Taku a

kullum mai k‟aunar ku Rash Kardam [8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:

AMANA TA CE By ©Rasheedah .A. Kardam Zaune suke a falo Zee Auta sai

zuba shagwaba take wa Ammar ko sai biye mata yakeyi, junior ne ya biyo

Khaira ta d‟aukar masa yar babynsa da gudu, suka sauko falo, ya kasa

kamata sai yaje gun Ammar da yar kukan shagwaba yace”Dad kaga

Khairat ta d‟aukan YAR AMANA TA Ammar yayi dariya kafin ya karbi

80 WHATSAPP 08105882006

Page 81: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Teddy ya basa, yace” kema zan sanyo miki naki, da murna tace” thanks u

My Sweet Dad luv u too, junior ya kalli Ammar yace” Dad kaifa ina YAR

AMAN KA?. Cike da fara‟a ya nuno musu Mummy su, da gudu suka haura

sama, sh‟ikuma yazo ya d‟auki Auta kamar yarinya yana ju-juyata yace”

ina kara sonki ko da yaushe yarinya kike k‟ara dawowa, kw‟ayar idonta ya

kalla yace” sh‟iya sa nake kara tattala AMANA TA CE. Alhamdulilah!!

Tsarki da mulki iko su tabbata ga Ubangijin Talikai, Ina mika godia ta ga

Allah(S.W.T.A) da yabani damar na kawo k‟arshen littafina mai sunan

AMANA TA CE. Yan‟uwa ina fatan zaku d‟au darasin da ke cikin wannan

littafin, ko da yaushe mukasance masu kula da zumunci, ha disi ne guda

ankarbo daga (musulum ya karbo daga manzon Allah tsira da aminci Allah

su tabbata a garesh‟i yace”la yadakulul jannati khad‟i‟u rahimi, mai yanke

zumunta bazai shiga Aljannah ba” ya Yan‟uwa kusani Zumunci da Amana

suna gefen siradi duk wanda ya yanke daya acikinsu kugiyace zata jash‟i

zuwa wuta). Sanna kuma duk wanda yayi riko da Zumunci da Amana to

zaiga sakamako mai ky‟au, yana da ky‟au muna tarayya da mutanen

kw‟arai sanna nu neman tsari da shaid‟an don harda sh‟i yake in gizamu

zuwa aikata ba dai-dai ba. Gareku mata masu zuwa gurin boka ko Malam

tsubbu hakan baida amfani sai tarin zunubi, ku sani duk wanda yaje gun

boka Allah bazai karbi Sallah sa ba na kw‟ana 40 sanan Mala‟iku suna

tsine mata, Ya Allah kasa mu fi k‟arfin zuciyan mu Ameen. IYAYENA ABIN

ALFARINA Iyayena abun alfarina jin-jina da godia ta musamman gareku

Alhaji Abdullahi Garba Kardam da Hajiya Khadija Aliyu Abdullahi.

SADAUKARWA na sadaukar da wannan littafin gareku Zainab Al -

hassan(Autar Hajiya) Maryam Alkali(Mermu) Kausar Luv Zee hrt

Nucceyluff Bilkisu Sildibe(Futha) Fatima(Falmi) Fulani Cerdiya Munay

Sadiya A Dahiru Maman Abideen K‟AWAYE NA KUNA RAINA Aunty

Zainab,Dijah Tahir,Afrah Luu, Queen Memie,Hauwa A

Shehu(jiddah),Maman Safwan,Nana Fiddausu, Indiana Fidy, Maman

Khairat, Maman Abideen,Amrah,Mrs Ak,Myer, Najaat,Haugal,Cutie, Swt

Fauxie,Zeenur, Xarah BB,Bebaloo, Zahra,Maman Fawaz,Nana Dizo, Hasna

Idris. Da duk sauran wanda ban samu rubuto sunansu ba. KUNFI KOWA

SON LITTAFINA Mrs Abdul, Farhat B Haske, Aliyu Haiydar Hajiya J amila,

81 WHATSAPP 08105882006

Page 82: amana ta ce - ArewaFlex

AMANATCE WWW.AREWAFLEX.COM

Khadijat Khadijat, Bilkisu lame, Rahma S Musa, da sauran wanda ban

samu damar jero suba. GODIYA MAI TARIN YAWA GA YAN GROUPS DINa

ZAUJIN NUHR RASHKARDAM HAUSA NOVELS 1&2 MURMUE HOME OF

NOVELS EXTREME HAUSA WRITTERS WISDOM HAUSA WRITER‟S BEST

HAUSA WRITERSGROUP DUNIYAR LITTAFIN HAUSA HAUSA NOVEL

GROUPS KHALEESAT HAIYDAR NOVEL GROUP FB. Godiya ta musamman

ga masoyan littafina, sai mun had‟u a sabon littafina. Taku a kullum mai

k‟aunar ku.

DAN SAMUN COMPLETE HAUSA NOVELS PDF, TXT,ONLINE & AUDIO VISIT

WWW.AREWAFLEX.COM

82

WHATSAPP 08105882006