AHLUL SUNNAH WAL JAMA’A SASHENSU BAYA KAFURTA SASHE
AHLUL SUNNAH WAL JAMA’A SASHENSU BAYA
KAFURTA SASHE
Ado Garba Abubakar
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
GABATARWA
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin
qai. Allah ka yi daxin tsira ga fiyayyen
halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da
alayensa da sahabbansa da duk
waxanda suka yi biyayya ga tafarkinsa
har yazuwa ranar sakamako.
Ina neman gafarar Ubangiji tare da
jagora wajen gabatar da wannan
taqaitaccen littafi, domin faxakar da
al’umar Musulmi akan tausayawa juna
wajen yanke hukunci ga juna, saboda
savanin fahimta. A yau a wannan qasa
mun wayi gari ‘yan’uwa waxanda suke
uwa xaya uba xaya suna kafurta juna:
Vangare guda na zargin ‘yan’uwansu
akan kuskure bisa ‘Qin Annabi
2
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
(S.A.W)’, xaya vangare na zargin
‘yan’uwansu
bisa kuskure da yin ‘Shirka’.
Subhanallah. .
Shin me ya yi zafi haka? Ga fahimtar
marubucin, abu biyu zuwa uku ya jawo
haka. Na farko, son rai, na biyu, jahilci,
na uku, rashin bin diddigin mas’saloli a
cikin kwanciyar hankali har akai
qarshen su domin kyakkyawar
fahimta.
Ina roqon Allah ya haxa mana
kawunanmu, ya kori shaixan daga
tsakaninmu, ya kuma jiqan mahaifana,
Hajiya Aminatu da Alhaji Abubakar da
gafara tare da dukkan al’umar Annabi
(S.A.W).
3
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Ado G. Abubakar 16 Muharram, 1431H, Abuja Nigeria
4
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
BABI NA FARKO
Su wane ne Ahlul Sunnah Wal Jama’ah
Malam Abdul kahir Al Bagdadi acikin Al
farku bainal firak yace: Ahlul Sunnah
Wal Jama’ah su ne; al’umar Musulmi
waxanda suka yi Imani da Allah da
Manzo Muhammad (S.A.W).Sun yi
Itifaqi a bisa halifancin Sahabbansa,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu
(RA). Su Ahlul Sunnah Wal Jama’ah
suna girmama dukkan sahabban
Annabi (S.A.W) da matayensa da Ahlul
Bait. Sun yadda da halifancin Xalha da
Zubair (RA) sa’annan basa sukar ko
xaya daga cikin sahabban Annabi
(S.A.W), akan abinda ya afku tsakanin
Mu’awiyya da Aliyu (RA) da ire-iren
5
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
waxannan al’amura, su masu
kewayewa ne, kuma masu kame
bakinsu a kan haka.
Dukkan xaukakin jama’ar Imamu
Malik, Imamu Shafi’i, Imamul
Auza’i, Imamu Sariyu, Imamu Abu
Hanifa, Imam Abi Laila, Abu Sauri,
da al’umar Imam Ahmad bin
Hanbal, da Ahlin Ahmad Zahir da
mutanen Imamu Shazali da sauran
al’umar faqihai waxanda basu bi
tafarkin vata ba (kamar na murji’a
Khawarijawa, Mu’utazilawa, da
Qadarawa).
Daga cikin Ahlul Sannah Wal Jama’ah
akwai salafawa, ko al’umar
Muhammad Ibn Abdul Wahab, akwai
Mujahidai, akwai kuma sufaye. Babu ja
6
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
duk waxanda muka ambata da ire –
iren su Musulmi ne ‘yan uwan juna.
Xaukakin Ahlul Sunnah wal Jama’ah
sun yi Imani zamu qetara siraxi kuma
zamu ga Allah ta’ala ranar Lahira.
7
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Nau’o’in Ahlul Sunnah Wal
Jama’ah
i. Mallam Abdul kahir yaci gaba
da cewa:
Akwai waxanda suka himmatu
wajen sanin Allah da kaxaita
shi, da sanin Annabi da bin
Sunnarsa, da hukunce-hukuncen
shari’a da sanin cewa Allah yana
sakamako ga bayinsa masu xa’a
da kuma azaba ga waxanda suka
sava masa. Waxannan
kammalallun bayi na Allah sun
qauracewa tafarkin vatattu irin
na rafidhat, Khawarijawa,
Jahmiyya, Najariyya da ire-iren
Jama’un ‘yan bid’a (vatattu).
8
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
ii. Al’umma ta biyu ita ce faqihai
waxanda suka himmatu wajen
sani da riqo da hadisan Annabi
(S.A.W), sun himmatu wajen
sanin Allah da siffofinsa
kebantattu, sani na haqiqa. Sun
qauracewa tunani irin na vata,
kamar na qadarawa da
Mu’utazilawa. Sun yi Imani da
Allah haqiqar Imani, sun yarda da
siraxi da qetare shi, sun yi Imani
da ceto da gafara (koma bayan
wanda ya yi shirka). Sun yi Imani
da dawwamar Muminai a Al’janna
da kuma tabbatar kafirai a wuta.
Bayan cewa sun yi Imani da
Halifancin sahabban Annabi
(S.A.W); Abubakar, Umar, Usman,
9
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
da Aliyu, suna riqo da Qur’ani da
Sunna sun yadda da shafa akan
Huffi, sun yadda da Afkar da saki
uku sun yadda da haramcin
auren mutu’a sun yadda da
wajibcin bin shugabanni
matsawar basu yi umarni da
savon Allah ba.
iii. Daga cikin su akwai waxanda
suka himmatu wajen tace
hadisai da tarihin Manzo
(S.A.W), suna matiqar tace
dukka ingantattun hadisai,
sahihai, da kuma raunana
daki-daki. Waxannan bayin
Allah basu yadda su gurvata
ayyukansu da na ‘yan bid’a
10
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
vatattu ba, kamar; Khawarij da
makamantansu.
iv. Akwai daga cikin Ahlul Sunnah,
waxanda suka duqufa wajen
sanin ilimin Adab, da nahawu
da luggar larabci domin
ilmantar da musulmi
ma’anonin Alqur’ani da
ma’anonin Hadisan Annabi
(S.A.W) kamar su; Khalil, Abi
Amru bn Ala’i, Saibuwiya, Farra’i,
Akhfashu, Al-Asma’i, Almazani,
Abi Ubaid, da wasu daga cikin
Malaman Basra da Kufa,
waxannan manyan bayin Allah
basu bar iliminsu ya gurvata da
aqidun ‘yan bid’a irin su
11
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Khawarijawa, Rifadhawa, da
Qadarawa ba.
v. Daga cikin Ahlu; Sunna Wal
Jama’ah, akwai waxanda suka
himmatu wajen karatun
Al’qur’ani da Tafsirinsa tare
da yin Tawili irin wanda ya
dace da Mazhabobi na Ahlul
Sunnah, ba tawili irin na ‘yan
bid’a (Kamar; Khawarijawa, da
Murji’a) ba.
vi. Daga cikin Ahlul Sunnah Wal
Jama’a akwai Zahidai waxanda
aka fi sani da sunan sufaye.
Waxannan manyan bayin Allah
sun himmatu wajen Ibada. Su
masu matuqar kiyaye dokokin
Allah maxaukakin Sarki ne. Basu
12
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
aikata aiki domin ganin ido.
Tauhidi shine abin riqonsu,
Tawakkali da miqa wuya ga Allah
da gudun duniya shine aikin su,
sun himmatu a wajen tarbiyyar
zuciya wajen gujewa savon Allah
da kuma Tuntuni da ambaton
Allah.
vii. Akwai daga cikin Ahlul Sunnah
Wal Jama’a waxanda suka
himmatu wajen tsare mutunci da
dukiyoyi da rayukan Musulmi.
Waxannan manyan bayin Allah
sun xauki tafarki na Jihadi Fi
sabilillah, suna kuma aiwatar da
dukkan al’amuran su bisa koyi da
sunnar Annabi (S.A.W) da kuma
bin Alqur’ani mai girma.
13
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
viii. Waxannan bayin Allah sun
himmamtu wajen bege, da
qasidu na yabo da na tarihin
Annabi (S.A.W) da
sahabbansa. Waxannan sune
Sha’irai na Sunnah. Waqe –
waqensu da qasidun su sun
tattaru akan sunnah da bin Allah
bi na haqiqa.
Mas’aloli Goma Shabiyar Da Ahlul
Sunna Wal Jama’a Suka Tattaru A
Kan Su:
1. Sun tattaru wajen sanin siffofin
Allah da ma’anoninsu da kuma sanin
ginshiken addini tare da ilimin
wadannan siffofi a tattarre da kuma a
rarrabe.
14
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
2. Dukkan su sun yadda cewa Allah
shine mahallincin dukkan ababen
halitta (jikunkuna da kuma rayuka)
3. Sun tattaru wajen Sani da yadda da
Allah Mahallici kuma Masanin dukkan
komai
4. Sun tattaru wajen sannin SiffofinSa
na azaliyya
5. Babu wani bambanci wajen sanin
sunayen Allah da siffofinsa a tsakanin
ahlil sunna wal jama’a
6. Haka nan sun yi itifaki bisa cikakken
Adalcin Allah tare da Gwanintarsa
7. Sun yarda da aiko manzanni daga
Allah
8. Su yadda da Mu’ujizozin Annabawa
(AS) da karamomin waliyan Allah
15
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
9 Sun yadda da ijmain malamai bisa
shari’ar musulunci da rukunanta
10 Haka kuma sun tattaru wajen sanin
hukunce hukuncen umarni da
kyakyawan aiki da hani ga munanan
aiyuka da kuma kame kai daga sabon
Allah
11. Sun yadda da yin fana’in bawan
Allah tare da hukunce-hukuncesa a
shari’a.
12 Sun yadda da halfanci da
shugabanci da sharadansu a
musulunci
13 Sun tattaru wajen hukunce-
hukuncen musulunci da na imani a
dunkulle
16
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
14 Dukkkan su sun san hukunci da
matsayin waliyan Allah da kuma girma
mabayin Allah na gari
15. Dukkansu sun san su wanene
makiyan addinin musulunci na daga
kafirai da masu bin son rai.
BABI NA BIYU
Mu’ujizozin Annabi (S.A.W)
Da Karamomin Sahabbai da
Tabi’ansa
17
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Daga cikin mu’ujizozinsa (SAW) akwai
tsagewar wata, gunjin kututturen
dabino, vovvugowar ruwa daga
yatsunsa (S.A.W), kututturen dabino
ya yi kuka yayin da Annabi ya daina
hawa kansa, abinci ya yawaita ga
mutane masu yawa ya kuma ishesu.
Rindinar sojoji a yaqin Haibar Annabi
(S.A.W) ya shigar da su ruwa daga
wata salka har kowa ya xiba. A yaqin
Tabuka Annabi (S.A.W) ya ciyar da
rindinar sojoji 30,000 sun ci sun qoshi,
kuma abincin bai ragu ba. Annabi
(S.A.W) ya qosar da mutane 1,500 da
abinci qanqani ya mai da idon Abu
Qatada.
18
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Annabi (S.A.W) ya shafi qafar
Muhammad Ibn Malama ta warke
bayan ta karye, yayin da zai kasha
Ka’ab. Ya ciyar da mutum 140 da
nama kalfata guda xaya. Abdullahi xan
Jabir, ya yin da yahuwawa suka matsa
masa akan bashin da suke bin
mahaifinsa, Annabi (S.A.W) ya umarce
su, su zo su xebi dabinon, Allah ya
yalwata dabinon ya isa, bayan Manzo
ya zaga wannan dabinon, aka biya
kowa har ausiqi 15 ya ragu bayan
dabinon bai fi ausiqi 15 ba. Irin
waxannan mu’ujizozi na Annabi (SAW)
inji Ibn Taimiyya sun fi dubu.
Karama
Amincewa da karama wajibine, kuma
qin amincewa da karama bid’a ce
19
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
muharrama. Ma’anar ta shine:
Bayyanar wani abu wanda ya sava da
al’ada. Ita karama ba ta kai matsayin
mu’ujiza ba, domin Annabawa kaxai
ne ke da mu’ujiza.
Ita karama tana bayyana ga bayin
Allah na gari masu cikakkiyar biyayya
ga Annabinsu, imani da karamar
waliyai yana daga cikin turaku na Ahlul
Sunna wal Jama’ah. Inkarin karamar
waliyai yana iya fitar da mutum daga
musulunci.
Imamu Xahawi ya na faxa a cikin
Aqidatul Xahawiyya; muna Imani da
duk irin labarin karama wacce ta
bayyana daga Sahihin baki, ta
sahihiyar hanya. Allah (S.W.T) Shine
yake bayarda karama ga bayinsa
20
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
masu xa’a gare shi da biyayya ga
Annabi (S.A.W).
Sayyidina Abubakar ya yi baqi,
yayinda suka ci abinci tare, abincin
yayi ta qaruwa a duk lokacin da sukayi
lauma, sai yaje kaiwa Annabi (SAW) ya
fada mishi abinda ya faru, Annabi ya
tara sahbbai da yawa suka ci wannan
abinci ya ishesu harma ya ragu.
Imamu Jalalil Muhalli a cikin sharhin
Jam’ul Jawami’i y ace: masana Allah
su ne Allah ke karewa, daga savon
Allah. Ya ce Sayyidna Umar ya yi
wasiqa wacce ya jefa ta a kogin Nil da
nufin saqo, kuma wannan kogin ya yi
biyaiya ga abinda Umar yake nufi a
wannan takarda.
21
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Sayyidina Umar yana Madina, Sahabin
Annabi, mai suna Sariya, yana
Nahawunde, yana jagorancin runduna
ta mayaqa, Umar (R.A) ya yi magana,
cewa ka yi a hankali da bayan dutsen
nan ya kai sariya. Wannan ya afku
yayin da Umar ya hango waxannan
mayaqa na kafirai yana kan mumbari,
a Madina, tattare da nisan da ke
tsakanin Nahawud da Madina, kuma
Sariya ya ji wannan magana ta Umar.
Wadannnan duk sun kuma zuwa a
cikin kitabbul sabilil salam na Makkiyu
Abdullahi Attijjaniyi.
Mu’utazilawa da wasu ire-iren su suna
inkarin karama. A cikin malamai,
kamar Abu Ishaql Isfarayiji, yana ganin
karama kidan har akwaita, to shine
22
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
amsa kiran Annabi. Bai yadda da duk
wani abu day a keta al’ada ba. Hakan
kuskure ne, malamai irinsu Ibn
Taimiyya sun yadda da karama, kamar
yadad ya zo a cikin Fatawal Kubra Juz’i
na 1, shafi na 194, a inda ya yi bayani
cewa mutum yana iya samun karama
a bisa wata nagarta tasa, amma kuma
ana iya samun sad a wasu kura-kurai.
Wato don mutum yana da karama ba
yana nufin shi ma’asumi ba ne.
Daga cikin tabi’ai waxanda karamarsu
ta bayyana akwai Sa’id Ibn Musayyib
wanda ya yin da Yazid ya kaiwa
Madina hari a yaqin Harra, ya kasance
mutane basa iya zuwa jam’i
masallacin Manzo, sai shi Sa’id. A
wannan lokaci duk sa’adda lokacin
23
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Salla ya yi, Sa’id yana jin kiran Sallah
ne daga kabarin Annabi (S.A.W).
Imamul Qushairiy, ya ce; Duk wata
mu’ujiza da Allah ya yi wa Annabawa,
yana iya yi wa bayinsa na gari a
matsayin karama, sai dai ita karama
ba’a takara da ita. Hakan bai cika
afkuwa ba, misali, ba’a ciak samun
waliyyi ya yi qure da ita ta hanyar
karama ba, an samu hakan a wurare
kaxa, kamar inda kafirai suka kawo wa
sahabin Annabi (S.A.W) Khalid bn
Walid gubam ya sha a bisa Imani,
kuma Allah ya kare shi, wannan guba
bata yi masa komai ba.
Xaukikin Ahlul Sunnah wal Jama’ah,
sun yarda da karama, kuma sun yarda
inkarinta bid’a ce muharrama, kuma
24
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
qirqirar karamar qarya shima bid’a ce
muharrama.
Ibn Taimiyya, a ciki Majamu’ul Fatawa
juz’i na 11 shafi na 274-283. ya ce
karama ga waliyai naq musulmi tana
daga cikin Mu’ujizozi na Annabi
(S.A.W).
An kuma samu daga cikin tabi’ai, cewa
Abu Muslimul Khaulani, wani sarkin
Yemen mai suna Al-Aswadil Ansi ya
tambaye shi cewa, ka yadda ni
Manzon Allah ne? sai Abu Muslimul
Khaulani ya ce ni bana jin abinda ka ke
faxa. Ya sake tambayar say a sake
bashi da wannan amsa. Sai ya
tambaye shi Abu Muslim to ka yadda
cewa Muhammad Manzon Allah ne?
25
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Sai ya amsa masa cewa: “Qwarai da
gaske”. Sai shi wannan sarki ya sa aka
haxa guma-gumai aka xaure Abu
Muslim aka jefa shi cikin wutar. Igiya
da aka xaure wannan bawan Allah, ita
ce kaxai ta qone, Sayyadina Umar
(R.A) ya ce: Na godewa Allah (S.W.T)
da ya nuna min a cikin al’umar Annabi
Muhammad, mai karama wacce ta yi
dai-dai da mu’ujiza irin ta Annabi
Ibrahim (A.S). Shaihul Islam
IbnTaimiyya ya yi bayanai a cikin
Majamu’ul Fatawarsa.
Ibn Abidin yace: Daga cikin karamomi
na Waliyai har su yi tsinkayu da wani
abu na gaibi, Mu’utazilawa ne kaxai
basu yadda da wannan ba.
26
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
An bada labari cewa, wani mutum
daga cikin qabilar Nakhax, ya na cikin
ayari tare a abokan tafiyarsa, sai
jakinsa ya mutu, abokan tafiyarsa suka
ce ai sai mu kwashe kayan jakin mu
xaukar maka su zuwa gida. Sai
wannan bawan Allah ya ce ku yi min
haquri, sai ya yi alwala kyakkyawa ya
yi nafila, ya roqi Allah cewa; Ya Allah
Kada kasa wani bawa naka ya
zamanto yana da abinda zai min gori
akansa”, Allah Ta’ala ya tayar masa da
jakinsa har zuwa gida. Yana isa gida,
ya ce da xan sa zo ka sauke kayan
dake kan wannan jaki, domin shi
wannan jaki na aro ne, ana sauke
wannan kaya, sai wannan jaki ya cika.
27
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Lokacin da Uwaisul Qarni ya rasu an
same shi yana cikin likkafani, wanda
kowa ya shaida cewa, kafon rasuwarsa
baya tare da wannan likkafani. Ya yin
da akaje za’a tona kabari domin a
binne shi, an tarar da kabarin a tone,
da kuma wata qofa ta dutse a ciki, a
inda aka sanya shi.
Amr Ibn Uqba Ibn Farqat yin sallah a
cikin rana, yayin da rana tatake, sai
aka ga wani gajimare ya zo ya yi masa
inuwa, yayin tafiya kuma namun daji
suke gadin su tare da abokan tafiyar
su, a duk sa’adda dare ya yi.
Muxarrab Ibn Abdullah Al-Shakkhir, an
bada labari cewa, a duk lokacin da ya
shiga gidansa, a duk lokacin da yake
cin abinci, sai aji kwanon yana yin
28
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
tasbihi tare da shi. Idan yana tafiya a
cikin hudu za’a ga wani haske yana
haska masa kamar fitila.
Ahnab: A yayin da ya rasu, wajen
binne shi sau hular wani mutum ta
faxa cikin kabarin, a yayinda wannan
abwan Allah ya sunkuya domin ya
xauko hularsa, sai ya ga cewa kaarin
ya yi zurfi da faxi, wanda bai ga iyakar
sa ba.
Ibrahimil Taimiy: Ance yak an i wata
guda bai ci komai ba, sai dai ya
samowa iyalinsa abinda za su ci; wata
rana ya fita nema bai samu ba, sai ya
hangi wani tsumma, da jar alkama a
ciki, ya kasance a duk lokacin da aka
buqaci abinci a gidansa sai wanan
tsumma ya futo da abinci kamar inji.
29
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Utbatul Gulam: Ya roqi Allah abubuwa
guda uku, daxin murya, da yin kuka
yayin karatun Alqur’ani da kuma
samun abinci ba tare da wahala ba.
Allah ya amsa masa.
Asim Ibn Sabit: Allah Ta’ala ya tsare
gawarsa daga kafirai yayin da suka so
su xauke ta, su walaqanta ta a wajen
yaqi, sai Allah ya aiko musu da qwarin
xango, kuma ba’a sami gawar ta sa
ba.
Usaidu Ib Khudair: Yana karanta
Suratul-Kahafi, sai aka ga wani irgije
wanda yake mala’ku ne suka sauko
domin jin karatun sa inji Shaihul Islam
Ibn Taimiya.
30
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Haka kuma, Salman da Abul Darda’i:
sun kasance suna cin abinc, kwanon
da suke cin abincin yana tasbihi.
Abdan bn Bashir, da Usaiyu bn
Khudair: Sun fito daga wajen Annabi
(S.A.W) a wani dare mai hudu sai
haske yake fita kamar fitilar cocilan
daga goshinsu, yayin da kuma suka
rabu zuwa gidajen su ko wannen su ya
tafi da wannan haske batare da na
kowannan su ya raguba.
Wadannan kadan ne daga cikin irin
karamomin sahabban annabi (SAW).
SON ANNABI (S.A.W)
- Shiga wata darika ko kungiya
ba shine zai sa a yanke wa
31
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
musulmi hukunci a kan son
Annabi ba
- Dole ne ga musulmi ya samu
tarbiyyar wacce zata bashi zauqi
na qaunar Annabi (S.A.W).
- Dole ne dukkan Musulmi ya
zama mai biyaiya ga Sunnar
Annabi (S.A.W) da bin abinda
Annabi yake so a aikace. So,
Alwujdani da kuma ittiba’i
(cikakken Imani).
Kuskure ne babba ka dubi Musulmi
domin bambancin ra’ayi ka ce baya
son Annabi (S.A.W). Bayin Alalh da
suka himmtu wajen bin diddigin
Hadisan Annabi (S.A.W) da bin Sunnar
sa lallai masu qaunar Annabi (S.A.W)
ne, koda wane vangare suka xauka a
32
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
matsayin aqidarsu. Sheikh Usman bn
Fodio yayi tafiya da masu Shaihi, wato
‘yan Xariqa da kuma waxanda basu da
shaihi, a matsayin dukkan su musulmi
ne masu qaunar Annabi (S.A.W).
Ma’anar Bid’a
Sheikh Muhammad Nasir Kabara
yana cewa acikin Annasihatul
Sarikha fil Raddi alal akidatul
Sahiha: A cikin ta’alikin Fawa’idul
Ahdil Talamiz na Sheikh
Muhammad Munir Al Shanawi Al
Khalwati (Fasali na farko) Bid’a ta
kasu kashi kashi.Ita Kalmar bid’a
ta samo asali daga Kalmar
badu’a- wato farar da abu sabo.
33
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Misali farar da Sammai da
Kassai.Kamar yadda Ibn Hajr (Al
Askalani) ya fada. Masu fassara
wannan aya suka ce ai Allah ya
samar ko ya farar da Sammai da
Kassai, al hani da babu su. Kuma
Al Isbali a cikin sharhin Ar’ba’ina
yana cewa : Ayyuka muhaddsai,
wato fararru sun kasu kasha biyu:
Marasa kyau wadanda basu ginu
a kan dalilai na shari’a ba.
Dakuma masu kyau wadanda
suka ginu a kan shari’a. ‘Allah
ta’ala ya na cewa: Ma yati him
min zirkin min Rabbihim
muhdasin’. Sayyadna Ali (RA)
34
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
yana cewa: Madalla da wannan
bid’a (wato sallar tarawihi). Daga
cikinsa, a kwai fadar maaiki
(SAW): Man sanna sunnatin
hasanatan fa lahu ajaraha wa
amalu man amila biha ila yaumil
kiyamati.Shekh Ibrahimlakkani
jahilci ne mutum ya dauka cewa
duk irin aiyukan dab a a aikata su
zamanin sahabbai ba bid’a ce
abarki. (Kitabul manarul fatawa fil
kawa’idul fata’I bil kawa. Misali
neman ilimin fiqhu bid’a da usulul
dini bid’o’I ne wajibai. (Marubucin
wannan littafi ya kara da cewa
misali: Musabakar karatun
35
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Alkur’ani mai girma bid’a ce
muhassana) , amma inkarin
karamar waliyan Allah bid’a ce
muharrama.)
BABI NA UKU
36
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
MA’ANAR SUFANCI A MUSULUNCI
Ma’anar sufanci shine gyara zuciya,
raba mutum daga miyagun xabi’u,
kyakkyawar alaqa tsakaninka da
ubangiji tsakaninka da al’umar
Musulmi.
Sheikh Ali Assayad Al-Qadiriy, ya ja
hankalin sufaye akan al-amura da
dama domin gyara akan kura-kuran
wasu daga cikin sufaye. Haka kuma
Sheikh Ahmad Zaruq a qawa’idul
Sufiyya da kuma Sheikh Usman Bin
Fodio a cikin Ihya’ussunar sa, sun yi
nasiha da gyare-gyare ga sufaye.
Amma kuskure ne ga wanda bai
fahimci al’amarin ba ya yanke hukunci
bisa son rai ko zalunci.
37
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Sheikh Usman Bn Fodio ya xauko wata
Magana ta Malam Izuddeen Ibn Abdul
Salam a inda ya karkasa sufaye gida
huxu, ko biyar, a cikin littafinsa
Qawa’idul Ahkam. Sheikh Abubakar
Gumi ya kawo irin wannan bayani a
cikin littafinsa Akidatil sahiha bi
muwafikatil shari’a, kamar yadda yazo
a Mudariji Salikin na Ibn kayyim.
Daga cikinsu akwai waxanda al-asama
(sauraro) yake tasiri a zuciyar su.
1. Sauraroon karatun Alqur’ani
yana sa su suyi kuka, ko suma, ko
hali domin ganin girman Allah.
Waxannnan sune suka fi. Jikinsu
yakan yi sanyi, ko su shixe saboda
sauraron Alqur’ani.
38
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
2. Imanin su yana qaruwa yayin
da suka ji wa’azi sune masu daraja
ta biyu.
3. Yayin da suka ji waqa al-hida,
kamar waqa wacce makiyaya ko
mata suke yi, idan suna niqa,
zuciyarsu tana karaya, su fusgu,
ko su yi hali, ko su shixe waxannan
sune kaso na uku. Abinda ya sa,
akwai jin daxin rai, don haka basu
kai sauran martabobi ba.
Masu jin Alqur’ani, zuciyarsu ka karye,
su suka fi daraja, sai waxanda wa’azi
ya ke sanya su su yi hali. Ya ci gaba da
kawo ragowar matakai a littafinsa.
Shi kuma Sheikh Muhammad Sani Ibn
Hassan Kafinga yana cewa, a cikin
Alminnahu Hamidat fil Raddi ala fasidil
39
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Akidat: Lalle ne babu shakka yin
mujahada tare cudandaya da bayin
Allah na gari yana daga cikin turakun
samun shiriya.Haka huma duk wanda
Allah ke so da samun suluki, sai Ya
arzutashi da da yin biyaiyya ga Allah
tare dagudun sabon Allahsa’annan ya
arzuta shi da yin sulukin.
Sheikh Usman Bn Fodio ya ce inkarin
karamar Waliyan Allah bid’a ce
muharrama. Ya ci gaba da cewa bid’a
ce muharrama mutum ya yi qaryar
karama. Malamin ya ce duka
waxannan ana yi musu tsoron
mummunar cikawa.
Sheikh Usman Bn Fodio ya yi bayani
kan cewa, yayin da malami, wanda ya
40
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
son Alqur’an da Hadisi ya yi karo da
wata magana ta wani sufi, sai ya
zamanto cewa bai fahimci wannan
magana ba, to ya bar ta a a matsayin
cewa, shi ne bai fahimci wannan sufi
ba, yayi masa uzuri. Kuma wannan ko
kaxan ba gazawa bace ga shi
malamin. Yanke hukunci a bisa irin
waxannan maganganu shike jawo
taqaddama da yiwa juna rashin adalci.
Ka yi aiki da abinda ka fahimta ka
qyale abinda baka sanshi ba.
A cikin A’azabul Masalikil Mahmudiyya
na Mahmud Muhammad Khattab
Al-Subki, juz’i na 1 shafi na 40.
- A ilmance ilimin gyaran zuciya
da gavvai yana taimakawa wajen
tsare zuciya daga mugunta, riqo,
41
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
hassada, fushi mara ma’ana, rawa,
girman kai, da makamantarsu.
- Nisantar Haramun
- Na taqaitawa wajen aikata
halal, kamar cin abinci ba tare da
hama ba.
- Neman kusanci ga Allah.
- Kare gavvai da savon Allah.
- Duqufa da yin aiki ba ji ba gani
akan abinda Allah ya ke so.
- Amfani da lokaci a abinda yafi
komai daraja da cancanta.
Imamu Junaid yana cewa:
Ma’anarsa shine gaskiya ta kasheka,
kuma ta raya ka.
Sheikh Sha’araniy ‘AbdulWahab bn
Ahmad’ (963A.H) y ace: Ma’anar
sufanci shine bayyana wani ilmi
42
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
sakamakon haske daga zuciya ke
samu, a bisa dalilin aiki da Alqur’ani da
Hadisi, wanda sai mai abin ne yake ji
(kamar yadda Ibn Qayyim yake faxa a
Mudarijissalikin ).
Babban al’amari anan shine tsarkakkar
zuciya, kaucewa shubuha, da
karkacewa dukkan abinda zai jawo
gafala.
Shaihul Islam Ibn Taimiyya a cikin
Majamu’ul Fatawah yana cewa: Daga
cikin (Ahlul Sunnah wal Jama’ah) akwai
waxanda suka himmatu wajen Ibada
kamar Sufaye.
Sheikh Muhammad bn Muhammad
bn AbdulWahab yana cewa a cikin
43
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Mauqifil Ayimmati na Sheikh Abdul
Hafiz Al Makki:
Ni da mahaifina bama inkarin Sufanci,
ko kuma xariqun sufaye. Sai dai mu ba
ma tawili akan maganar Ubangiji
maxaukakin Sarki, ko Hadisan Annabi
(S.A.W) ko kuma maganar wani
malami. Yaci gaba da cewa; mu bamu
kai matsayin Ijtihadi ba sai dai mukan
auna duk wani hukunci da wani
malami ya aiwatar a bisa ma’auni na
hadisi da nassin Alqur’ani. A duk inda
wani malami ya bada fatawa wacce ta
sava da wannan ma’auni mu bama
aiki da ita. Mu kuma bama inkarin
Taqlidi da wata Mazhaba ta Ahlul
Sunnah, kuma mun kasance masu bin
Mazhabar Imam Ahmad bn Hanbal ne.
44
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Idan har babu kyakkyawar niyya da
kuma gaskiya, babu yadda Shaihul
Islam Ibn Taimiyya zai kashe lokaci ya
vata kusan shafuka xari a cikin
Majamu’ul Fatawarsa Mujalladi na 10
shafi 455-550.1 ) yana ta bayani (na
yabo) a kan maganganun Sheikh
Abdulqadir Jilani (R.H), da yayi a
cikin littafin Futuhul Ghaib na shi
Sheikh Abdulkadir din .
Idan kuma ka duba Ihya’ussanna na
Sheikh Usman bn Fodio za ka ga
inda ya ware sufanci na haqiqa daga
bidi’o’i da suka haifu a cikin sufanci.
Malamin ya yi jan kunnen gaske akan
inkarin karamar Waliyyai, sa’annan ya
yi jan kunne a bisa afkawa littattafan
sufaye musamman ga marasa ilimin 1 Majamu’ul Fatawa.
45
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Hadisi da Alqur’ani. Ya yi jan kunne
sosai ga masu qaryar karama (ko
qaryar kashafi). Shi kuwa Shaihin
Malamin nan Ibn Qayyim Al-Jauziy,
littafi guda ya yi (ba na suka ba), mai
suna Mudarijil Salikin. Kowa ya san
cewa suluki al’amari ne na sufaye.
Idan ka duba Tazyinil Waraqat na
Sheikh Abdullahi bn Fodio shafi na
44 zuwa na 46 zaka ga inda ya yi
waqe (na yabo), ga Sheikh AbdulQadir
Jilani.
Mallam Ibrahim Khalil Kano yace:
“Malamanmu suna da kyakkyawan
zato cewa, ba dan Sheihil Islam Ibn
Taimiyya ya rayu har ya rasu kafin
Sheikh Ahmadu Tijjani, da zai yi taliqin
wasu daga cikin bayanansa kamar
46
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
yadda yayi wa Futuhul Gaib. Allahu
A’alam.”
Dan haka kuskure ne, da rashin adalci
a xauki sufanci a vata shi baki xaya.
Babban abinda sufanci yake so ya gina
a zukatan musulmi shine tarbiyyar da
bayin Allah wajen neman yardar Allah
shi kaxai. Ita ce hanyar da ake bi
domin samun wannan tarbiya, bayanai
na malamai irin su Ibn Taimiyya da su
Ibn Qayyim sun yadda cewa sufaye
sun fi kowa qwarewa wajen wannan
tarbiyya.
Lallai ne jama’u guda uku su sani
cewa;
i. Masu qaunar Ibn Taimiyya
kuma suka san shi, su sani
cewa ya san sufanci, kuma
47
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
yana da kyakkyawar alaqa da
sufanci. Koda zai yi bayani a
inda yake ganin akwai gyara
wannan baya nufin cewa shi
baya qaunar sufanci.
ii. Masu ganin cewa shi Ibn
Taimiyya baya qaunar sufanci
su san cewa ba haka ba ne.
iii. Su kuma malamanmu su riqa
yin adalci koda daga wane
vangare suka karkata.
Dan an samu wasu waxanda suke
da’awar sufanci, suka samu kansu
cikin aikata kuskure, wannan kuskure
bai kamata ya zama hujja ta haxawa a
rafke wannan kyakkyawar aqida ba.
Sheikh Usman Xan-Fodio yana cewa a
cikin Ihya’ussunnarsa; kuskure ne
48
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
ga wanda ba zai iya bambancewa
tsakanin tururuwa da giwa ba ya riqa
xaukar littattafan sufaye ko kuma
bayin Allah masu kashafi yana yanke
hukunci (na yabo ko na suka) a kansu.
Shaihun Malamin ya yi jan kunne ga
sufaye (har ma da wanda ba sufaye
ba) a kan cewa duk lokacin da ka ji
wani ‘Hatifi’ akan aikata wani aiki,
lallai ne ka aunashi akan ma’auni na
Hadisan Annabi (S.A.W) da nassin
Alqur’ani mai girma. Idan har ya
zamanto wannan hatafi naka bai yi
muwafaqa da hadisan Annabi (S.A.W)
da Alqur’ani ba to ka yi watsi da shi
kawai.
Bayanin Malaman Azhar Akan
Sufanci
49
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Malaman Azhar suka ce a cikin
kundinsu mai suna Haza Bayanin
Linnas karkashin jagorancin Shaihi
malaminnan, Jadil Haq Aliyu Jadil Haq.
[Juz’i na 2 shafi na 35-37];
Haqiqa an yi rubuce-rubuce akan
sufanci masu wayan gaske. Xabaqatil
Sufiyya na Abu Abdul Rahman Al-
Sulami shi ne na farkon wanda ya fara
rubutu akan sufanci. Sai Al-Risalatil
Qushriyya fi Ilmil Tasawwuf Abul
Qasim Abdul Karim Ibn Hawazim Al-
Qushairiy.
Imamul Qushairi ya ce ‘Kalmar sufanci,
laqabi ne kamar dai kalmar mutum
take’. A ganin sa kuskure ne a
danganta ma’anarsa da ‘Suffa’ ko ‘Suf’
50
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
wace ke a masallacin Annabi (S.A.W)
ko safa, ko saffi ko suffu.
Abinda ake cewa sufanci shine gaskiya
ta kasheka, kuma ta rayaka. Ma’anar
gaskiya anan shine Allah ko shari’a;
Ya ce: Shehunnai sun tafi sai dai
kufansu, sai dai matasa (a shekara ta
xari huxu). Amma a cikin matasan
akwai masu nagarta da dama (abin
koyi ne).
Yayi bayanai a kan kura-kuran wasu
daga cikin sufaye a kan aqida da kuma
suluki.
Wasu daga cikin malaman tarihi suna
danganta asalin maganganu masu
nuna wujdaniyya da zauqi iri na sufaye
daga sahabin Annabi (S.A.W)
Huzaifatul Yamaniy daga inda suke
51
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
ganin Hasanul Basri ya sami wannan
tarbiya. Hasanul Basri ya rasu
(110A.H). Ana ganin daga shi Hasanul
Basri sufanci ya samo asali.
Ma’aunin da za’a auna sufaye da shi
shine faxin Allah Ta’ala: “Ala inna
Auliya’ullahi la Khaufun alaihim wala
hum yahazanuun. Allazina Amanu wa
kanu yattaqun. Lahumul Bushra fil
hayatuddunya wa fil akhira. La tabdila
li Kalimatillah, zalika huwal fauzil
Amim”
“Wa anna haza siraxiy mustaqima
fattabi’uhu, wala tattabi’al subula fa
tafarraqa bikum”.
Da kuma Hadisan Annabi (S.A.W) Man
Ahdasa fi Amrina haza ma laisa minhu
fa huwa raddun.
52
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Dan haka, a ganin malaman Azhar irin
wannan gudun mawa ta sufaye abin
yabo ne, kuma abin a qarfafa musu
gwiwa ne. Suka ci gaba da cewa a
yayin da aka samu wasu daga cikin
sufaye, sun kaucewa koyarwa wacce
ta dace da Sunnar Annabi (S.A.W) da
Alqur’ani mai girma, to lallai ne a dawo
da su kan hanya.
To, mene ne dalilin rashin jituwa
tsakanin wasu daga cikin Ahlul
Sunanna Wal Jama’a {Kamar Sufaye
(‘Yan Xariqa) Da Kuma Salafawa (‘Yan Izala)} a
wannan zamanin?
A qashin gaskiya, babu wani dalili na
gaskiya da zai sa hakan ta faru, idan
har kuwa akwai bai wuce son zuciya
53
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
na masu ilimi daga ciki ba, sai kuma
jahilci da qarancin fahimta.
Babban abin baqin ciki shine ko
wannan su yana suka wanda ya wuce
iyaka, wanda haqiqa malaman dukkan
vangarorin biyu sun tabbatar ba
gaskiya ba ne. Misali, Malaman Xariqu
sun san cewa ba gaskiya ba ne, kuma
kuskure ne babba ka ce da xan Izala
maqiyin Annabi (S.A.W). Haka nan
Malamai daga cikin ‘yan izala sun sani
cewa kuskure ne ka kira Sufaye da
sunan Mushirikai, ko ‘yan bid’a.
Allah Ta’ala ka shiga tsakaninmu da
shaixan jefaffe. Taqaitaccen misali na
kwanannan shine yadda Sheikh
Nasiruddeen Albani, wanda kowa ya
san ra’ayinsa irin na Almajiran Sheikh
54
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
Muhammad Ibn AbdulWahab ne, ya
varke da kuka a yayin da wasu ‘yan
‘uwa (mata) suka buga masa waya
suna yi masa Albishir da cewa; Sun ga,
ko kuma xaya daga cikin su ta ga
Annabi (S.A.W) cikin bacci yana gaba
suna bin sa a baya, sai suka yi karo da
wani Shaihin Malami, suka yi da masa
sallama, shi kuma malamin ya amsa. A
yayin da Nasirudddeen Albani ya ji
wannan bayani sai ya ce, wanene
wannan malamin? Sai suka ce kai ne
wanda muka gain a cikin wannan
mafarki. Ya ce: kunga Annabi! Suka ce
qwarai. Allahu Akbar, wannan babban
Malami, masanin Hadisai sai ya varke
da kuka.2
‘Yan uwa sai muyi hattara. 2 Domin karin bayani, ka duba http://www.youtube.nasiruldeenalbani...
55
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
To kai kuma xan izala mai cewa da
sufaye mushirikai, ka sani cewa
Babban Malamin nan mai suna
Yusufun Nabahaniy a cikin littafinsa
Shawhidil hak ya ce: “Na yi mafarki, a
inda naji magana, na tabbatar cewa
Allah ta’ala ne, na waiga na kalli sama,
na ga haske kwatankwacin yadda
Annabi Musa Alaihis Salam ya gani, sai
naji ance; Ni ina qaunarka, Allah shine
shaida akan abinda muka ambata”.
Tirqashi! Malamai sun san cewa babu
wasa a maganar mafarki da Allah ko
Manzo (SAW). Don haka kowa ya tsaya
matsayinsa a kuma yi ta karatu a
kuma guji karambani.
56
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
BABI NA HUDU
NASIHA…
…..GA MALAMANMU
1. Wajibi ne Malamai su san cewa
su halifofi ne na Annabi (S.A.W).
2. Su kasance masu qaunar
al’uma da tausayawa al’umar
Annabi (S.A.W).
3. Annabi (S.A.W) baya jin daxin
kafircin kafirai ma saboda tausaya
musu, don haka wajibi ne malamai
su yi wa musulmi duka, duba na
Rahama da qauna.
4. Zalunci ne da cutarwa ga
al’umma malamai su sanya qiyaiya
57
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
ga wasu daga cikin musulmi domin
kawai bambancin aqida.
5. Imam Malik yana cewa ka yi
wa xan’wanka hanzari sau xari,
sa’annan ka nema masa gafara
wajen ubangiji (akan kura-
kuransa).
6. Annabi (S.A.W) ya yi haquri da
larabawan qauye, ya kasance mai
tausayawa da qauna ga al’umarsa.
7. Wajibi ne malamai su yi
Tarayus da nuna qauna wajen
da’awa.
8. Tausayawa juna da nasiha
cikin hikima da rashin qyamar juna
shi kansa wa’azi ne wanda zai sa
ka ja hankalin xan’uwanka ya yi
sha’awar aqidar ka.
58
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
……..GA DALIBAI
1. Kada ku yadda a tunkuxa ku
wajen qin ‘yan’uwanku musulmi
domin bambancin aqida ko
mazhaba.
2. Akwai Hadisin Annabi (S.A.W)
wanda Sheikh Al-Baniy ya kawo shi
a cikin Silsilarsa, Annabi Ayub
(A.S.) ya kasance idan ya zo
yucewa ya ji wani Musulmi yana
rantsuwa a kan zai yi kaza ko ba
zai yi ba, yakan yi sadaka, ya
kuma ‘yanta bayi, ya ce Allah na
‘yanta wannan bayi, idan kaffara
ta kama wannan bawa naka, to na
yi masa kaffara ka yafe masa.
Haka ya kamata mu zama masu
59
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
tausayi da qaunar ‘yan uwanmu
Musulmi.
RUFEWA
‘Yan Uwa Musulmi, sai muyi hattara
wajen neman ilimi tare da yi wa juna
kyakkyawar fahimata. Hakan ba zai
samu ba sai mun san matsayin mu
kafin mu san matsayin ya’n uwanmu
akan mas’aloli: Inda mukayi
musharaka da kuma inda muka sha
bam ban wajen fhimta.Tare da fatan
mun gamsu cewa ‘yan uwan mu
sufaye Ahlul sunna ne cikakku ba
mushrikai bane,’yan uwanmu ‘yan
Izala ba makiya annabi bane suma
Ahlul sunna ne kuma masoya Annabi
(SAW) ne sa’annan wanda baya wat
60
Ahlul Sunnah Wal Jama’ah ……
kungiya ko darika matsawar yayi riko
da sunna shi ma ahlul sunna ne kuma
kuskure ne ace masa Jemage.
ALLAH YI MANA MUWAFAKA DA BIN
SUNNAR MA’AIKI (SAW). AMIN
61